Jirgin yaƙin Amurka a karo na biyu ya faɗa Tekun Maliya

Hoton jirgin yaki

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A karo na biyu cikin kwana takwas, wani jirgin yaƙin Amurka ya tsunduma tekun Maliya daga kan jirgin ruwan dakon jiragen yaƙin Amurka mai suna USS Truman, kamar yadda jami'an Amurka suka bayyana.

Jirgin ƙirar F/A-18F Super Hornet yana ƙoƙarin sauka ne a doron titin saukar jirage na jirgin ruwan Truman ranar Talata, lokacin da wata dabara ta ƙi aiki, "lamarin da ya sa jirgin ya yi saɓi-zarce zuwa cikin teku", wani jami'i ya shaida wa tashar CBS, abokiyar ƙawancen BBC a Amurka.

Matuƙan jirgin biyu sun fitar lema, ko da yake sun ji ƙananan ranuka. Farashin duk ɗaya cikin jiragen ya kai gomman miliyoyin daloli kamar yadda aka ba da rahoto.

"An ceto matuƙan jirgin da suka kuɓuta cikin aminci a wani jirgin shalkwafta," jami'in ya faɗa wa tashar CBS.

Lamarin ya zo ne bayan wani jirgin yaƙin daban ƙirar Super Hornet ya yi saɓi-zarce ya tsunduma cikin tekun ta Maliya ranar Litinin da ta wuce a wani lamari na daban.

"An janyo jirgin ne daga rumfar ajiyar jiragen yaƙi lokacin da ya kufce wa jami'an da suka ɗauko shi", sanarwar Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta ce. Wani sojan ruwa ya ji ciwo, kuma an janyo motar tarakta da suka faɗa cikin teku da jirgin.

A lokacin kifawar jirgin yaƙin na biyu, jami'ai sun ce an samu gazawar wata murtukekiyar wayar da ake amfani da ita don taimaka wa jirgin yaƙi rage gudu a lokacin da ya sauka.

Har yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma zuwa yanzu ba a gano jirgin da ya faɗa tekun ba.

Jirgin yaƙin mai yiwuwa ya tuntsira cikin teku ne bayan jirgin dakon jiragen yaƙin ya yi wata wawar zamiya a ƙoƙarinsa na kauce wa wani al'amari daga 'yan ta-da-ƙayar-bayan Houthi na Yemen, kamar yadda jami'an Amurka suka faɗa wa tashar CBS.

'Yan sa'o'i kafin nan nan a ranar Talata, Shugaba Donald Trump ya ba da sanarwar cewa Amurka za ta dakatar da hare-haren da take kai wa 'yan Houthi masu samun goyon bayan Iran, matuƙar ƙungiyar ta daina far wa jiragen ruwan da ke wucewa a Tekun Maliya.

Jirgin dakon jiragen yaƙi na Truman ya gamu da tuntuɓe da dama tun bayan tura shi Tekun Maliya, ciki har da abin da ya faru a watan Disamba lokacin da jirgin dakon jiragen yaƙin Amurka USS Gettysburg cikin kuskure ya kakkaɓo wani jirgin yaƙin Amurka ƙirar F/A-18 da ke aiki da Truman.

Amurka ta ji tsoro - Houthi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sanarwar ta zo ne bayan wani babban jami'in ƙungiyar Houthi ya yi watsi da iƙirarin Shugaban Amurka Donald Trump na cewa an kassara ƙungiyar masu gwagwarmaya da makaman ta ƙasar Yemen ɗin lokacin da suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta, yana cewa maimakon haka Amurka "tsoro ta ji".

"Abin da ya canza shi ne matsayin Amnurka, amma mu muna nan a kan bakanmu," babban mai shiga tsakani Mohammed Abdul Salam ya faɗa wa tashar talbijin ɗin Al-Masirah ta 'yan Houthi.

Ƙasar Oman wadda ke shiga tsakani ta ce Amurka da Houthi sun amince su "daina kai wa juna hari", bayan mako bakwai da Amurka ta kwashe tana zafafa hare-hare a kan Yemen don mayar da martani ga makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Houthi ke harbawa kan jiragen ruwan da ke sufuri a Tekun Maliya.

Abdul Salam ya kuma ce yarjejeniyar ba ta ƙunshi dakatar da hare-hare kan Isra'ila ba, wadda ta gudanar da zagaye na biyu na hare-haren ramuwar gayya kan Yemen a cikin wannan mako.

Goyon bayan Houthi ga al'ummar Falasɗinawa a Gaza "ba zai canza ba", ya ƙara da cewa.

ƙungiyar mai samun goyon bayan Iran tana iko da mafi yawan yankin arewa maso yammacin ƙasar Yemen tun daga 2014, lokacin da ta hamɓarar da gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita daga Sanaa, babban birnin ƙasar, abin da kuma ya janyo wani yaƙin basasa da ya tagayyara al'umma.

Tun cikin watan Nuwamban 2023 ne, 'yan Houthi suke kai hare-hare kan gomman jiragen ruwan kasuwanci na makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa baya ga amfani da hare-haren ƙananan jiragen ruwa a Tekun Maliya da Mashigin Tekun Aden. Sun dulmiyar da jirgin ruwa biyu, kuma sun ƙwace na uku, yayin da suka kashe ma'aikatan jirgin ruwan huɗu.

Sun ce suna yin haka ne don nuna goyon bayansu ga al'ummar Falasɗinawa a yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza, kuma sun yi iƙirari - ko da yake sau da yawa na ƙarya ne - cewa suna kai farmaki ne kan jiragen ruwan da ke da alaƙa da Isra'ila, Amurka da kuma Birtaniya.

'Yan Houthi ba su nuna tsoro ba kan jiragen yaƙin da Ƙasashen Yamma suka tura zuwa Tekun Maliya da Mashigar Tekun Aden domin kare jiragen ruwan kasuwanci a bara, ko kuma da jerin hare-haren Amurka birjik a kan cibiyoyin soji kamar yadda tsohon Shugaban Amurka Joe Biden ya riƙa ba da umarni.