An sace makamashin uranium da ake haɗa makamin nukiliya da shi a Libya – MDD

BBC

Asalin hoton, Reuters

Hukumar da ke sanya ido kan makamashi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tan biyu da rabi na makamashin uranium ya yi ɓatan dabo a Libya.

Hukumar kula da Nukiliya ta Duniya ce ta bayyana hakan bayan wata ziyarar aiki da wasu wakilanta da ke sanya idanu suka kai a farkon makon nan.

Sun gano diro 10 da ke ɗauke da makamashin uranium a baya amma yanzu babu komai cikinsu, in ji hukumar.

Akwai barazanar iskar makamashin na uranium ka iya haifar da gagarumin haɗari da kuma barazana ga tsaron makamashin nukiliya.

Hukumar IAEA ta ce wurin da aka ajiye makamashin ba ya ƙarƙashin ikon gwamnati.

Cikin wata sanarwa, IAEA ta ce za ta gudanar da wani bincike na musamman “domin gano dalilin kwashe makamashin nukiliyar da kuma inda aka ɓoye shi a yanzu”.

Ba dai a san yaushe aka ɗauke makamashin ba kuma babu tabbacin wanda ya ɗauke shi.

“Amma an ɗauke shi ne daga wani waje a gefen kudancin Libya,” in ji Scott Roecker na wata ƙungiya da ke lura da makamashi, da ke aiki da MDD.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

“Duk wanda ya biyo wannan makamashi har nan ya ɗauke shi, to yana son shi ne kuma ya san amfanin shi,” ya shaida wa BBC, yana cewa “yawan makamashin da aka ɗiba yakai kashi ɗaya cikin 10 na wanda aka ajiye a wurin, don haka dole ka gane an dauke shi”.

Hukumar IAEA tana ƙoƙarin yadda za ta fito da abin da ya faru a fili kowa ya sani, yadda aka sace makamashin da kuma inda aka yi da shi yanzu.

Sai dai a wannan ƙadamin, masu sanya idanu na nuna fargaba kan rashin sanin illar da iskar makamashin za ta iya haifarwa da kuma barazanarsa ga tsaron nukiliya.

Kazalika makamashin “na kan ganiyar haɗarinsa da aka fi sani da (yanayin ruwan ɗorawa) wanda ba za a iya mayar da shi makamashin nukiliya ba, don haka babu damar akwai isasshen makamashin da za a iya mayarwa na nukiliya a yanzu”, in ji Mr Roecker.

Haka kuma babu wata “damuwa ta a zo a gani kan gurɓatacciyar iskar da makamashin ke ɗauke da ita a yanzu”, kamar yadda ya ƙara da cewa.

IAEA ta ce shi wurin da makamashin yake a yanzu wani abu ne mai sarƙaƙiya.

Masu sanya idanu sun so su kai ziyara wurin a bara, amma dole haka tawagarsu ta ɗage ziyarar saboda rikicin da ke faruwa tsakanin masu ɗauke da bindiga a Libya.

A watan Disambar 2003 ne, Libya ta sanar da shirinta na nukiliya ta kuma amince za ta taƙaitawa kanta mallakar makami mai cin dogon zango da bai wuce kilomita 30 ba.

Amma tun bayan kisan da aka yi wa tsohon shugaban ƙasar Kanar Muammar Gaddafi a 2011, ƙasar ta faɗa cikin wani yanayin gasa ta fuskar siyasa da kuma rabuwar kan soji.

Yanzu ta rabu tsakanin gwamnatin riƙon ƙwarya da ke Tripoli babban birnin ƙasar da kuma ta gabashi da Janar Khalifa Haftar ke jagoranta.