Bikin Halloween: Fiye da mutum 150 sun mutu yayin mummunar turereniya

Asalin hoton, Getty Images
Rahotannin baya-bayan nan da muke samu na cewa akalla mutum 151 ne suka halaka a sanadin wani gagarumin turereniyar da ya auku a wani matsattsen layi da ke Seoul babban birnin Koriya ta Kudu.
Jami'ai sun ce tarin jamar sun fita bisa titunan birnin ne domin yin wani biki na shekara-shekara da aka saba yi, sai dai wannan nan ne irinsa na farko tun bayan da aka dage dokar sanya takunkumin yaki da cutar korona.
Wasu rahotannin sun bayyana yadda wasu 'yan bikin suka rika danne wasu mutanen saboda mummunan matsi har ta kai ga wasunsu na kwance kan wadanda aka danne.
Yawancin wadanda suka mutu matasa ne, wadanda shekarunsu na haihuwa ba su zarce 20 da wani abu ba. Sai dai an tabbatar da 19 cikinsu 'yan kasashen waje ne.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton, ba a san dalilin da ya haddasa wannan turereniyar ba.
Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol ya umarci a kafa wani kwamiti da zai kula da lafiyar wadanda suka sami raunuka.
Ya kuma kaddamar da wani bincike kan musabbabin turereniyar.
Wannan ne dai iftila'i mafi muni da kasar Koriya ta Kudu ta gani tun bayan da wani jirgin ruwa ya nutse kuma ya yi sanadin halakar fiye da mutum 300 a garin Sewol na kasar.










