Me dokar ƙwace gonaki a Afirka ta Kudu da ta harzuƙa Trump ta ƙunsa?

Hoton hannun wani mutum riƙe da rairayi a lardin Limpopo, na Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴan Afirka ta kudu dama na son a alaƙanta su da gonaki
    • Marubuci, Farouk Chothia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na cikin tsaka mai wuyar siyasa bayan amincewa da dokar da ta bai wa gwamnati ikon ƙwace wasu gonaki ba tare da biyan diyya ba.

Dokar - wadda har yanzu ba a fara aiwatar da ita ba - ta ja hankali Shugaban Amurka Donald Trump, wanda yake kallonta a matsayin nuna wariya ga manoma fararen fata.

Jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayi da ƙungiyoyin jan ra'ayin jama'a a Afirka ta Kudu na adawa da dokar, suna masu cewa za su ƙalubalanci Dokar Ƙwace Karɓar Gonakin - kamar yadda aka sanya mata suna - a gaban kotu, saboda tana barazana ga ƴancin mallakar kadara, kamar yadda suka yi bayani.

Gwamnatin Ramaphosa ta ce dokar ta bayar da damar biyar diyya a wuraren da ake ƙwace filayen da yawa, kuma akwai buƙatar ƙarin sauye-sauye domin ƙara wa baƙaƙe damar mallakar gonaki.

Fararen fata ne suka mallaki mafi yawan gonaki a ƙasar.

A lokacin da Nelson Mandela ya karɓi ragamar ƙasar fiye da shekara 30 da suka gabata, ya kawo ƙarshen wariyar launin fata, an alƙawarta cewa za a magance matsalar rashin mallakar gonaki ga baƙaƙen fata, ta hanyar saye da sayarwa da wanda ya ga dama, to sai dai masu suka na ganin hakan na kawo jan ƙafa da tsada musamman ga baƙaƙen fata.

Me ake ƙwacewa ba tare da diyya ba?

A mafi ƙarancin lokuta gonaki ne idan ana buƙatarsu ''domin amfanin jama'a'' , kamar yadda wani masanin shari'a ya shaida wa BBC.

Duk da cewa ana iya amfani da gonakin wajen haƙo ma'adinai da ruwa, kamar yadda masanin shari'ar ya yi ƙarin haske.

Mabasa da Karberg sun shaida wa BBC a ra'ayinsu cewa bai kamata a ƙwace gonakin da ake nomansu ba tare da biyan diyya ba.

Sun ƙara da cewa ana ƙwacen kowace irin gona ba tare da diyya ba a wuraren ƙalilan

  • Alal misali, idan mamallakin gonar ba ya amfani da ita, kuma yana riƙe da ita domin wata ''mummunar manufa''.
  • Ko idan mamallakin ya yi "watsi da ita ta hanyar kasa nuna ikonsa a kan gonar duk kuwa da cewa zai iya yin hakan''.

Lauyoyin sun ƙara da cewa za a iya biyan mamallakan filayen diyya, idan za a yi gine-gine ko haƙo ma'adinai.

Me ya sa ake biyan diyya da kuɗi ƙalilan?

Gwamnati na biyan diyyar gwargwadon darajar gona a kasuwa, duk kuwa da cewa wannan ba ya cikin kundin tsarin mulkin da aka ci gaba da amfani da shi bayan ƙarewar mulkin fararen fata marasa rinjaye a 1994, a cewar lauyoyin.

Lauyoyin biyu sun ƙara da cewa duka ƙwace gonakin da ake yi ''yana da tsarin da ya kamata a bi domin aiwatar da ƙwacen,'' ciki har da damar da mamallak filayen ke da shi na zuwa kotu idan ba su gamsu ba.

To amma ana iya biyan diyya ƙalilan da ba ta kai darajar filayen a kasuwa ba, idan za a yi amfani da filin domin ''amfanin jama'a'', kamar gina makarantu ko titunan jiragen ƙasa.

Gwamnati za ta iya mallakar gona?

Farfesa Ruth Halla na Jami'ar Yammacin Cape ta shaida wa BBC cewa fiye da gonaki 80,000 a gwamnati ta ƙwace har yanzu ba a daidaita ba.

A yankunan gabashin ƙasar, baƙaƙen fata kan yi aiki a gonaki kyauta domin masu gonakin su yanka musu ɗan wurin da za su zauna su da dabbobinsu.

Gwamnati na son mayar da mallakar gonakin ga masu kwadagon, kuma hakan bai ''dace'' ba a yi tunanin za ta biya darajar gonakin, a cewar Farfesa Hall.

A cikin shekaru 30 da suka gabata, gwamnati ta yi amfani da ikon da ake da ita don kwace kadarorin - tare da biyan diyya kasa da kimar kasuwa - har sau wajen 20, in ji ta.

Farfesa Hall ta ƙara da cewa, sabuwar dokar na da nufin kawo sauƙi da rahusa wajen mayar da filayen ga baƙaƙen fata waɗanda aka "kwace" wa su a lokacin mulkin 'yan tsiraru ko kuma aka tilasta musu zama 'yan haya na dogon lokaci saboda ba za su iya mallakar fili ba.

Wasu ƴan Afirka ta Kudu fararen fata ke nuna goyon bayansu kan dokar da Shugaba Trump na Amurka ya amince da ita na ba su matsayin ƴangudun hijira.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Gwamnati ta musanta cewa tana nuna wariya ga manoma fararen fata

Malamar jami'ar ta ce abn da ya sa Trump ke adawa da sabuwar dokar shi ne savoda a cewarsa tana nuna wariya ga manoma fararen fata tare da ''ƙwace'' gonakinsu, wani zargi da gwamnatin ƙasar ta sha musantawa.

A cikin watan Fabrairu ne Trump ya katse tallafin da yake bai wa Afirka ta Kudu, kuma a cikin watan Afrilu ya ba da sanarwar saka harajin kashi 30% kan kayayyaki da kayayyakin amfanin gona na Afirka ta Kudu, kodayake daga baya an dakatar da hakan na tsawon kwanaki 90.

Bayan haka mako biyu da suka gabata Trump ya titsiye Ramaphosa a ofishinsa bayan da ya yi masa bazata da wani bidiyo da ke ɗauke da labaran zargin cin zarafin farar fata - kodayake daga baya an musanta labaran da ke cikin bidiyon.

Me ƴan ƙasar ke cewa?

Kamar dai Donald Trump, jam'iyya ta biyu mafi girma a gwamnatin haɗaka ta Ramaphosa, Democratic Alliance (DA), tana adawa da wannan doka.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar 26 ga watan Mayu, jam'iyyar ta ce manyan shugabanninta sun yi watsi da batun "rashin biyan diyya".

Kodayake, ta amince da manufar biyan diyya na adalci da adalci maimakon biyan diyya-darajar kasuwa, inda ta ƙara da cewa ya kamata a "koli ta yanke hukunci"

Wani abin mamaki, Jaco Kleynhans na ƙungiyar Solidarity Movement, wata ƙungiya mai fafutikar kare muradun fararen fata, ya ce yayin da sabuwar dokar za ta iya "rusa" wasu 'yan kasuwa kuma yana adawa da ita, bai yi imanin cewa za ta kai ga "ƙwashe manyan gonakin noma ba".

Ƙungiyar masu kadarorin Afirka ta Kudu ta ce bai dace ba a ba da "diyya mara kyau" ga mai shi da ya rike filaye don hasashe.

Me gwamnati ke cewa?

Ministan ayyukan jama'a na Afirka ta Kudu Dean Macpherson, ya kare wannan doka, inda ya soki jam'iyyarsa - DA.

Ministan shi ke kula da sabuwar dokar, kuma a wani taron tattaunawa kan dokar, ya bayyana cewa, yayin da yake da wasu matsaloli game da dokar, za ta kasance "mai kawo muhimmin ci gaba" tare da samar da kariya ga masu gonaki.

Ya ƙara da cewa dokar za ta iya taimakawa wajen kawo ƙarshen buƙatun da ake ɗora wa ƙasar, kuma a wasu lokutan "rashin biyan diyya" na iya zama hujja.

Ya bayar da misali da matsalolin da hukumar samar da wutar lantarki ta ƙasar Eskom ke fuskanta.

Tana shirin ƙaddamar da hanyar sadarwa mai tsawon kilomita 4,500 (mil 28,000) na gonaki domin bunƙasa wutar lantarki don kawo ƙarshen matsalar wutar lantarki a ƙasar.

Gabanin ƙaddamar da shirin, wasu mutane sun haɗa baki da jami'an Eskom don siyan gonakin a kan rand miliyan ɗaya (dala 56,000), sannan suka buƙaci rand miliyan 20 a kan gonakin, in ji shi.

Ministan ayyuka na jama'a Dean Macpherson ya ce ana gudanar da shirye-shiryen faɗaɗa hanyoyin sadarwa na Eskom don neman kuɗin fansa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ministan ayyuka na jama'a Dean Macpherson ya ce ana gudanar da shirye-shiryen faɗaɗa hanyoyin sadarwa na Eskom don neman kuɗin fansa

"Shin adalci ne kuma a yi adalci a ba su abin da suke so? Ina ganin hakan bai dace da moriyar al'umma ko ƙasa ba," in ji Macpherson.

Da yake ba da wani misali, Macpherson ya ce wasu daga cikin biranen Afirka ta Kudu na cikin wani yanayi "mummuna".

Bayan masu gonakin suka bar wuraren aka kuma kwace gine-ginensu saboda mallakarsu ba bisa ƙa'ida ba.

Kuɗin da ƙasa ke kashewa don sake gina su zai iya wuce kimarsu, kuma a irin wannan yanayi kotuna za su iya yanke hukuncin cewa masu shi sun cancanci "rashin diyya", in ji shi.

Me ya rage?

Yanzu haka dokar na cikin halin rashin tabbasa, yayin da Ramaphosa - wanda ya sanya mata hannu wata hudu da suka gabata - har yanzu bai saka ranar fara aiwatar da ita ba.

Sai dai zai iya yin hakan a koyaushe, domin ba zai so ya ƙara nuna adawa da Trump ba yayin da Afirka ta Kudu ke ƙoƙarin yin shawarwari kan yarjejeniyar kasuwanci da Amurka.

Sannan kuma a ɓangaren cikin gida, jam'iyyar DA da ke jagorantar adawa da dokar. Ta ce tana son a sake yin nazari a kansa, yayin da a lokaci guda kuma take ci gaba da ɗaukar matakin kotu don kalubalantar kundin tsarin mulkin ƙasar.