Babu ƙasar da za ta so a saka ta tsakiyar rikicin Hamas da Isra'ila - Sarkin Jordan

- Marubuci, Fergal Keane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Special correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
Ƙasashe za su ƙi a "tursasa" musu ƙaƙaba yarjejeniyar zaman lafiyar da Trump ya tsara idan aka tura su Gaza, kamar yadda Sarkin Abdallah na Jordan ya shaida wa BBC.
A ƙarƙashin yarjejeniyar zaman lafiya da Donald Trump ya jagoranci samarwa mai ƙunshe da ƙudurori 20, ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen duniya za su samar da wata rundunar daidaita lamurra wadda "za ta horas da kuma tallafa wa wata rundunar ƴansanda ta Falasɗinawa da aka tantance a Gaza, kuma za su riƙa tuntuɓar ƙasashen Jordan da Masar wadanda suke da ƙwarewa a wannan fanni."
Hamas za ta watsar da makamanta sannan ta kauce daga harkar jagorancin yankin.
"Mene ne abubuwan da suka wajabta da dakarun tsaro a cikin Gaza? Muna fatan ya zama tabbatar da tsaro ne, domin kuwa idan tursasa zaman lafiya ne, babu wanda zai so ya yi hakan," in ji Sarki Abdallah.
A wata tattaunawa da ya yi da shirin Panorama na BBC, ya ce Jordan da Masar a shirye suke su horas da jami'an tsaro Falasɗinawa.
"Wanzar da zaman lafiya shi ne ka je ka tallafa wa ƴansanda na yankin, wato Falasɗinawa, wanda Jordan da Masar a shirye muke mu horas da su da yawa, sai dai abin zai ɗauki lokaci. Amma idan za mu riƙa sintiri ne a cikin Gaza ɗauke da makamai, babu wata ƙasa da za ta so ta tsoma kanta cikin irin haka."
Kalaman Sarkin sun yi daidai da damuwar da Amurka da sauran ƙasashe ke nunawa kan cewa za a iya tsunduma su cikin rikicin Isra'ila da Hamas ko kuma na Hamas da sauran ƙungiyoyin Falasɗinawa.
Sarki Abdullah ya ce ba zai tura dakarun Jordan zuwa Gaza ba saboda ƙasarsa na da "alaƙa ta kut da ƙut da lamarin a siyasance".
Fiye da rabin al'ummar Jordan asalinsu Falasɗinawa ne, sannan kuma a cikin gomman shekaru da suka gabata Jordan ta karɓi Falasɗinawa ƴan gudun hijira miliyan 2.3, mafi yawa a yankin.
Lokacin da aka tambaye shi ko yana da ƙwarin gwiwar cewa Hamas za ta cika alƙawarin ficewa daga lamurran mulkin Gaza, sai ya ce: "Ban san su ba, to amma masu alaƙa da su ƙut da ƙut - Qatar da Masar - na da ƙwarin gwiwa cewa za su cika alƙawari.
"Idan ba mu maganace wannan matsala ba, idan ba mu nemo mafita ga Isra'ila da Falasɗinawa ba da kuma alaƙar da ke tsakanin Larabawa da Musulmai da kuma Isra'ila a ɓangare ɗaya ba, to mun shiga uku."

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tattaunawar zaman lafiyar a lokacin da ake gwabza yaƙin ya gudana ne tsakanin Qatar da Masar da kuma Amurka.
Jordan na cikin ƙasashen duniya da suka riƙa fafutikar ganin an shigar da kayan agaji zuwa Gaza tare da fitar da marasa lafiya da wadanda aka raunata zuwa wasu ƙasashe domin samun kulawa.
Sarkin ya shiga yankin a jirgin sama sau uku a yunkurin kai kayan agaji ta sama.
"Kallon abin da ya faru ta jirgin sama abu ne mai girgiza mutum," in ji shi. "Yadda aka dagargaza wannan ɓangaren na Gaza ya girgiza ni.
"Na gani da idona, kuma yadda mu ƙasashen duniya muka zura ido muna kallon wannan lamari abu ne mai sosa rai."
Sarkin ya buƙaci Shugaba Trump ya taimaka a fitar da yara 2,000 waɗanda ke fama da rashin lafiya mai tsanani daga Gaza. A wata tattaunawa da sarkin na Jordan a watan Fabarairu, Mista Trump ya bayyana abin a matsayin "mataki mai kyau".
Tun daga wancan lokacin, yara 253 ne aka kwasa daga Gaza zuwa Jordan. Gaba ɗaya kuma an kwashe sama da mutum 5,000 bisa hujja ta rashin lafiya, mafi yawancinsu an kai su Masar ne da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Qatar.
Fiye da mutanen Gaza 15,000 ke jiran a fitar da su daga yankin, cikinsu har da yara 3,000, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya.
Kafin a fita da yara da iyayensu daga Gaza sai sun fuskanci tantancewa mai tsauri daga Isra'ila da kuma ƙasar da za ta karɓi baƙuncinsu.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana tsarin a matsayin "mai matuƙar jan ƙafa".
Ɓangaren rundunar sojin Isra'ila da ke lura da ayyukan samar da kayan tallafi a Gaza - Cogat - ta dage kan cewa "tana bayar da matuƙar muhimmanci" kan hanzarta samar da kayan jin-ƙai a Gaza, ciki har da fitar da marasa lafiya "masu fama da matsananciyar rashin lafiya" zuwa wasu ƙasashen.
Ta jaddada muhimmancin tantancewa na tsaro kan duk wani mutum da zai ratsa ta cikin yankunan Isra'ila.

A tattaunawarta da shirin Panorama, Sarauniyar Jordan, Rania ta soki lamirin ƙasashen duniya saboda abin da ta bayyana gazawarsu wajen dakatar da yaƙin tsawon shekara biyu.
Sarauniyar wadda ke da tsatson Falasɗinawa ta yaba wa shugaba Trump kan ƙoƙarin da ya yi na tabbatuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas. Ta ce ya yi amfani da ƙarfin diflomasiyya da na soji da na arziƙin Amurka wajen shawo kan Isra'ila.

Isra'ila ta sha zargin Hamas da tsawaita yaƙin saboda ta ƙi sakin Isra'ilawa da take garkuwa da su, sannan ta ce ƙungiyar - wadda ƙasashen Birtaniya da Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta ƴan ta'adda - na amfani da fararen hula a matsayin garkuwa a Gaza.
Ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin Hamas ta ce sama da mutane 68,000 ne aka kashe a Gaza tun bayan fara samamen na Isra'ila a yankin.
Samamen da Isra'ila ta yi wa Gaza ya biyo bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai, wanda ya yi sanadin rayukan sama da mutum 1,200, mafi yawansu Isra'ila fararen hula, sannan suka yi garkuwa da mutum 251 a Gaza.
Tun daga lokacin, Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kama Firaiminista Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant da kuma kwamandan sojin Hamas Mohammed Deif kan zargin aikata laifukan yaƙi, duk da cewa daga baya Hamas ta sanar da cewa an kashe Deif a wani harin Isra'ila ta sama.











