Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Koriya ta Kudu za ta je Gasar Cin Kofin Duniya da Son mai jinya
Koriya ta Kudu ta bayyana 'yan wasa 26 da za su buga mata Gasar Cin Kofin Duniya ciki har da Son Heung-min, wanda ya ce ya warke daga jinya.
Son, mai shekara 30 ya ji rauni a fuskarsa, wanda aka yi ta fargabar ba zai buga gasar cin kofin duniya da za a fara ranar 20 ga watan Nuwamba ba.
Sai dai a ranar Laraba dan wasan ya bayar da tabbacin zai buga wasannin da za a yi a Qatar a cikin watan nan.
Koci, Paulo Bento ya ce baya da tabbacin ranar da Son zai fara atisaye, bayan da kasar za ta fara wasa da Uruguay ranar 24 ga watan Nuwamba.
Watakila dan wasan ya saka fuska ta kariya idan zai buga wasannin a Qatar din a cikin rukuni na bakwai da ya kunshi Ghana da Portugal
'Yan kwallon Koriya ta Kudu da za su buga Kofin Duniya:
Masu tsaron raga: Kim Seung-gyu (Al Shabab), Jo Hyeon-woo (Ulsan Hyundai), Song Bum-keun (Jeonbuk Motors)
Masu tsaron baya: Kim Min-jae (Napoli), Kim Jin-su (Jeonbuk Motors), Hong Chul (Daegu FC), Kim Moon-hwan (Jeonbuk Motors), Yoon Jong-gyu (FC Seoul), Kim Young-gwon (Ulsan Hyundai), Kim Tae-hwan (Ulsan Hyundai), Kwon Kyung-won (Gamba Osaka), Cho Yu-min (Daejon Citizen)
Masu buga tsakiya: Jung Woo-young (Al Sadd), Na Sang-ho (FC Seoul), Paik Seung-ho (Jeonbuk Motors), Son Jun-ho (Shandong Taishan), Song Min-kyu (Jeonbuk Motors), Kwon Chang-hoon (Gimcheon Sangmu), Lee Jae-sung (Mainz), Hwang Hee-chan (Wolverhampton Wanderers), Hwang In-beom (Olympiacos), Jeong Woo-yeong (Freiburg), Lee Kang-in (Real Mallorca)
Masu cin kwallaye: Hwang Ui-jo (Olympiacos), Cho Gue-sung (Jeonbuk Motors), Son Heung-min (Tottenham Hotspur)