Ko zuwan Mbappe Real zai ɗauki Champions League da Ballon d'Or?

Real Madrid ta kammala ƙulla yarjejeniyar ɗaukar Kylian Mbappe, wanda ƙwantiraginsa zai kare a Paris St Germain a karshen 30 ga watan Yunin 2024.

Ana sa ran mai shekara 25 zai koma Sifaniya da taka leda ranar 1 ga watan Yuli da zarar an buɗe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo a La Liga.

Koda yake a lokacin ana tsaka da wasannin Euro 2024, kenan za a jira ƙwazon da tawagar Faransa za ta yi ko za ta kai wasan karshe da za a yi ranar 14 ga watan Yuli.

Daga nan ne zai ɗan hutu, sai kuma ya koma Santiago Bernabeu da taka leda a matakin sabon ɗan wasan da ta fara ɗaukar a kakar nan.

Tun cikin watan Fabrairu ɗan ƙwallon tawagar Faransa ya amince baka da baka da cewar zai koma Sifaniya, sannan cikin watan Mayu aka sanar da zai bar PSG a karshen kakar nan.

Ƙwazon da Mbappe ya yi a fannin taka leda

Yana da shekara 16 ya fara buga wa Monaco wasa a Disambar 2015, wanda ya doke tarihin Thierry Henry a matakin matashin da ya fara yiwa ƙungiyar tamaula.

Haka kuma shi ne matashin da ke kan gaba a ci wa ƙungiyar ƙwallaye a tarihi, yayin da a 2016/17 yana cikin ƴan wasan Monaco da suka kai daf da karshe a Champions League.

A kuma kakar ce ya zura ƙwallo 15 a raga da ta kai Monaco ta lashe babban kofin gasar tamaula ta Faransa da ake kira Ligue 1.

Mbappe, ya koma Paris St Germain kan Yuro miliyan 180 yana da shekara 18 da haihuwa.

Ya lashe kofin duniya a 2018 a Rasha, wanda ya zama matashi mai karancin shekaru da ya ɗauki kofin duniya, bayan Pele a 1958 da cin ƙwallo a wasan karshe.

Tawagar Faransa ta doke ta Croatia 4-2 a Moscow ta lashe babban kofin duniya a fannin tamaula a ɗaya daga wasan da ya ƙayatar.

Haka kuma Mbappe ya kai wasan karshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, inda Faransa ta yi rashin nasara a hannun Argentina a bugun fenariti.

Shi ne kan gaba a cin ƙwallaye a gasar Faransa ta Ligue 1 da aka kammala, kuma karo shida a jere yana wannan bajintar.

Ya kuma lashe Ligue 1 karo bakwai a tarihi, wanda ke fatan ɗaukar Champions League da kuma ƙyautar Ballon d'Or nan gaba.

Sai dai kafin nan yana fatan zai taimakawa kasar ta lashe Euro 2024 da za ta buga a Jamus a bana.

Ƙwantiragin da ya ƙulla da Real Madrid

Mbappe ya lashe kofin duniya a 2018, kuma shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a PSG mai 256 a raga, tun bayan da ya koma ƙungiyar aro daga Monaco a 2017.

Ya amince da yarjejeniyar da za ta kare a Real zuwa karshen 2029, zai ke karbar £12.8m a kowacce kaka.

Haka kuma zai karɓi karin ladan £128m wato na tsarabe-tsarabe da za a biya cikin shekara biyar, kuma zai rike kudin tallace-tallacensa.

Real Madrid ce ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla da tazarar maki 10 tsakani da Barcelona, wadda ta yi ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta 2023/24.

Haka kuma Real Madrid ce ta ɗauki Champions League na bana na 15 jimilla, bayan da ta doke Borussia Dortmund 2-0 a Wembley.