Abin da mutane ke cewa kan hukuncin zaɓen gwamnan Kano

f

Asalin hoton, Facebook/Nasiru Yusuf Gawuna

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Al'umma a ciki da wajen Kano, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a kan zaɓen gwamnan jihar.

A ranar Juma'a, kotun da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, inda ta jaddada Nasiru Yusuf Gawuna na APC, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

Hukuncin ga dukkan alamu, ya zo wa da wasu da matukar bazata, musamman magoya bayan gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP.

Ya dai ɗaukaka ƙara ne zuwa kotun da fatan za ta rushe hukuncin kotun farko.

A ɗaya ɓangaren kuma, magoya bayan Nasiru Yusuf Gawuna na APC na cike da murna har kunne, kasancewar hukuncin ya yi musu daɗi.

Tun gabanin yanke hukuncin ne, mutane suka yi ta tafka muhawara kan fatansu game da hukuncin, haka ma bayan yanke shi.

Ma'abota shafukan sada zumunta sun yi amfani da maudu'ai daban-daban wajen tofa albarkacin bakinsu.

Alal misali a shafin X da a baya aka fi sani da Twitter, an kaddamar da maudu'in #Kano wanda ya zuwa ƙarfe 3:20 na ranar Juma'a, aka yi amfani da shi sau fiye da 46,000.

Ga abin da wasu ma'abota shafin ke cewa game da hukuncin.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Ƙaramar ministar birnin tarayya, Dakta Mariya Mahmoud Mairiga, wadda 'yar asalin jihar Kano ce ta ce: "Ina taya ɗan takarar gwamnan ƙarƙashin jam'iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna, tare da mataimakinsa Murtala Garo kan nasarar da suka samu a yau".

Shi kuwa Nasiru Fulata godiya ya yi ga Allah sannan ya ce

"Mai girma gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, Allah ya sa jinkirin adalci ya zame maka alkari, Allah shi ne mai iko a kan komai kuma da shi muka dogara. Muna da yaƙinin gaskiya za ta bayyana a kotun Koli".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Shi kuwa wani mai suna Murad da ke amfani da shafin cewa ya yi

"Injiniya Abba Kabir zai ci gaba da kasancewa gwamnan jihar Kano, har sai idan kotun ƙoli ta sauke shi. Muna fatan Allah ya dafa mana a wannan shari'a da ma bayanta".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Su ma ma'abota shafin Facebook, ba a bar su a baya ba, wajen bayyana ra'ayoyinsu kan wannan hukunci.

Bashir Ahmad hadimin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, bayan ya gode wa Allah, ya ce "A kotun ɗaukaka ƙara ma Allah ya bai wa Gawuna Nasara. Allah mun gode maka".

.

Asalin hoton, Facebook/ Bashir Ahmad

.

Asalin hoton, Facebook/Maryam Ibrahim Iliyasu

Bayan da ta yi godiya ga Allah sai ta ce "Gawuna da Garo sun iso".

.

Asalin hoton, Facebook/ Abdulwahab Sani

Shi kuwa, Abdulwahab Sani tsayawa ya yi a tsakiya inda ya ce "Ba ni da matsala da kowanne, ni dai fatana ko ma waye zai jagorancemu, Allah ya ba shi ikon kyautata wa talakawan jihar Kano har da masu kuɗin cikinta".

Duk abin da ka ga ya faru shi ne hukuncin Allah.

Allah ka zaunar mana da Kano lafiya

f

Asalin hoton, X/Mukhtar m shitu

A yanzu dai zaɓi ɗaya ya rage wa gwamnan na jihar Kano, wanda shi ne zuwa kotun ƙolin ƙasar domin ƙalubalantar wannan hukunci.

Kotun ƙolin ce dai kawai take da hukuncin ƙarshe game da batun, idan ta yi watsi da wannan hukuncin, to Abba Kabir Yusuf zai ci gaba da zama a matsayin gwamna.

Idan kuwa ta tabbatar da hukunci, to ba makawa zai sauka, inda za a rantsar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin gwamna ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Kuma idan har hakan ta tabbata jihar Kano ka iya ficewa daga cikin jihohin ƙasar da za a riƙa gudanar da zaɓen gwamnan a lokaci guda, saboda wannan batu.