Abin da ya sa SERAP ta maka INEC kotu

Shugaban INEC

Asalin hoton, other

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta shigar da hukumar zaben kasar INEC kara a gaban kotu, kan gaza gurfanar da masu hannu a rikice-rikicen zabe a gaban shari’a.

SERAP ta ce INEC ta gaza yin aikinta don haka ba ta da wani zabi da ya wuce neman kotu ta tilasta ma ta yin abun da ya dace.

SERAP ta ce idan har ana kyale masu aikata laifukan zabe suna cin bilis ba tare da hanzarta gurfanar da su a gaban shari’a ba, hakan tamkar ba wa wasu lasisin ci gaba da aikata laifukan ne.

Kungiyar ta ce a Najeriya yanzu an kai wani mataki da cikin gadara wasu kan tayar da hankali a rumfunan zabe domin an san sakamakon hakan zai iya sa a soke zaben.

Mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP, Kolawole Oluwadare, ya shaida wa BBC cewa, sun shigar da INEC kara ne saboda bukatar kungiyarsu da ma sauran masu ruwa da tsaki kan bukatar INEC ta yi aikinta.

Ya ce,” Aikinta shi ne gurfanar da wadanda ke da hannu a rigingimun zabe, mun aika musu wasika, amma sakamakon rashin daukar mataki shi ne ya sa muka ga ba mu da wani zabi illa gurfanar da INEC din gaban kuliya.”

Mr Oluwadare, ya ce matakin nasu zai taimaka wa dimkoradiyya da ma harkar zaben kasar don kaucewa sake afkuwar hakan a nan gaba.

Martanin INEC

Hukumar zaben Najeriyar INEC, ta mayar wa da SERAP martani kan matakin nata, inda ta ce kungiyar ta yi gaggawa domin da ta yi hakuri ta ga irin matakin da za a dauka.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Aikin hukumar zabe shi ne shirya zabe da gudanar da shi, amma kama masu aikata laifi a lokacin zabe alhaki ne na jami’an tsaro, in ji Hajiya Zainab Aminu, mai magana da yawun hukumar INEC.

Ta ce,” Idan jami’an tsaro musamman ‘yan sanda suka kama mutum ya aikata laifi a lokacin zabe to za su kama shi sannan su yi bincike kuma su aikowa hukumar zabe rahoton da suka tattara.”

Ta ce Idan har rahoton da aka aika wa hukumar zabe ya tabbatar da cewa an aikata wannan laifi, daga nan sai INEC ta kai mutum kotu don alkalai su yi bincike sannan su yanke hukuncin da ya dace.”

“Kungiyar SERAP, ta yi gaggawa da gajen hakuri domin hukumar ‘yan sanda ma ba ta gama bincike ba, ballantana ta kawo rahoton da ta tattara sannan kuma har mu dauki mataki na gaba da ya dace.”

Ta ce, su ma burinsu a kodayaushe shi ne su ga an hukunta duk wanda aka samu da laifi a yayin zabe.

Batun tashin hankali a lokutan zabe a Najeriya, ya zama ruwan dare gama duniya duk da jibge jami’an tsaron da ake a wuraren da ake zaben.