Wakilin BBC a Gaza: ‘Na sare, rayuwa ta tarwatse a kan idona’

Rahoto daga wakilin sashen Larabci na BBC Adnan El-Bursh

A birnin Khan Younis, Gaza

Matasa maza sanye da wandon Jins da riga mai dogon hannu, sun jeru tamkar ana sallar janaza a gaban asibitin Nasser da ke Khan Younus.

Daruruwan mutane ne suka mutu, tun bayan da Isra'ila ta zafafa kai hare-haren bama-bama a kudancin Gaza a ranar 1 ga watan Disamba.

Wata mummunar rana mai cike da tashin hankali ce a gaban kofar shiga sashen gaggawa da hadari a asibitin.

Ma'ikata sanye da kayan asibiti, suna kai-komo, muryoyi na tashi yayin da maza suka yi dandazo wuri guda.

Duk wani umarni da ake bayarwa ba ya tasiri, mutane na cikin rudu da kidima, wasu a gajiye matuka.

Wata mota ce ta tsaya a wurin, an kuma danna odarta da kunna fitilunta, cikin gaggawa aka fito da wani matashi aka dora kan gadon daukar marassa lafiya aka yi gaggawar shiga da shi cikin asibitin.

Ba a jima ba, wata motar ta shigo a sukwane, ta yi budu-budu da kura, aka yi gaggawar fito da wani yaro, da kafafunsa ya taka, zai kai akalla shekara huɗu zuwa biyar.

Washegari, a can wata unguwa, wata uwar 'ya'ya shida mai suna Samah Ilwan ce ke neman taimako.

"Ina son aika sako ga duk duniya, da kasashen Larabawa," in ji ta.

"Ina son shaida wa duniya babu abin da muka yi, ba mu aikata laifi ba."

Sai ta daga gorar ruwa guda biyu da babu komai a ciki, ta ce 'ya'yanta mata biyar da namiji daya suna tsananin bukatar ruwan sha.

"Mun zama tamkar maguna da karnuka. Kai karnuka da maguna sun fi mu gata tun da suna da wurin zama. Amma mu ba mu da komai. Gararanba kawai muke yi a kan tituna."

Tun ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kaddamar da hare-hare kan Isra'ila, rayuwa ta tsananta.

Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da Birtaniya sun ayyana Hamas a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, wadda ta kashe Isra'ilawa akalla 1,200, tare da yin garkuwa da sama da mutum 240, tare da tsare su a Gaza.

Daga nan Isra'ila ta fara kai munanan hare-haren bama-bamai da makamai masu linzami babu kakkatawa.

Ma'aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta, ta ce sama da Falasdinawa 15,800 aka kashe daga fara yakin, kuma yawancinsu mata da kananan yara.

An amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 7, wadda a lokacin ne aka yi musayar Isra'ilawan da Hamas ke tsare da su da kuma Falasdinawan da Isra'ila ke tsarewa a gidajen kasonta, yawancinsu tun kafin fara yakin na baya-bayan nan.

Wannan ne wuri mai aminci musamman ga babbar motar tauraron ɗan'adam, ana samun layin intanet mai kyau, amma kwanaki kadan da suka wuce komai ya kacame.

A koda yaushe burina da alfaharina shi ne zama dan Jarida, amma yanzu lamuran na neman fin karfina. Rayuwa na neman karewa kan idona.

Lokaci zuwa lokaci, nakan samu damar yin balaguro zuwa tsakiyar Gaza domin ziyartar iyalina. Amma yanzu da Isra'ila ta rufe wata hanya, dayar da ke bude na da hatsari, ina ji ina gani na hakura da zuwa.

Asalinmu 'yan arewacin Gaza ne, amma sai muka tsero kudanci tare da iyalina da ƴan'uwana, bayan umarnin da sojin Isra'ila suka bai wa mazauna yankin inda suka ce Kudancin Gaza ya fi aminci da tsaro.

A yanzu suna gargadin mu tattara kayanmu mu bar yankin, saboda suna shirin kai farmaki ta kasa a Khan Younus, sun shaida mana mu koma Rafah da ke iyaka da Masar wanda nan ma a wani bangaren kudancin ne.

Duk da irin abubuwan da suka same ni da iyalina da ƴan'uwana tun fara wannan yakin, wannan ne karon farko da na ji na sare, na rasa yadda zan yi, ba ni da wani karfi ko iko, komai ya kubuce daga hannuna.

Na saba bai wa iyalai da ƴan'uwana kariya da tabbatar da tsaronsu, kullum akwai shirin da nake yi don tabbatar da hakan. Amma yanzu na rasa tudun dafawa, ban san wane matakin zan dauka ba.

Shin na tafi Rafah, na ci gaba da aiki, in yi fatan iyali da ƴan 'uwana za su kasance cikin aminci? Ko dai na yi kokarin komawa inda suke, na daina dauka da aiko rahoto, idan kuma mai aukuwa ta kasance, ko ba komai za mu mutu tare?

Ba na fatan wani mahaluki ya samu kan shi cikin hali irin wannan, wanda ba abu ne mai sauki ba.