Wane ne Sheikh Nasiru Kabara, shugaban ɗarikar Qadiriyya na Afirka?

..

Asalin hoton, Darul Ƙadiryya

Bayanan hoto, Sheikh Nasiru Kabara 1912 -1996
    • Marubuci, Usman Minjibir
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 7

A ƙarshen makon da ya gabata ne mabiya ɗariƙar Qadiriyya a Najeriya suka gudanar da bikin Maukibi a birnin Kano a karo na 75.

Mabiya ɗarikar sun ce suna gudanar da bikin ne a duk ranar Asabar ta farko a watan Rabi al-Thani ta kowace shekara, amma idan Asabar ɗin farko ba ta kai ranar 10 ga watan ba, sai a gudanar da bikin a ranar Asabar ta biyu.

Dubban ƴan ɗarikar Ƙadiriyya daga Najeriya da ma wasu ƙasashen waje ne ke halartar taron bikin, inda ake zagaye a cikin birnin Kano tare da waƙe da yabon Annabi da kuma zama domin karance-karancen littafan addini, musamman na tarihin Annabi da Sheikh Abduqadir Jelani da wasu magabata.

Sheikh Muhammadu Nasiru Kabara, jagoran ɗariƙar Qadiriyya ne ya assasa bikin kimanin shekara 75 suka gabata da manufar sauya akalar taruka da al'adun maguzanci da ake yi a lokacin.

Shin wane ne Sheikh Nasiru Kabara? BBC ta yi nazari dangane da tarihin wannan fitaccen malami na Afirka.

Haihuwarsa

..

Asalin hoton, Daha Tijjani

An haifi Sheikh Nasiru Muhammad Kabara ranar Alhamis ta watan Shawwal na Hijra ta 1331wanda ya yi daidai da shekarar 1912.

An haifi Malam Nasiru Kabara ko kuma Amirul Jaishi kamar yadda mabiya ke yi masa lakabi a ƙauyen Gurungawa da ke wajen birnin Kano.

"An haife shi a Gurungawa wani ɗan ƙauye ne da ke wajen Kano wanda yanzu ma ya haɗe da gari, yana nan gaban gidan Zoo. Saboda a nan ne gonakin iyayensu suke. Bisa al'ada idan lokacin noma ya yi su kan tafi da iyalinsu su tare a can," in ji Farfesa Matabuli Shehu Kabara, malami a sashen koyar da Larabci a jami'ar Bayero da ke Kano sannan kuma ɗa ga babbar jikar Sheikh Nasiru Kabara.

"Mahaifinsa ya tafi da mahaifiyarsa wadda da ma ita ƴar Gurungawa ce, aka haife shi. To amma kuma bayan haihuwarsa sai iyayen nasa suka koma gida Kabara, inda a nan ne ya yi rayuwarsa har kuma lokacin rasuwarsa." a cewar babban ɗan nasa.

Ma'anar Kabara

..

Asalin hoton, Daha Tijjani

Kabara na ɗaya daga cikin unguwanni a birnin Kano, waɗanda sunansu ya sauya daga yadda ake kiran su a baya.

"Sunan unguwar Jarƙasa amma tun bayan zuwan kakan Amirul Jaishi wato Malam Umaru Kabara sai sunan unguwar ya rikiɗe ya koma Kabara. Kabara sunan gari ne a birnin Timbuktu na ƙasar Mali. Kuma daga can Malam Umaru ya zo Kano," in Farfesa Matabuli.

Neman ilimi - Tasirin Malam Ibrahim Natsugune

..

Asalin hoton, Zinariya/Facebook

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Saɓanin mafi yawancin yara da ke gudun karatu, shi Sheikh Nasiru Kabara ya kasance yana son a kai shi makarantar ne tun ma bai isa zuwa makarantar ba.

"Tun yana ɗan mitsitsi yake kuka sai an saka shi a makaranta, Yakan yi mafarkin ya je makaranta saboda duk lokacin da ya farka daga barci to zai tafi makaranta da ke Lagwanawa kusa da Daneji a nan Kano. A nan ne makarantar allonsu take."

"Bayan ya kammala sauke Ƙur'ani sai kuma ya koma karatun littattafai a wurin malamansa da dama waɗanda su ne manyan malaman Kano na lokacin musamman kawunsa Malam Ibrahim Natsugune wanda ya tasirantu da shi ƙwarai da gaske. A wurinsa ya yi yawancin karance-karancensa." In ji Farfesa Matabuli.

A gwagwarmayarsa ta neman ilimi a birnin Kano, Malam Nasiru Kabara yakan je zaurukan malamai aƙalla guda biyar a kullum.

"A makarantun nan biyar a kullum yana ɗaukar littafi guda 30 kuma ba ya rintsa idanunsa domin yin barci komai nisan dare har sai ya duba da yin bitar dukkannin littafan nan guda 30. Wani lokacin ma yana bitar su zai ji ana kiran sallar Asuba."

"Yana faɗa mana cewa shi a tsawon rayuwarsa ta neman ilimi bai taɓa yin shimfiɗa tasa ta kansa ba wai domin ya kwanta bacci. Sai dai idan barci ya tarar masa sai ya gyalle shi wani lokacin sai ya farka ya gan shi a kan litattafan." Kamar yadda Farfesa Matabuli ya yi ƙarin haske.

Sheikh Nasiru Kabara ya yi fice a ɓangaren Larabci da kuma Tauhidi duk da cewa yana da ƙwarewa a kusan dukkannin fannonin addinin Musulunci.

Malamansa

..

Asalin hoton, Daha Tijjani

Sheikh Nasiru Kabara ya tasirantu da manyan malaman Kano ƙwarai da gaske a shekarun ɗalibtarsa.

  • Sheikh Ibrahim Na-Tsugune wanda baffansa ne
  • Alƙali Ibrahim Ibnul Ustaz: Tsohon alkalin alƙalai na Kano.
  • Alƙali Mustapha: Alƙalin Bichi.
  • Malam Yunusa Ciromawa
  • Malam Inuwa, Limamin Zawiyya.
  • Malam Sani: Babban Limamin Kano na wannan lokacin

"Malam ya sha faɗa da bakinsa cewa ya tasirantu da mutanen nan ƙwarai da gaske amma babu kamar mutum biyu wato Malam Na-Tsugune da Alƙali Ibrahim." In ji Farfesa Matabuli.

Ta yaya Sheikh Kabara ya karɓi Qadiriyya?

..

Asalin hoton, Daha Tijjani

Sheikh Nasir Kabara ya karɓi ɗarikar Qadiriyya a birnin Kano wurin wani fitaccen malamin ɗarikar mai suna Sheikh Sa'ad da ke unguwar Alfindiƙi a birnin a Kano.

"Tun yana ƙaramin yaro shi Malam ya nemi izinin baffan nasa, Malam Ibrahim Na-Tsugune ya ce yana son ya karɓi wuriɗin ƙadiryya kuma nan take ya haɗa shi da mutum aka kai shi Alfindiƙi aka ba shi." In ji Farfesa Matabuli Kabara.

Daga baya kuma Malam Nasiru Kabara ya nemi zama muƙaddami inda yake son fara kira a tafarkin, sai ya rubuta wasiƙa ya kuma bai wa Sarkin Kano na wannan lokacin, Sarki Abdullahi Bayero, da zai je aikin Hajji.

"Ya faɗa masa cewa idan ya je Madina akwai wani babban malamin ɗarikar Qadiriyya mai suna Shehu Hassan Assaman ya ce ya kai masa takardar yana son yanaɗa shi a matsayin muƙaddamin Qadiryya ya yi masa izinin fara yaɗa wuridin ɗarikar. Kuma ya rubuto masa martani ɗauke da izini a shekarar 1355, lokacin shi malam bai fi shekara 20 da ɗan wani abu ba." In ji Farfesa Matabuli.

Bayan da shehun Malamin ya samu izini sai ya fara assasa zawiyya ta hanyar mayar da soron gidansa wurin zikiri, inda ya samu mutum huɗu da suke gudanar da ayyukan ɗarikar tare.

..

Asalin hoton, Daha Tijjani

Kuma zawiyyar tasa ta zama ta biyu a fagen Qadiriyya bayan ta Alfindiƙi.

Kafin assasa zawiyyar ta Kabara, mabiya ɗarikar Qadiriyya suna yin zikiransu ne a ɗaiɗaiku ba haɗuwa a yi a jam'i ba.

" Mutanen da suka fara zawiyyar tare sun haɗa da Sheikh Muhammadul Bashir wanda shi ne babban almajirinsa da Malam Muhammadu Tukur da ake kira Baban asibiti da Malam Sulaimanu Hausawa sai kuma shi Malam wanda ya kasance cikon na huɗun." In ji Farfesa Matabuli.

Littafai nawa Sheikh Nasiru kabara ya rubuta?

..

Asalin hoton, Kabara Family

Allah ya huwace wa Sheikh Nasiru Kabara basirar rubutu inda mafi yawancin rubuce-rubucensa yake yin su domin warware wata mas'ala da aka bujuro masa.

Kuma yakan yi rubutun ne a harshen Larabci da kuma Hausa, inda wani lokacin ka iya zama zube ko kuma waƙe.

Masana da masu nazarin littafan marigayi Sheikh Nasiru Kabara sun ce har kawo yanzu babu ƙididdigar yawan littafan da ya rubuta kasancewar rubutunsa na hannu ne.

"Gaskiya ko ni ɗin nan, a kundin digirina na uku na kawo sunayen littafi sama da 150 ya doshi kusan 200. To amma bayan na gama kuma sai na ga wasu da dama daga baya kuma ban ma saka su a ciki ba. Mafi yawa daga littafan ba a buga su ba," kamar yadda Farfesa Matabuli ya yi ƙarin haske.

Farfesa Matabuli ya lissafa kaɗan daga cikin littafan Sheikh Nasiru Kabara:

  • Fassarar Alƙur'ani zuwa harshen Hausa mai suna Ihsanunl Mannan Fi Ibrazul Khabayin All-Qur'ani
  • Fassarar Ashifa zuwa harshen Hausa mai suna Yambu'ussafa Fi Tahri Bayanatul Shifa
  • Littafin Sira mai baiti 1000 mai suna Alfiyatul Siyar
  • Da'awatul Gausi Ilallah
  • Risalatuk Kabariyya Bi Shuruɗi Adabizzikhir Fi Aɗɗariqatul Qadiriyya
  • Diwani a Larabci mai suna Sibhatul Anwar
  • Diwani mai suna Nagamatuɗɗar
  • Diwani mai tattare da ƙasidunsa a harshen hausa mai suna Diwanul Haƙa'iƙil Islamiyya.

Sheikh Nasiru a matsayin malamin makarantar zamani

..

Asalin hoton, Daha Tijjani

Sheikh Nasiru Kabara ya koyar a makarantu na zamani tun gabanin ya kafa tasa makarantar.

Ya koyar da harshen Arabiyya a makarantar firamare ta gidan Sarki wadda su Janar Murtala Ramat Muhammad da su Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero da su Mahe Bashir Wali suka halarta.

Malam Kabara ya kuma koyar a makarantar gidan Makama kafin ya koma makarantar da ake kira Judicial School da ke Shahuci a birnin Kano inda har ya zama shugaban makarantar.

Shi ne ya taka rawar da sai da aka mayar da makarantar babbar makaranta.

A 1958 ne kuma Sheikh Nasiru Kabara ya kafa makarantarsa ta ƙashin kansa ta nizami wadda ake kira Ma'ahad.

"Yana kuma daga cikin mutanen da suka fara buɗe makarantar matan aure domin ƴaƴansa mata manya da matansa suke koyarwa''.

''Na tuna lokacin da idan ƙarfe 10 na dare ta yi ƙofar gidan yana cika da motoci an zo ɗaukar matan da suka halarci makarantar." In Matabuli.

Sheikh Kabara – Mai sassauci da tsauri

..

Asalin hoton, Daha Tijjani

Bayanan hoto, Sheikh Nasiru Kabara tare da Sheikh Abubakar Gumi a yayin aikin Hajji.

Sheikh Nasiru Kabara musamman ga waɗanda suka san shi ko kuma suka zauna da shi, sun tabbatar da cewa mutum ne shi mai halayya biyu wato ta sassauci da zafi a lokaci guda.

Yana da sassauci a fagen mu'amala da jama'a amma kuma yana da tsauri idan aka taɓa aƙidarsa.

"Duk da haka akwai wani lokaci da malam ya fahimci halin da Musulman Najeriya ke ciki ya ga lokaci ya yi na fara kiran háɗin kan Musulmi da ya kira "Wahad".

''Da ni aka je gidan Sheikh Abubakar Gumi wanda ɗalibinsa ne inda aka kai masa ziyarar neman háɗin kai." In ji Farfesa Matabuli.

A ƙarshe Sheikh Nasiru Kabara ya rasu ranar Juma'a 4 ga watan Oktoban 1996, a gidansa da ke birnin Kano yana da shekara 84 a duniya.