Me ya sa ba a gama finafinan Hausa masu dogon zango?

Izzar so

Asalin hoton, Lawan Ahmad/Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

Wasu masu kallon finafinan Hausa suna ci gaba da tambayar wai me ya sa ba a kawo ƙarshen finafinan Hausa masu dogon zango, tambayar da har yanzu ba ta samu cikakkiyar amsa ba.

Daga cikin finafinan da aka daɗe ana yi akwai fim ɗin Izzar so mai dogon zango, wanda ya kasance cikin finafinai masu dogon zango na farko-farko.

Fim ɗin wanda aka fara sakin fitowa na ɗaya a ranar 12 ga Afrilun shekarar 2020, an yi fitowa wato episode guda 100, sannan aka koma Izzar so sabon salo daga fitowa ta 101, zuwa fitowa ta 150.

Daga nan kuma sai suka koma Izzar so takun farko, wanda shi ake yi yanzu, kuma ana fitowa ta 10.

Sai dai ba fim ɗin Izzar so ba ne ya fi daɗewa ana yi, domin akwai fim ɗin Daɗin Kowa na tashar Arewa24, wanda zuwa yanzu an haura shekara 10 ana yi.

Fim ɗin Gidan Badamasi wanda shi ma ake kallo a tashar Arewa24, a baya an sanar da kammala shi, amma yanzu an dawo an cigaba.

Haka akwai finafinai da dama masu dogon zango da wasu suke ganin kamar ya dace a ce an dakatar da su, an shiga wasu.

A finafinan Hausa masu dogon, ana tunanin yanzu fim ɗin Watarana a Kano na Abubakar Bashir Maishadda, wanda yake da fitowa biyar kacal ne aka nuna shi a manhajar Arewa on demand na Arewa24 aka gama.

Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki.

Me ya sa ba a gamawa ɗin?

Nazir

Asalin hoton, Nazir Adam Salih/Facebook

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa ta Bakori TV, ya ce masu kallo ne ba su gaji da kallo shirin ba, shi ya sa ba zai daina ba.

Ya ce kasancewar Youtube ya daɗe kudu, amma bai je arewacin Najeriya ba ne ya sa suka gwada domin su koya wa mutane kallon fim a YouTube.

"Shi kuma wannan fim ɗin yana ciki, ko in ce shi ne ɗaya tilo da ya koya wa mutane kallo a YouTube, kuma mutane ba su gaji da kallonsa ba," in ji shi, inda ya ƙara da cewa, "ka ga babu dalilin da za mu daina."

"Na biyu kuma shi ne akwai abubuwa na addini da muke kawowa da suke tasiri a zukatan al'umma kamar soyayyar Annabi. Sannan akwai abubuwa da dama da an manta su a cikin addini, idan muka nuna sai su zama matashiya."

Fitaccen jarumin ya ƙara da cewa a sanadiyar dim ɗin akwai aƙalla mutum uku da suka karɓi addininin musulunci, wanda a cewarsa hakan na cikin abubuwan da suka sa bai daina fim ɗin ba.

A nasa jawabin a zantawarsa da BBC, fitaccen marubuci kuma furodusa, Nazir Adam Salihi, wanda yake cikin marubuta shirin Daɗin Kowa mai dogon zango, kuma forudusan shirin Gidan Badamasi, ya ce nan gaba kaɗan za a fara kammala wasu shirye-shirye.

Ya ce "mu ne muka fara finafinan nan masu dogon zango, kuma sama da shekara 10 ne da suke wuce ne muka fara zuwa yanzu. A turai irin su Ingila kuma akwai finafinai masu dogon zango da aka yi shekara 65 ana yi ba a gama ba, ka ga ba za a yi gaggawar cewa ba a gama na Hausa mu da muka fara sama da shekara 10 da suka wuce."

Sai dai ya ce akwai wasu finafinai da aka gama ɗaukarsu, "nan gaba kaɗan zuwa shekara mai zuwa za a kammala wasu finafinan, a shiga wasu daba."

A game da ko ana ƙarancin labaran ne, marubucin ya ce Hausawa na da labarai masu kyau da inganci.

A ƙarshe Salihi ya ba marubuta shawarar su dage da karatu da bincike da kuma natsuwa wajen biyayya ga gaba.

Wannan ba ci gaba ba ne - Muhsin Ibrahim

Muhsin

Asalin hoton, Muhsin Ibrahim/Facebook

Da yake jawabi kan lamarin, Dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus ya ce wannan matsala ce ga masana'antar, wadda ba za ta haifa ɗa mai ido ba.

A cewarsa, "abin da yake faruwa shi ne masu shirya finafinan suna fargabar idan suka daina fim ɗin ba dole ba ne wanda za su fara ɗin ya samu karɓuwa kamar shi," inji shi.

Sai dai ya ce wannan matsala ce babba saboda "babu labarin da ba shi da ƙarshe kuma duk haƙurin ɗan kallo ana iy ƙure shi."

Ya ce duk masana'antun fim na duniya da suka ci gaba a duk labarin da suka tsara, akwai farkonsa da tsakiya da ƙarshe.

"Shi ya sa nake ganin wannan rashin dabara ce saboda ƴan kallon da suke tunani dai dole sai sun kuɓuce musu, musamman idan sun samu wani fim da ya fi wannan."

Muhsin ya ƙara da cewa ya kamata a ce duk wani fim da za a fara, "a san cewa za a iya fara wani wanda ya fi shi ko kuma ya gaza shi. Misali shirin Labarina mai dogon zango, duk da cewa Aminu Saira ya riƙe sunan, ai na biyu ya fi na farko karɓuwa. Shi fim ɗin kamfanin UK Entertainment ai Garwashi ya fi Fatake karɓuwa," in ji shi.

Ya ce rashin gama fim yana rage wa masu kallo karsashin cigaba da kallon saboda fargabar ko sun fara kallo, suna tunanin ba za a gama ba.