Tuchel ya mayar da Rashford cikin tawagar Ingila a wasan neman gurbi

Lokacin karatu: Minti 1

Sabon kocin Ingila, Thomas Tuchel ya kira Marcus Rashford cikin tawagar ƙasar da za ta buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026.

Ɗan wasan na Manchester Uniten da ke zaman aro a Aston Villa bai samu shiga tawagar ƙasar da ta buga wasannin baya ba.

Cikin jerin ƴan wasa 26 da sabon kocin ƙasar Thomas Tuchel ya fitar, ranar Juma'a ya sanar da sunan Rashford da tsohon ɗan wasan Liverpool da ke taka leda a ƙugiyar Ajax, Jordan Henderson cikin tawagar.

Haka kuma a karon farko mai tsaron ragar Burnley, James Trafford da ɗan wasan bayan Liverpool, Jarell Quansah za su iya samun damar buga wa babbar tawagar Ingila ƙwallo ba a ke cikin tawagar

A ranar Juma'a, 21 da watan Maris ne tawagar Ingila za ta ƙarbi baƙuncin Albania a filin wasa na Wembley, kafin ranar Litinin 24 ga watan na Maris ta kara da ƙasar Latvia a wasannin neman gurbin.

Ga jerin ƴan wasa 26 da ke cikin tawagar.

Masu tsaron raga: Dean Henderson (Crystal Palace), Jordan Pickford (Everton), Aaron Ramsdale (Southampton), James Trafford (Burnley)

Ƴanwasan baya: Dan Burn (Newcastle United), Levi Colwill (Chelsea), Marc Guehi (Crystal Palace), Reece James (Chelsea), Ezri Konsa (Aston Villa), Myles Lewis-Skelly (Arsenal), Tino Livramento (Newcastle United), Jarell Quansah (Liverpool), Kyle Walker (AC Milan, loan from Manchester City)

Ƴan wasan tsakiya: Jude Bellingham (Real Madrid), Eberechi Eze (Crystal Palace), Jordan Henderson (Ajax), Curtis Jones (Liverpool), Cole Palmer (Chelsea), Declan Rice (Arsenal), Morgan Rogers (Aston Villa)

Ƴan wasan gaba: Jarrod Bowen (West Ham United), Phil Foden (Manchester City), Anthony Gordon (Newcastle United), Harry Kane (Bayern Munich), Marcus Rashford (Aston Villa, loan from Manchester United), Dominic Solanke (Tottenham Hotspur)