Yadda manufofin Isra'ila suka janyo ƙangin yunwa a Gaza

Wani yaro riƙe da tukunyar abinci yana lekowa daga shingen rabon tallafin abinci

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Emir Nader
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 7

Ana fama da yunwa a Gaza - tafiya kaɗan daga ɗaruruwan manyan motocin agaji da ke ajiye a wajen iyakokin birnin.

Yaya aka haihu a ragaya?

Ƙungiyar samar da abinci da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya shi ne kan gaba a bibiyar matsalar yunwa a duniya.

Nazarin da shirin ya yi cewa mutum dubu 500 - kashi daya bisa hudu na Falasdinawa a Gaza - na fama da kangin yunwa wani abu na mamaki.

Babban dalilin shi ne rahoton shirin da ya tabbatar da cewa yanayin da ake ciki "abu ne da aka kirkira da gangan" yayin da kungiyoyin agaji a yanzu suke zargin Isra'ila da kawo cikas ga tsarin da aka tanada na shigar da abinci zuwa zirin Gaza.

Rahoton ƙungiyar IPC ya ce ya gano cewa mutanen da ke zaune a birnin Gaza na fama da matsalolin yunwa.

Ya kuma gano cewa yunwar na bazuwa cikin sauri - inda ake sa ran yunwar za ta mamaye ragowar yankunan Gaza a Satumba.

Rahoton ya fitar da sakamakonsa bisa la'akari da muhimman abubuwa uku:

  • Yunwa: Akalla gida 1 cikin biyar na fama da raguwa ta abincin da suka saba ci
  • Rashin abinci mai gina jiki: Yaro daya cikin uku na fuskantar rashin abinci mai gina jiki.
  • Mace-mace: Akalla mutum biyu cikin kowane mutum 10,000 na mutuwa a kullum saboda yunwa ko rashin abinci mai gina hadi da wata cuta.

Idan aka samu haduwar wadannan abubuwan uku, IPC na ganin hakan a matsayin matsala ta yunwa.

IPC ta ce alamar "mace-mace" ba ta nunawa a bayanan da ake da su saboda rugujewar tsarin bibiyar al'amura. Tana ganin ba duka mace-mace ake da bayanansu ba.

An wallafa rahoton yayin da ma'aikatar lafiyar Hamas ta ba da bayanan mutuwar mutum biyu sakamakon rashin abinci mai gina jiki, abin da ya sa jumullar mace-mace ta kai 273, har da kananan yara 112.

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha musanta matsalar yunwa a Gaza inda ya ce inda ake samun yunwar, laifi ne daga kungiyoyin agaji da kuma Hamas.

Isra'ila ta zargi kungiyoyin agaji na kasa da kasa kamar Majalisar Dinkin Duniya da kin karbar kayayyakin jin kan da ke jibge a bakin iyakar Gaza, tana magana ne kan manyan motocin jin kai da ke jibge a wajen.

An ƙirƙiri matsalar yunwar

Ana duba lafiyar wani yaro da ke fama da rashin abinci mai gina jiki a asibitin Al-Rantisi da ke Gaza ranar 7 ga Agusta

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana duba lafiyar wani yaro da ke fama da rashin abinci mai gina jiki a asibitin Al-Rantisi da ke Gaza ranar 7 ga Agusta
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan shafe makonni duniya na ganin irin hotunan yara da suka kanjame sakamakon yunwa, kasusuwa sun bayyana, mutane da dama za su ji abu ne da aka dade ana tsammanin faruwar sa.

Ikon Falasdinawa na samun abinci abu ne mai sarkakiya a kusan shekaru biyun da aka shafe ana gabza yakin Gaza.

Isra'ila ta dade tana kakaba takunkumi kan kayayyakin da ke shiga Gaza kuma wadannan takunkumai sun karu bayan soma yakin ranar 7 ga Oktoban 2023 da ya samo asali bayan jerin hare-haren da Hamas ta kaddamar kan Isra'ila.

Sai dai tun Maris din 2025, yanayin ya kazance bayan da Isra'ila ta toshe hanyoyin kai kayan jin kai zuwa Gaza tsawon kusan wata uku.

Sai dai kasashen duniya suka matsa mata lamba sannan isra'ila ta ba da damar shigar da kayyadaddun kayan abinci zuwa Gaza a karshen watan Mayu.

Ta kuma bijiro da sabon tsarin rarraba abinci karkashin wata gidauniyar jin kai ta Gaza domin maye gurbin tsarin da tun farko Majalisar Dinkin Duniya ta tanada.

GHF tana da cibiyoyin rabon agaji a yankunan da sojoji suke wanda dole Falasdinawa sai sun yi tafiya mai nisa lamarin da ke jefa su cikin hadari kafin su isa wuraren, wadanda kuma suka maye gurbin cibiyoyin rabo 400 da ake da su a karkashin tsarin Majalisar dinkin Duniya.

Nemo abinci ya zama wani babban tarnaki ga Falasdinawa kuma sun sha fada mana cewa dole su zabi tsakanin yunwa da mutuwa, suna magana ne kan yadda ake harbe mutane kusan kullum a kokarin karbar abinci daga cibiyoyin rabon jin kai na GHF.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana da bayanin kisan akalla Falasdinawa 994 a wuraren rabon agaji na GHF kadai tun karshen Mayu, wasu 1,760 an kashe su a kokarin da suke neman agaji.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce galibin wadanda aka kashe sojojin Isra'ila ne suka harbe su kuma hakan ya yi daidai da bayanan shaidu da likitoci a Gaza da muka yi magana da su. Isra'ila ta sha musanta wadannan zarge-zargen.

A ƙarƙashin wannan tsarin, da Isra'ila ke sa ido a kai, matsalar yunwa a Gaza na kara ta'azzara.

Wani jirgin sama na Indonesia ya jefa kayan jin kai ta saman Zirin Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani jirgin sama na Indonesia ya jefa kayan jin kai ta saman Zirin Gaza

Yayin da ake ci gaba da matsa wa Isra'ila lambar ta bayar da damar shigar da karin abinci zuwa Gaza, a karshen watan Yuli, sai ta soma barin karin manyan motocin agaji su shiga Gaza a kullum inda kuma ta bijiro da tsarin tsagaita wuta don bayar da damar motocin agaji su shiga yankin.

An samu shigar kayan jin kai zuwa yankin a makonnin baya-bayan nan sannan kuma an ga raguwar farashin wasu kayayyaki a kasuwanni - duk da cewa kayan na da tsada a wajen akasarin Falasdinawa.

A wasu lokutan farashin garin fulawa ya kai sama da dala 85 kowane kilo daya, duk da cewa farashin ya soma raguwa.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji sun ce duk da cewa Isra'ila tana sassauta wasu daga cikin takunkuman da ta kakaba kan shigar kayan abinci zuwa zirin Gaza, har yanzu akwai gagarumar matsala wajen karbar abincin da kuma rarraba shi.

Kungiyoyin sun ce abin da ake bukata shi ne manyan motoci 600 a rana da za su rika shigar da abinci zuwa Gaza domin biyan bukatun mutane - a yanzu motocin da suka iya shiga ba su kai 300 ba.

Isra'ila ta kuma fara barin tsarin jefa abincin jin kai, abin da kungiyoyin agaji da dama suka yi suka a kai.

An kuma soki zargin da Isra'ila take cewa Hamas ce ke janyo matsalar yunwa. Rahotanni da dama har da wani rahoto na gwamnatin Amurka, sun gano cewa babu wata hujja da ke nuna cewa Hamas tana karkatar da kayan jin kai.

Ana samun wawaso kan motocin da suke shigar da jin kai zuwa Gaza - amma kungiyoyin agaji sun ce galibi Falasdinawan da ke cikin matsalar yunwa ne ke daka wawa da kuma wasu kungiyoyin da ke neman sake samun riba.

Kungiyoyin agaji sun sha fadin cewa idan har ana son a magance matsalar yunwa, to dole ne a yi ta shigar da abinci babu kakkautawa zuwa Gaza kuma a halin da ake ciki Isra'ila har yanzu Isra'ila na sanya takunkumi.

Martanin Isra'ila

Wasu jami'an gwamnatin Isra'ila sun yi watsi da rahoton IPC.

Ma'aikatr harkokin wajen Isra'ila ta zargi IPC da wallafa rahoton karya domin farantawa Hamas.

Hukumar da ke bibiyar ayyukan gwamnati a yankunan Isra'ila, Cogat ta kira rahoton na IPC a matsayin na karya da son kai.

Isra'ila ta ce IPC ta sauka daga tsarinta na duniya, inda ta rage adadin mutanen da ke fama da yunwa daga kashi 30 zuwa kashi 15 sannan kuma ta yi burus da adadin mace-mace.

IPC ta yi fatali da zarge-zargen inda ta ce ta bi tsarin da aka kafa da dadewa wajen fitar da rahotonta.

Zargin Isra'ila cewa IPC ta yi amfani da bayanan Hamas da alama na nuna cewa wasu daga cikin rahotanninta kan rashin abinci mai gina jiki a Gaza ya fito ne daga ma'aiktar lafiyar Hamas a Gaza.

Sai dai ana ganin sahihancin bayanan ma'aikatar kan mace-mace da wadanda suka jikkata yayin yakin.

Martanin da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da shugabannin kasashen duniya suka yi game da rahoton na da karfi.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce Isra'ila tana da wajibci a karkashin dokokin kasa da kasa - har da aikin tabbatar da abinci da magunguna ga jama'a.

Ba za mu bari wannan lamari ya ci gaba ba babu daukar mataki."

Shugaban hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher ya ce yunwar ta samo asali ne daga toshe hanyoyin jin kai da Isra'ila ta yi.

Shi kuma, Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya ce: "Kin amincewar gwamnatin Isra'ila ta ba da damar shigar da isassun kayan jin kai zuwa Gaza ya janyo kirkirarren bala'i."

A ranarJuma'a ne, Babban jami'in jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya ce "laifin yaki ne yin amfani da yunwa a matsayin wata hanya ta yaki kuma mace-macen da ake samu sakamakon haka na iya zama laifukan yaki na kisa da gangan.

Mamaye birnin Gaza

A wannan makon ne Isra'ila ta ba da izinin kiran dubban sojoji domin shirinta na mamaye birnin Gaza, yankin da IPC ta ayyana cewa akwai matsalar yunwa.

Netanyahu ya ce kwace birnin baki daya shi ne zafin da ya fi dacewa na murkushe Hamas da kawo karshen yakin da kuma sakin Isra'ilawan da ke tsare a Gaza.

Mamayar za ta daidaita Falasdinawa da aka kiyasta za su kai miliyan guda da ke zaune a birnin Gaza da yankunan da ke kawaye da birnin.

Tuni Isra'ila ta fada wa likitoci da kungiyoyin agaji da su shirya domin su tsara hanyoyin ficewa daga yankin.

Wata sanarwar hadin gwiwa daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya har da Unicef da WFP da WHO ta bayyana damuwa game da shirin na Isra'ilar inda suka ce "hakan zai kara ta'azzara halin da farar hula ke ciki musamman na yunwa.

"Mutane da dama - musamman marasa lafiya da yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki, da tsofaffi da mutane masu bukata ta musamman - ba lalle su iya ficewa ba."