'Peter Obi na da farin jini amma ba shi da ƙwarewar ceto Najeriya'

Okowa

Gwamnan Jihar Delta a Najeriya, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a jami’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, ya bayyana ra’ayinsa a kan ɗan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi wanda ya bar PDP.

Okowa ya amince cewa Obi yana da farin jini, amma kuma ya ce ba shi da ƙwarewar ceto Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da BBC Pidigin.

Ya ce “Ni ban ce ba zai samu ƙuri’a ba, zai samu ƙuri’a.”

"Na ga abun da ya faru a baya, yanayin yanzu ba irin wancan ba ne, zai yi wahala, saboda irin abun da ya faru da shi a baya, akwai irin ƙwarewar da kake samu, bai yi zurfi sosai ba," a cewar Okowa.

A cikin hirar, gwamnan na Delta ya kuma ce suna tattaunawa domin ɗinke ɓarakar da ke jam’iyyarsu ta PDP.

Kalaman nasa sun zo ne bayan martanin da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya yi kan batutuwan da Atiku Abubakar ya faɗa a cikin wata hira da ya yi a baya-bayan nan kan zaɓen abokin takararsa na 2023.

Wike ya ce Atiku ya fadi karya da yawa kuma zai fito ya fadi gaskiya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai Sanata Okowa ya gaya wa sashen Pidgin na BBC a wata tattaunawa ta musamman cewa ya samu hanyar da zai bi don tattaunawa da Wike kuma za a warware komai.

“Muna tattaunawa a bayan fage, kuma ana wareware komai a hankali, ka san cewa idan wani abu ya faru kuma aka samu rashin daidaituwa, dole sai an bi a hankali domin kamo bakin zaren.

"To shi ne abun da muke ta yi a bayan fage. Muna samun hanyoyin magana. Abokina ne, kuma ni ma abokinsa ne, muna lalubo bakin zaren.

”Atiku ya fadi nasa ɓangaren dangane da abun da ya faru, kuma na tabbata abun da ya fada gaskiya ne, kuma ban ce Wike ƙarya yake ba. Amma idan mutum ya yi fushi, yana da kyau ya faɗi abun da ke ransa.

"Amma muhimmin abu a gare mu da jam’iyyarmu shi ne yadda za mu hada kan kowa, yadda za mu yi aiki tare, shi ne abun da ke gabanmu.

"Wike yana da muhimmanci ga jam’iyyarmu, kuma ya yi aiki tuƙuru don ci gaban jam’iyyar kamar yadda da yawa daga cikinmu muka yi.

"Saboda haka muna fata komai zai daidaita kuma muna magana a hankali-hankali. Na tabbatar nan ba da jimawa ba za mu zauna.” a cewarsa.

Abin da ya sa na tsaya mataimakin Atiku a takarar

Dan takarar mataimakin shugaban kasar na PDP ya kuma bayyana dalilin da ya sa ya amince zama mataimakin Atiku.

"Ni na san mutumin yana da ƙwarewar da ake buƙata domin tafiyar da gwamnati a halin yanzu.

"Najeriyar da muke da ita yanzu, ba kowa ne yake cewa yana son zama shugaban ƙasa ba, akwai waɗanda suna son zama shugaba saboda kawai suna son zama shugaba, akwai waɗanda suna so ne domin su yaudari jama’a.

"Yanzu ba ta jam’iyya ake yi ba, amma ta mutanen da za su iya wannan aikin ne tun daga daren farko, waɗanda za su iya riƙe yanayin.

"Ana son wanda za a iya girmamawa kuma zai iya zama da mutane, ya kawo tsare-tsare masu kyau, wanda zai iya yi wa mutane magana su gane kuma su yi amanna. Kuma shi kaɗai ne yake da ƙwarewar da ke da muhimmanci ga kujerar.” a cewarsa.

Dangane da ko wace irin rawa suke ganin za su taka a zaɓen 2023, ya bayyana cewa suna neman goyon bayan matasa akan kar su yanke shawara mara kyau.

“Mu dai namu shi ne mu cigaba da ganawa da matasa, domin su fara ɗaukar saƙonninmu suna yaɗawa, na cewa a wannan lokacin na takaici, kar su yanke shawarar da ba ta dace ba.

"Abun da muke gaya musu kenan. Ba a kan APC ba ne, ko PDP, ko jam’iyyar Labour, ko NNPP da sauran jami’iyyu, wannan zaben ya dogara ne a kan batutuwan da suka shafi ƙasa."

Sanata Ifeanyi Okowa ya kuma bayyana nasa ra’ayin a kan ɗan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi wanda ya bar PDP, Okowa ya amince cewa yana da farin jini, amma kuma ya ce ba shi da ƙwarewar ceto Najeriya.

“Ni ban ce ba zai samu ƙuri’a ba, zai samu ƙuri’a.”

"Na ga abun da ya faru a baya, yanayin yanzu ba irin wancan ba ne, zai yi wahala, saboda irin abun da ya faru da shi a baya, akwai irin ƙwarewar da kake samu, bai yi zurfi sosai ba.

"Ko ni da aka ɗauka daga kujerar gwamna, maganar da nake yi, na fuskanci lokuta masu cike da ƙalubale kuma na san irin wahalar da ake sha, kuma ina so na koyi abubuwa daga wajen Atiku, saboda yana da ƙwarewa daga gwamnatin tarayya saboda haka zai iya fuskantar duk wani ƙalubale.

Duk da rigingimun da suka sa INEC ƙin saka sunan ɗan takarar PDPn a jerin sunayen ‘yan takara na jihar Delta, tsohon Sanatan yana da ƙarfin gwiwar cewa za a wareware matsalar.

"Babu matsala, yanayin gudanarwar jam’iyya ne, kuma komai zai tafi akan tsarin jam’iyya, mun yi takarar cikin gida kuma an kai lamarin kotu, saboda haka idan abu na kotu, za a bar kujerar babu kowa sai an kammala shari’a.

"Saboda haka kar a yi fargaba, PDP za ta samu ɗan takara a wannan zaɓen," a cewar Okowa.