Yaƙi ba mafita ba ne ga Nijar a rikicinta da su Ecowas - Masana

Asalin hoton, Forces Armees Nigeriennes
Wasu masana fannin tsaro a Jamhuriyar Nijar na ganin har yanzu dangantaka ba ta yi munin da za a kasa zama teburin sasantawa ba, tsakanin hukumomin mulkin sojin ƙasar da maƙwabtanta Benin da Najeriya, har ma da Faransa.
"Ba daidai ba ne, duk maganar da ake yi a riƙa ɗauka kawai harka ce ta yaƙi."
"Ba ta ɓaci ba, gwamnatin ga na Nijar ɗin, har yau dai da na Faransa ɗin, da duka Ecowas ɗin, a sake tattamnawa," wani masanin tsaro a Nijar ya ce.
Moustapha Abdoulaye na wannan bayani ne bayan sojoji masu mulki a Nijar sun sanar da warware yarjejeniyar soji da ke tsakaninsu da ƙasar Benin.
Suna zargin maƙwabciyar tasu ta Kudu maso Yamma ne da bai wa Ecowas wuri domin jibge sojojin da suka ce na shirin mamaye ƙasar tasu.
Yunƙurin tattaunawa tsakanin shugabannin mulkin sojan Nijar da Ecowas, ya ci tura, bayan kowanne ɓangare ya kafe a kan matsayinsa game da juyin mulkin da sojojin suka yi ranar 26 ga watan Yuli.
Tun farko, Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar jerin takunkumai, sannan ta yi barazanar amfani da ƙarfin soji matuƙar masu juyin mulkin Nijar suka ƙi mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan karagar mulki bayan hamɓaras da shi.
Nijar ta yi watsi da wa'adin kwana bakwai da ƙungiyar raya ƙasashen Afirka ta Yamma ta ba ta. Sannan ta tura dakaru kan iyakokinta da ƙasashen Benin da Najeriya. Yayin da ƙasashen Mali da Burkina Faso suka lashi takobin shigar mata faɗa.
Shugabannin mulkin sojan dai sun ce: "sun yanke shawarar katse alaƙar ayyukan soji tsakaninsu da Benin".
Benin "ta ba da wuri don girke sojoji, da sojojin haya da kuma kayan aiki" a wani yanayi da zai iya kai wa ga mamayen sojojin Ecowas, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin Nijar ya karanta a gidan talbijin ɗin ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Har yanzu Benin ba ta ce uffan ba game da wannan batu. Ecowas ma ba ta yi ƙarin bayani a kan zargin mamayen da Nijar ta yi ba, duk da yake a makon jiya ƙungiyar ta ce tana ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Nijar.
Nijar da Jamhuriyar Benin na ayyukan soji na haɗin gwiwa a yankin Sahel don kakkaɓe mayaƙa masu iƙirarin jihadi.
Kanal Manjo Amadou Abdramane a cikin sanarwar da ya karanta da maryacen Talata, ya yi tur da goyon bayan da Benin ke bayarwa ga wani shiri na yiwuwar amfani da ƙarfin soja daga Ecowas, inda ya ce matakin ya saɓa da alaƙar dogon tarihi da ke tsakanin ƙasashen biyu.
"Majalisar Ceton Al'umma ta Ƙasa da gwamnatin Nijar sun yi la'akari da tsohuwar alaƙar da ta haɗa al'ummar Nijar da 'yan'uwansu na Benin, waɗanda ke da al'umma ɗaya da muradai iri ɗaya.
Irin wannan alaƙa da ta zama al'ada, su ne ƙashin bayan sanya hannu kan wata yarjejeniyar haɗin gwiwa ta ayyukan soja tsakanin ƙasashen guda biyu."
"Sai dai, ƙasar, wadda ke cikin ƙalubalen tsaro da na siyasa da tattalin arziƙi, ta yanke shawarar bin matakin takalar faɗa a kan Nijar maimakon goyo mata baya," in Kanal Abdramane.
"Jamhuriyar Benin ta ba da umarnin jibge dakarun sojoji da sojojin haya da kayan yaƙi da nufin auka wa ƙasarmu daga Faransa da haɗin gwiwar wasu ƙasashen Ecowas."
'Zaman doya da man ja ba alheri ba ne'
Mustapha Abdoulaye ya ce buƙatar tattaunawa da ƙasashe ta wajaba ne saboda rufe harkokin da Ecowas da kuma Faransa suka yi wa Nijar.
Wannan zaman doya da man ja tsakaninmu da Benin, in ji Mustapha Abdoulaye, ba alheri ba ne. "A can Benin, akwai 'yan Nijar masu yawa, haka zalika, a nan Nijar, akwai 'yan Benin da yawa.
A cewarsa, ko yanzu duka ɓangarorin sun ji jiki, tun bayan fara wannan turka-turka tsakanin ƙasashe na Afirka ta Yamma.
Masanin ya ce muradan Nijar na tattalin arziƙi na da ɗumbin yawa a Benin.
"Batutun man fetur na Nijar yana bi ta Benin. Gaskiya, ya kamata mu samu daidaito."











