Mece ce makomar tsaron Nijar idan dakarun Faransa suka fice?

Asalin hoton, Reuters
Shugabannin mulkin soja a Nijar sun ce za su fara tattaunawa don ganin janyewar dakarun Faransa cikin sauri daga ƙasar.
Firaminista Ali Mahamane Lamine Zeine wanda sojoji suka naɗa ya kuma ce akwai fatan za su cimma yarjejeniya da ƙungiyar raya ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas).
Masu zanga-zangar nuna goyon bayan juyin mulki sun nemi buƙatar sojojin Faransa su fice daga ƙasar ta Nijar bayan da Faransa ta ki amincewa da gwamnatin mulkin sojin ƙasar.
Ba a dai san wane ne ke jagorantar tattaunawar da Faransa ba. Firaminista Ali Zeine ya tabbatar wa manema labarai cewa dole ne jakadan Faransa ya bar ƙasar.
Ya dage cewa ci gaba da kasancewar Faransa a ƙasar "haramtacce ne" bayan da sojojin suka kawo karshen dangantaka a ɓangaren tsaro da Faransa.
Faransa wadda ta yi wa Nijar ɗin mulkin mallaka, ta ce Shugaba Mohamed Bazoum kaɗai ta sani a matsayin halastaccen shugaban ƙasar, ba sojojin ba.
Jagororin mulkin sojin na cikin matsin lamba daga ƙungiyar Ecowas tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum.
Sojojin sun sanar da cewa za su riƙe madafun iko har na tsawon shekara uku kafin su mayar da mulki hannun farar hula, abin da Ecowas ta yi fatali da shi.
Ƙungiyar ta yi barazanar ɗaukar matakin soji domin dawo da Shugaba Bazoum kan mulki muddin tattaunawar diflomasiyya ta gaza.
Sai dai rahotanni na cewa China na nuna yunkurin shiga tsakani domin ganin an samu hanyar warware rikicin.
"Nijar za ta iya kare kanta ko babu sojojin Faransa"
Masana da dama dai na mayar da martani kan wannan dambarwa.
Wani mai bincike a wata cibiya mai suna International Center of Study and Reflection on Sahel da ke Faransa, Dakta Sadiq Abba ya ce ko da a ce Faransa ta janye sojojinta daga Nijar, ƙasar tana da karfin da za ta kare kanta.
Ya ce batun janyewar sojojin Faransa daga Nijar lamari ne mai daɗi ga ƙasar, inda ya ce da tun da farko tattaunawa aka yi maimakon shiga takun-tsaka.
Sa dai ya ce za a ɗauki tsawon lokaci kafin dakarun na Faransa su fice daga Nijar saboda a cewarsa akwai kaya da dama da za su ɗauka kafin su fice.
Ya ce dukkan kayan aikinsu an dawo da su Nijar bayan ficewarsu daga Mali.
Dakta Sadiq ya ce ko da lokacin da sojojin Faransa suka fice daga Mali, sun ɗauki tsawon watanni shida.
Ya ce kafin dakarun Faransa su fice, sai an zauna an tsara yadda ficewar tasu za ta kasance tsakanin ɓangarorin biyu don ganin ba a samu tarnaki ba ko kuma shiga gaba da juna.
Yaya makomar tsaron Nijar zai kasance idan sojojin Faransa suka fice?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dakta Sadiq Abba ya ci gaba da cewa ficewar sojojin na Faransa ba zai kawo wani tashin hankali ga Nijar ba, saboda sojojin ƙasar sun koyi yadda ake yin yaƙin tawaye.
"Yanzu Nijar za ta haɗa-kai da ƙasashen Mali da Burkina Faso wanda za su taimaka wa ƙasar ko da sojojjin Faransa sun bar ƙasar. Ba bu wsani tasiri da hakan zai yi," in ji Masanin.
Ya ce Nijar tana da yawan makaman yaƙi waɗanda za su taimaka mata wajen kare kanta ko da dakarun Faransa sun tafi.
Masanin ya ce tun lokacin Shugaba Bazoum ƙasar ta sayo jirage marasa matuka inda ake jiran isowar su.
Ya ce kayan za su taimaka wa ƙasar matuka wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar-baya da suka addabe su.
Sannan ya ƙara da cewa ko Faransa ta tafi, Nijar za ta iya sayen makamai daga wata ƙasa, don haka za ta iya kare kanta yadda ya kamata.
Dakta Abba ya ce da wuya ficewar Faransa ya sanya wasu ƙasashe su ma su bar ƙasar, saboda kowa da manufarsa da kuma abin da yake so.
Mai binciken ya ce idan ana so a samu mafita kan yaƙi da ta'addanci a yankin Sahel, sai an magance matsalar talauci da rashin gaskiya da kuma samun kyakkaywar shugabanci.










