Tasirin yarjejeniyar tsaro da Nijar ta soke da Faransa

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin da ke mulkin Nijar sun soke yarjejeniyar ayyukan tsaro da Faransa ranar Alhamis, a wani mataki da zai shafi yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Kamar a maƙwabtanta Burkina Faso da Mali, kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka yi ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani ya zo ne daidai lokacin da ake ƙara tsanar Faransa a yankin.
Faransa wadda ta yi wa ƙasashen uku mulkin mallaka, na da sojoji 1,000 zuwa 1,500 a Nijar, a cewar kamfanin labarai na Reuters, waɗanda suke yaƙi da ƙungiyoyi masu alaƙa da al-Qaeda da kuma ISIS a yankin Sahel.
Sai dai Faransa ta sa ƙafa ta shure matakin yin watsi da yarjejeniyoyin ayyukan sojoji na haɗin gwiwa da shugabannin juyin mulkin suka ɗauka.
Ta ce masu juyin mulkin ba su da damar yin haka.
Matakin na zuwa ne bayan sojoji masu juyin mulkin sun ba da sanarwar soke yarjejeniyoyin tsaro da na diflomasiyya da ƙasashen Faransa da Togo da Najeriya da kuma Amurka.
Kakakin majalisar sojojin, Amadou Abdramane, shi ne ya bayyana matakin kai-tsaye a talbijin. An ƙulla yarjejeniyoyin a shekarun 1977 da 2020, a cewar Reuters.
Janar Abdramane ya ƙara da cewa za a aika wa Faransa sanarwar a hukumance.
Ƙawayen Nijar na Afirka da Yammacin duniya, ciki har da Faransa, sun ƙaƙaba mata takunkumai da zummar matsa wa sojoji su mayar da ƙasar kan turbar tsarin mulki.
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa dai ta ce "tsarin shari'a da aka shimfiɗa yarjejeniyoyin tsaron tsakanin Faransa da Nijar, an yi shi ne a kan yardar juna, kuma halartattun hukumomin Nijar suka sanya wa hannu".
Juyin mulkin na Nijar, shi ne karo bakwai da aka yi a Afirka ta Yamma da Tsakiya tun daga 2020, inda ya shafi ƙasashen Mali, da Burkina Faso, da Guinea.
Sai dai, shugaban gwamnati Janar Abdourahamane Tciani ya ce ba za su ja da baya ba, har ma suka nemi taimakon Rasha.
Haka nan, Tchiani ya samu goyon bayan sojojin Mali da Burkina Faso, waɗanda dukkansu suka bayyana matsalar tsaro a matsayin dalilin da ya suka yi juyin mulkin.
Tasirin da Nijar za ta iya fuskanta
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
La'akari da arziƙin ma'adanin yuraniyam da man fetur, da muhimmancinta a yaƙi da Ƙasashen Yamma kamar Amurka da Faransa da Tarayyar Turai ke yi da 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi.
Ƙasashen Yamma masu ba da gudunmawa sun katse tallafin da suke bai wa Nijar don nuna adawa da juyin mulkin sojoji. Nijar, na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya kuma ta dogara a kan agaji daga ƙasashen Turai da Amurka wajen samun kashi 40% na kasafin kuɗinta.
A ƙarƙashin yarjejeniyoyin haɗin gwiwar tsaro, sojojin Faransa kimanin 1,000-1,500 na amfani da jiragen yaƙi da sauran jirage marasa matuƙa, don taimaka wa yaƙi da ƙungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya masu alaƙa da al Qaeda da kuma IS a yankin Sahel.
Nijar na fama da gagarumin ƙalubalen tsaro a kan iyakar ƙasashe guda uku, wadda ta haɗar da Burkina Faso da Mali, masu iƙirarin jihadi a ƙasashen suna iko da maka-makan yankuna, kuma har sukan tsallako iyaka su kai hari ciki Nijar.
A farkon watan Fabrairun bana, mayaƙa sun kai hari a arewacin yankin Banibangou na jihar Tillabery kusa da kan iyaka da ali, inda suka kashe sojojin Nijar aƙalla goma, mutum 16 suka ɓace, yayin da aka jikkata sojoji guda 13.
Daga ɓangaren, kudu masu gabashin ƙasar kuma, Nijar na fama da rikicin Boko Haram, wadda mayaƙanta akasari ke tsallaka iyaka daga Najeriya, suna kai hare-hare.
Hare-haren ƙungiyar sun yi sanadin tilasta wa dubun dubatar mutane zuwa gudun hijira da ɗaiɗaita garuruwa da ƙauyuka tare da kashe ɗumbin 'yan ƙasar.
Taimakon horas da sojoji da kayan ayyukan yaƙi sun yi gagarumin tallafa wa Nijar wajen durƙusar da harkokin ƙungiyar musamman a yankin jihar Diffa.
Babban hafsan rundunar sojin Nijar a cikin watan Janairun bana ya bayyana cewa ayyukan haɗin gwiwa da Ƙasashe Yamma sun taimaka wa ƙasar wajen yaƙin da take yi.
Masu juyin mulki sun ba da misali da taɓarɓarewar tsaro a matsayin babbar hujjarsu ta ƙwace mulki, sai dai alƙaluman hare-haren da ake kai wa sun nuna cewa haƙiƙanin gaskiya tsaro ya inganta a Nijar.
Shi kansa hamɓararren shugaban ƙasar na Nijar, Mohamed Bazoum ya faɗa a jawabinsa na farko tun bayan juyin mulki cewa "matuƙar ƙasashen duniya suka bari juyin mulkin ya yi nasara, hakan zai kasance mai matuƙar illa ga ƙasarmu, da yankinmu da kuma ɗaukacin duniya," kamar yadda ya rubuta a jaridar Washington Post.
Wakilan Ecowas ba su ga Janar Tchiani ba

Asalin hoton, State House
A ranar Alhamis tawagar wakilci da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura a madadin Ecowas ta isa Yamai don shawo kan sojojin mulkin ƙarƙashin Janar Abourahamane Tciani.
Sai dai wata majiya ta faɗa wa Reuters cewa an kammala tattaunawar a filin jirgin sama tun a daren Alhamis ba tare da cimma wata matsaya ba.
A cewar majiyar, tawagar ta fice daga Nijar a daren ba tare da ganin Janar Tchiani ba,
Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar ne ya jagoranci tawagar mai mutum 15, inda shi kuma shugaban ya tura tawagar mutum biyar a madadinsa bisa jagorancin Janar Bamou.
Ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma ta yi barazanar amfani da ƙarfin soja idan ba a mayar da Bazoum kan mulki ba.
A ranar Juma'a hafsoshin tsaro na mambobin ƙungiyar za su kammala taron kwana uku da suke yi a Abuja, babban birnin Najeriya.
Ana garkuwa da ni - Bazoum

Asalin hoton, @GmahamatIdi

Asalin hoton, PA Media
A gefe guda kuma, hamɓararren Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya roƙi Amurka da "duka ƙasashen duniya" da su taimaka "wajen mayar da ƙasar kan tsarin mulki" bayan juyin mulkin na makon jiya.
Cikin wata maƙala da ya rubuta a jaridar Washington Post ranar Alhamis, Shugaba Mohamed Bazoum, ya ce yana rubutun ne a matsayin "mutumin da aka yi garkuwa da shi".
Rashin kwanciyar hankali na ƙara ta’azzara a ƙasar da ke yammacin Afrika tun bayan hamɓarar da shugaban.
A ranar Alhamis, shugaban da ya jagoranci juyin mulkin ya sanar da kiran jakadunsu gida daga ƙasashen Faransa, da Amurka, da Najeriya, da kuma Togo.










