Wadansu ƴanbindiga na neman sulhu - Ribadu

NSA NIGERIA

Asalin hoton, OTHER

An wallafa

Mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya ce akwai wadanda daga cikin ƴanbindigar da suka samu fahimtar juna da su: "Nasani wannan abin idan Allah zai kawo mana sauki sai mun samu fahimtar juna, domin wadanda suke yin wannan abun ƴan uwanmu ne masifa ce ta zo mana".

Nuhu Ribadu ya ce suna ƙoƙarin samun fahimta tsakaninsu da wasu ƴanbindigar.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana aiki, koda yake basa fitowa fili su bayyana matakan da suke dauka saboda yanayin aikin tsaro ba a magana.

Nuhu Ribadu ya ce akwai canje-canje da aka samu da dama musamman wajen adadin mutanen da ake kashewa a Najeriya kowane wata, inda lokacin da suka hau mulki ana kashe dubban mutane, "yanzu idan mutum ya je Neja Delta ya san an yi aiki, haka ƙasar Inyamurai, ofishin ƴansanda kusan 50 duk an tada su a baya amman yanzu duk sun koma suna aiki, kuma mun kawo ƙarshen zaman gida na dole da a baya ake yi a yankin, haka a yankin Arewa maso gabas an rage yawan kashe-kashe sosai".

Mai ba shugaban Najeriyar shawara kan tsaro ya ce sun yi nasarar kashe wasu da dama daga cikin shugabannin ƴanbindiga da suka da Ali Kachallah wanda ya jagoranci harin jami'ar Gusau ta jihar Zamfara da aka sace dalibai da kuma Boderu da Damina da Dangote da sauransu.

Nuhu Ribadu ya ce an samu taaro a ƙasar idan aka yi la'akari da yadda yanzu mutane ke zuwa duk inda suke so ba tare da fargaba ba.

Najeriya dai na fuskantar matsalar tsaro a kowane ɓangare na ƙasar, lamarin da hukumomi ke cewa sun kusa kawar da shi.

'Matsalar tana karuwa a wadansu yankuna'

Bayanai sun ce jama'ar garuruwa kimanin dari da hamsin na yankunan kananan hukumomin Malumfashi da Kankara na jihar Katsina, sun tsere zuwa wasu wurare.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Jama'ar da abin ya shafa sun koka da cewa, 'yan bindigan suna cin karensu ba babbaka, saboda rashin kwararan matakan tsaro.

Matsalar hare-haren 'yanbindiga da ta zama wani karfen kafa a yankin arewa maso yammacin Najeriya tana ci gaba da jefa jama’a a cikin tsaka mai wuya a garuruwa da dama na karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC.

A yankin karamar hukumar Kankara ma, matsalar ta 'yan bindiga ta dawo sabuwa a wasu wuraren, har ta fasa garuruwa fiye da dari a kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC.

‘’Kana zaune gidanka a zo a kore ka, a harbe ka, dole kana ji kana gani ka bar yayanka, ka bar matanka ka ruga da gudu, in kuma ba ka samu sa’a ba a zo a banke ka da mashin'' in ji wani ganau.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar 'yansandan Najeriya da kwamishinan tsaro na jihar game da wannan al'amari amma kuma hakar ba ta cimma ruwa ba saboda mun kasa samunsu ta waya har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto.