Abin da BBC ta gano kan yarjejeniyar nukiliya tsakanin Saudiyya da Amurka

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

BBC Persian ta samu kwafin yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amurka da Saudiyya da aka sanya wa hannu a watan Yuli, kuma yarjejeniyar ba ta ƙunshi wani sharadi da ke tilasta wa Saudiyya ta amince da Isra'ila domin samun shirinta na nukiliya ba.

Kundin yarjejeniyar ya bai wa Riyadh damar fara hanyoyin tace sinadarin uranium zuwa kusan kashi 20 bisa wasu sharuɗɗa da matakai daban-daban.

Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa, aƙalla a cikin kundin wannan yarjejeniya, babu wata magana game da Yarjejeniyar Abraham Accords da ke neman ƙasashen Larabawa su amince da isra'ila a matsayin ƙasa, kuma ba a ɗora wa Saudiyya wani nauyin amincewa da Isra'ila ba. Saboda haka, abin da ke cikin wannan kundi bai yi daidai da kalaman Shugaban Amurka Donald Trump ba.

Bayan kulla yarjejeniyar, Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa amincewa da yarjejeniyar nukiliyar farar hula tsakanin Amurka da Saudiyya zai dogara ne kan Saudiyya ta shiga Yarjejeniyar Ibrahim.

"Za a amince da yarjejeniyar nukiliyar zaman lafiya tsakanin Ma'aikatar Makamashi ta Amurka da Saudiyya," in Trump.

Ya kuma bayyana cewa yarjejeniyar ba ta ba da damar samar da wani abu da za a iya amfani da shi wajen ƙera makamai ba, domin an takaita ta ne kawai ga amfanin farar hula da ba na soja ba.

Ya ambaci shirye-shiryen nukiliyar zaman lafiya na Iran, Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu ƙasashe a matsayin misalai, yana mai cewa Amurka ba ta adawa da amfani da cibiyoyin nukiliya domin ayyukan farar hula.

Wadanne ƙarin abubuwa ne yarjejeniyar ta ƙunsa?

..

Asalin hoton, Getty Images

Bisa tanadin sashi na 7 na yarjejeniyar, uranium da za a samar ko kuma a tura ƙarƙashin wannan yarjejeniya na iya shiga matakin tacewa idan ɓangarorin biyu sun amince a rubuce. Domin cimma hakan, bangarorin biyu za su gudanar da tantancewa tare kan yiwuwa da kuma amfani da tace sindarin uranium.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bisa sakin layi na biyar na wannan mataki, idan aka yi amfani da kayan aiki da fasahar Amurka wajen tace uranium, adadin tacewar zai tsaya ne a kashi 5.

Sai dai idan ɓangarorin biyu sun amince, Saudiyya za ta iya ƙara matakin tacewar sinadarin uranium zuwa kashi 20.

Masu adawa da shirin Iran na tace uranium sama da kashi 5 sun daɗe suna jayayya cewa kaiwa matakin kashi 20 na nufin an kammala kusan kashi 90 na hanyar samun fasahar ƙera bam ɗin nukiliya, domin sauran matakan da suka rage ana iya kammala su cikin sauri sosai.

A wani ɓangaren kuma, duk da cewa yarjejeniyar ta wajabta wa Saudiyya amincewa da bincike da sa ido da aka tanada a cikinta, ba ta wajabta mata shiga Ƙarin Yarjejeniyar IAEA ba.

Kazalika, samar da duk wata na'ura, kayan aiki ko wasu sassan da suka shafi wannan shiri, ko da kuwa za a yi amfani da su ne don ayyukan da ba su da alaƙa da abubuwan da ake ɗauka masu haɗari, zai kasance ƙarƙashin aiwatar da wata yarjejeniyar tsaro ta bai ɗaya tsakanin Amurka da Saudiyya, wadda za ta bai wa Amurka damar sa ido da kulawa kan yadda ake amfani da waɗannan kayayyaki.

Ko shugaba Trump ya yi sassauci ga Saudiyya ne?

..

Asalin hoton, Getty Images

Masu sharhi da ƙwararrun da ke aiki domin hana yaɗuwar makaman nukiliya sun fi nuna damuwa ne kan wannan batu.

Yarjejeniyar bincike da sa ido tsakanin Amurka da Saudiyya ta takaita ne ga "wuraren da yarjejeniyar ta shafa" kawai, wato wuraren da ke da alaƙa kai tsaye da wannan yarjejeniya.

Wannan na nufin cibiyoyin da ke amfani da fasahar Amurka ko kuma kayan nukiliyar da suka fito daga Amurka.

Amma shiga Ƙarin Yarjejeniyar IAEA zai ba masu bincike damar sa ido kan dukkan shirye-shiryen nukiliyar ƙasa baki ɗaya, har da wuraren da ka iya kasancewa a ɓoye ko kuma waɗanda ba su da alaƙa da haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasar da Amurka.

Idan aka kwatanta yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da sabuwar yarjejeniyar da Saudiyya, a bayyane yake cewa Shugaba Trump ya yi wa Saudiyya gagarumin sassauci.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta amince cewa ba za ta taɓa gudanar da aikin tace uranium ko sake sarrafa shi a cikin ƙasarta ba, ko da kuwa fasahar Amurka ce ko kuma wata fasaha daban.

Haka kuma, shiga Ƙarin Yarjejeniyar IAEA ya kasance wani sharadi kafin Amurka ta ba da lasisin fitar da duk wani kayan aikin nukiliya zuwa UAE.

Bugu da ƙari, duk wani yunƙuri da UAE za ta yi na fara tace uranium, ko da kuwa ba ta karya wata yarjejeniya ba, za a ɗauke shi a matsayin cikakkiyar karya yarjejeniyar haɗin gwiwar da ke tsakaninta da Amurka.

Saudiyya kuwa ba ta amince da ɗaya daga cikin waɗannan sharuɗɗa ba.

A wasiƙar da Fadar White House ta aika wa Majalisar Dokokin Amurka, an ambaci wasu ƙarin takardu biyu masu sirri, amma har yanzu ba a bayyana abin da suka ƙunsa ba.

Idan ma waɗannan takardun suna ɗauke da wasu tanade-tanade game da waɗannan batutuwa, to muddin Saudiyya ba ta amince da su ba kuma ba ta sanya musu hannu ba, ba za su iya yin tasiri kai tsaye kan irin wannan haɗin gwiwar nukiliya ba.

Me Isra'ila ta ce game da yarjejeniyar nukiliya tsakanin Amurka da Saudiyya?

..

Asalin hoton, Getty Images

Ofishin Firaministan Isra'ila ya sake jaddada kalaman Trump cewa yarjejeniyar za ta kasance "wani babban mataki na tarihi wajen samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya."

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X, ofishin Netanyahu ya ce yaƙin da Amurka da Isra'ila suka yi da Iran ya "haifar da wata dama ta faɗaɗa da'irarar zaman lafiya."

A halin da ake ciki, masana harkokin nukiliya da wasu tsoffin jami'ai a Isra'ila, wadda ita ce muhimmiyar ƙawar Amurka a Gabas ta Tsakiya, sun nuna damuwa cewa wannan shiri na iya bai wa Saudiyya damar haɓaka shirinta har ya kai ga ƙera makaman nukiliya.

Ministan Tattalin Arzikin Isra'ila, Nir Barkat, ya ce idan Saudiyya za ta yi amfani da makamashin nukiliya ne kawai domin samar da makamashi, to Isra'ila ba ta da wata matsala da hakan.

Da yake magana da gidan rediyon sojojin Isra'ila, ya ce:

"Idan suna son yin amfani da shi ne don manufar lumana, za mu iya yin aiki tare da su. Amurka ba ta son ɗaukar wani mataki da zai jefa Isra'ila cikin haɗari."

Nir Barkat ya ƙara da cewa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka Donald Trump bai kamata su ci gaba da irin waɗannan matakai ba tare da sun fara fahimtar haɗurran da ke tattare da su ba.

Sai dai tsohon Ministan Tsaro da Harkokin Wajen Isra'ila, Avigdor Lieberman, na da ra'ayi dabam, inda yake ganin ya kamata Isra'ila ta yi adawa da wannan yarjejeniya.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Lieberman ya rubuta cewa:

"Shirin nukiliyar farar hula na Saudiyya na iya zama hanyar da za ta kai ga ƙera makaman nukiliya nan gaba."