Chiesa zai iya barin Liverpool, AC Milan za ta taya Endrick

Asalin hoton, Getty Images
Federico Chiesa na fuskantar rashin tabbas a Liverpool, Jadon Sancho ka iya komawa gasar Premier, sannan farin jinin Endrick na Real Madrid na ƙaruwa tsakanin kungiyoyi daga kasar Italiya.
Ɗan wasan gaba na Liverpool Federico Chiesa mai shekara 26, zai nemi barin ƙungiyar a watan Janairu idan har ya fuskanci matsalar samun isasshen lokacin buga wasa bayan ya dawo daga jinya. (Football Insider)
Tsohon ɗan wasan Manchester United Jadon Sancho na tattaunawa da aƙalla ƙungiyoyin Premier biyu game da yiwuwar komawarsa can. (Teamtalk)
AC Milan tana shirin aro dan wasan gaba na Brazil Endrick mai shekara, daga Real Madrid a watan Janairu. (Calciomercato)
Manchester United na ci gaba da zawarcin ɗan wasan tsakiya na Leicester City Louis Page mai shekara 18, bayan da ta kasa ɗaukarsa a ranar ƙarshe ta rufe kasuwar musayar ƴan wasa ta baya-bayan nan. (ESPN)
Manchester City ta sanya ido kan ɗan wasan Atletico Madrid Alex Baena, amma da ƙyar idan za ta yi yunkurin daukar ɗan wasan mai shekaru 25 a watan Janairu. (Football Insider)
Liverpool da Manchester United sun tuntuɓi kungiyar Wolves kai-tsaye game da yiwuwar ɗaukar Matheus Mane. (Ekrem Konur)
Brentford ta buɗe tattaunawa kan sabuwar kwangila da ɗan wasan gaba na kasar Jamus Kevin Schade mai shekara 24 domin ta daƙile sha'awar da Arsenal ke da ita a kansa. (Teamtalk)
Manchester United ta kammala yarjejeniyar siyan ɗan wasan tsakiya na Liverpool Isaac Konde mai shekara 16. (Fabrizio Romano)











