KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Talata 08/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir

Rahoto kai-tsaye

Daga Muslim Muhammad Yusuf

  1. INEC ta sanya ranar zaɓukan cike gurbi a Kano, Gombe, Bauchi da Delta

    INEC

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC, ta sanya ranar 19 ga watan Satumba domin gudanar da zaɓukan cike gurbi guda biyar a jihohin Gombe, Kano, Bauchi da Delta.

    Sakataren yaɗa labarai na shugaban INEC, Tunde Oketola, ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, cewa zaɓukan sun ƙunshina kujerar majalisar wakilai ta tarayya guda ɗaya da kuma kujerun majalisun jihohi huɗu.

    Ya ce za a gudanar da zaɓen kujerar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Gombe/Kwami/Funakaye ta jihar Gombe.

    Zaɓukan kujerun majalisar jihohin kuma za su gudana a mazabar Disina da Sakwa a jihar Bauchi, sannan Udu a jihar Delta da Dawakin Kudu a jihar Kano.

  2. Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Jamus kan nasarar jam’iyyar masu ra’ayin riƙau

    Saxony-Anhalt protest

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a ƙofar Brandenburg da ke birnin Berlin, domin nuna adawa da nasarar da jam’iyyar AfD mai ra’ayin riƙau ta samu a zaɓen jihar Saxony-Anhalt.

    Masu zanga-zangar sun yi kira da a haramta jam’iyyar, wadda hukumomin leƙen asirin Jamus suka ayyana a matsayin mai tsattsauran ra'ayi.

    Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce ya firgita da sakamakon zaɓen, inda AfD ta samu kusan kashi 44 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a Saxony-Anhalt.

    Wakiliyar BBC ta ce abin da ake gani shi ne yadda mutane da dama suka gaji da jam’iyyun gargajiya da suka saba bai wa ra'ayinsu.

    Jam’iyyar AfD ta ce za ta nemi goyon bayan sauran jam’iyyu ko kuma wasu daga cikin ƴan majalisar jihar domin samun damar kafa gwamnati a Saxony-Anhalt.

  3. NAHCON ta tunatar da maniyyata ranar da za a rufe biyan kuɗin Hajjin 2027 a Najeriya

    Hajj

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sake tunatar da maniyyatan Hajjin 2027 cewa ranar 26 ga Satumba ce wa'adin kammala rajista da biyan kuɗin aikin Hajjin.

    Hukumar ta yi wannan tunatarwa ne a wasu saƙonni da ta wallafa a safukanta na sada zumunta, inda ta buƙaci maniyyatan da ba su kammala rajista da biyan kuɗaɗen ba da su yi hakan kafin cikar wa'adin.

    NAHCON ta ce wa'adin shi ne jadawalin da hukumomin Saudiyya suka bayar domin shirye-shiryen aikin Hajjin 2027.

    Hukumar ta ce kammala wannan aiki cikin lokaci ya zama wajibi domin daidaita bayanan maniyyata da kuma rabon kujerun jirgi, tana mai gargaɗin cewa rashin cika wa'adin na iya janyo rasa guraben Hajjin da aka ware wa maniyyata.

    NAHCON ta kuma buƙaci hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da maniyyatan da kansu su kammala dukkan matakan da ake buƙata kafin lokacin Hajjin.

    A watan Agusta, NAHCON ta sanar da kuɗin aikin Hajjin 2027, inda maniyyatan da za su tashi daga Maiduguri da Yola za su biya N7,560,822, yayin da na yankin Arewa za su biya N7,672,822.

    Maniyyatan yankin Kudu kuwa za su biya N7,882,822.

  4. Muna da ƙarfin ikon kai wa jiragen ruwan Amurka hari - Iran

    Iran

    Asalin hoton, iRNA

    Muƙaddashin ministan tsaron Iran Majiɗ Ibn-e-Reza, ya ce dakarun sojin ƙasar suna da ƙarfin ikon kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka.

    A cikin ƴan kwanakin da suka gabata, jami'an Iran sun yi iƙirarin cewa sun kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka guda biyu a Tekun Fasha, ta hanyar amfani da makamai masu linzami da ake amfani da su wajen kai hari kan jiragen ruwa.

    Sakataren majalisar ƙoli ta tsaron ƙasa ta Iran, Mohsen Rezaei, ya ce cikin sa'o'i 48 da suka gabata, dakarun sojin Iran sun samu damar gwada makamin da aka ƙera a ƙasar.

    Ya ce: “A karon farko, mun gwada wani makami mai linzami na Iran da aka ƙera domin kai hari kan jirgin yaƙi, a kan wani jirgin ruwan Amurka. Wannan makami ya jefa Amurkawa cikin wani hali na tashin hankali, kuma suka gudu.”

    Rundunar Tsakiyar Sojin Amurka, CENTCOM, ba ta mayar da martani kai tsaye kan iƙirarin Iran ba.

    Sai dai jiya, a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, ta yi alamar cewa ta na magana ne kan harin da aka ce an kai wa jiragen ruwanta guda biyu.

    Ta ce: “Idan kuka harbi jiragen ruwanmu guda biyu, za mu kakaba muku wani mummunan takunkumin tattalin arziki, tare da lalata jiragen ruwanku guda uku.”

    CENTCOM ta ƙara da cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen kare sojojin Amurka ba, kuma idan ya zama dole, za ta lalata jiragen ruwan dakon mai na Iran.

  5. Me zai faru idan ɗalibi ya kasa biyan bashin NELFUND?

    NELFUND

    Asalin hoton, NELFUND

    A ƙarshen makon da ya gabata ne wata sabuwar dambarwa ta ɓarke a Najeriya game da biyan bashin karatu da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shi na NELFUND.

    Mahawarar ta ɓarke ne bayan da aka fitar da hoton wata jarida ɗauke da wani labari da ke nuna shugaba Bola Tinubu ya amince da hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan ɗaliban da suka gaza biyan bashin da suka karɓa daga asusun ba da Lamunin karatu na Najeriya (NELFUND).

    Wannan labarin dai ya tayar da ƙura tsakanin ɗaliban ƙasar musamman waɗanda suka amfana daga shirin lamunin, lamarin da ya sanya daya

  6. Barka da Safiya!!!

    Masa

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai tsaye daga BBC Hausa muna muku barka da safiyar Talata.

    Muslim Muhammad Yusuf tare da sauran abokan aiki ne za mu kasance da ku.

    Za ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin kallon wasu hotuna da bidiyon hirarraki da muke wallafawa tare da yin tsokaci a kai.