Me C.G. Musa ya ce kan Nasir El-Rufai da ya tayar da ƙura?

Nasir El-Rufai da Christopher Musa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Ministan tsaron Najeriya ya haifar da muhawara bayan wasu kalamai da ya furta a tattaunawar da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Channels.

Tattaunawar ta faru ne a ranar Alhamis, inda tsohon babban hafsan sojin na Najeriya ya yi wasu manyan zarge-zarge kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

El-Rufai ya mulki jihar Kaduna tsawon shekara takwas, daga 2015 zuwa 2023, sai dai yanzu haka yana riƙe a hannun hukumomi bisa zarge-zarge da dama waɗanda suka shafi kashe kuɗin gwamnati.

Tattaunawar wadda tun darko ta mayar da hankali kan matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita, ta rikiɗe zuwa zarge-zargen ''kitsa'' kisan mutane a kudancin jihar Kaduna.

Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar tsaro, sai dai kundancin jihar ya yi ƙaurin suna wajen rikici tsakanin manoma da makiyaya, wanda a mafi yawan lokuta yake rikiɗewa zuwa na ƙabilanci.

Me C.G Musa ya faɗi?

A lokacin da yake bayani a cikin shirin sa’ilin da aka yi masa tambaya game da lawo kuri’un mazabarsa, ministan tsaro na Najeriya ya fara bayani, amma sai batun ya koma al’amrin da ya shafi tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

C.G. Musa ya: “Abubuwa sun sauya daga lokacin da El-Rufa'i ya bar mulki, mun san yadda abubuwa suke a lokacin da El-Rufa'i ke mulki, abin babu daɗi, El-Rufai ya tafka abubuwa masu muni a jihar Kaduna, ya raba kawunan jihar zuwa gida biyu.

“Za ka ga cewa idan kana kudanci ba ka isa ka je arewaci ba, wanda ke arewa ba ya iya zuwa kudu,” in ji Musa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya kara da cewa: “Bai kamata a ce ana irin haka ba, a wannan ƙasa wadda ya kamata a ce duk an zama ɗaya.

“Amma Gwamna Uba ya warware hakan a cikin shekara ɗaya, yanzu kowa ya samu ƴanci, kowa yana iya yin magana”.

Lokacin da aka tambaye shi: "Ko har yanzu wasu daga cikinku a kudancin Kaduna kuna jin haushin El-Rufa'i?"

Sai C.G. Musa ya ce: "Idan akwai abin da ya fi jin haushi, to shi ne. Babu yadda za a yi mu ji daɗin wani mutum da ya tsara kashe mutanenmu da gangan."

Lokacin da ɗan jaridar ya yi ƙoƙarin janyo hankalin ministan tsron, kan cewa "wannan gagarumin zargi ne".

Sai Musa ya ce: "Ka kalli bidiyoyinsa da maganganun da ya yi, yana alfahari da abin da ya yi, ya ce ya biya ƴan bindiga kuɗi, ya faɗa cewa ya yi kaza, ya yi kaza, bai ɓoye ba saboda girman kai.

“Kuma bai ba mu dama an yi abubuwa ba, amma yanzu an samu saƙat,” in ji Janar Musa.

Ya ƙara da cewa yana wannan maganar ne a matsayin ɗan Najeriya.

Ya kuma ce ba mutanen Kudancin Kaduna kawai ba, amma "hatta mutanen yankinsa ma ya cuzguna musu, sai ya tura katafila ta rushe gidanka."

“Ina ganin cewa shi kansa ya yi abubuwan da ba ya alfahari da su”.

Ya bayyana cewa bai kamata a bai wa duk wani mai ƙoƙarin rarraba kawuna ba damar jagorantar al'umma.

Kuma ya ƙara da cewa abubuwan da tsohon gwamnan na Kaduna ya aikata ne suka sanya ya gaza samun mukamin minista.

Martani daga ƙungiyoyi

Yayin da ake ci gaba da muhawara kan wadannan kalamai, bangaren tsohon gwamnan na jihar Kaduna bai mayar da martani ba game da lamarin duk kuwa da kokarin samun hakan da BBC ta yi daga mai magana da yawunsa da kuma sauran makusantansa, ciki har da tsofaffin kwamishinoni.

Sai dai daya daga cikin tsoffin kwamishinonin da BBC ta tuntuba ya bayyana cewa bangaren na El-Rufai zai mayar da martani nan ba da dadewa ba, saboda a cewarsa “zarge-zarge me marasa tushe”.

To amma bayan kalaman na Musa mutane da dama a shafukan sada zumunta sun yi ta musayar muhawarori da bidiyoyi da kuma takardu da ke dauke da bayanai, ko dai na kare tsohon gwamnan, ko kuma masu kokarin jaddada abin da ministan tsaron na Nakeriya ya bayyana.

Sai dai daga yankin Kudancin Kaduna, inda ake takaddama kan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa wata kungiya ta mayar da martani, tana kare El-Rufai daga zarge-zargen na C.G. Musa.

A tattaunawa da BBC Hausa, shugaban kungiyar matasa Musulmai ta Kudancin Jihar Kaduna Dr Muhammad Kabir ya ce kalaman ministan tsaro Christopher Musa sun ba su mamaki, kuma halin da ake ciki a yankin ba shi da alaka da El-Rufa'i.

Dr Muhammad ya kara da cewa "kalaman ministan ba wani abu ba ne face manufar siyasa, kuma bai kamata ƴan siyasa su dinga kokarin ɓata wa wani suna don biyan bukatar ransu;

Jihar Kaduna dai ta jima ta na fuskantar tashe-tashen hankula masu nasaba da addini da kabilanci, sai kuma matsalar 'yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Ya ƙara da cewa "bai kamata kalamai irin wannan su fito daga bakin mutum kamar Ministan tsaron Najeriya ba, wanda kamata ya yi ace ya na kokarin tabbatar da zaman lafiya tsakanin 'yan Najeriya ba kalamai da za su tunzura mutane ba a daidai lokacin da kasar ke fama da matsaloli da dama musamman na tsaro."

Yadda rikice-rikicen Kaduna suka samo asali

Kudancin Kaduna, wanda ke iyaka da tsakiyar Najeriya, yanki ne da ya shafe shekaru yana fama da rikice-rikicen siyasa da na ƙabila da addini masu nasaba da fafutukar neman iko da mallakar filaye da na tattalin arziki da kuma albarkatun noma.

A lokutan sauye-sauyen siyasa daban-daban da Najeriya ta fuskanta, ƙabilu da dama na Kudancin Kaduna sun gina tarihinsu da ainihin asalinsu ne bisa raɗaɗin ƙorafe-ƙorafe da suka daɗe suna yi, tare da zargin cewa Hausawa da Fulani, waɗanda suke da tasiri sosai a siyasar yankin, sun yi musu danniya.

Masu nazari sun ce rashin ci gaba da taɓarɓarewar ilimi da talauci da raunin hukumomi da rashin amincewar jama'a da raguwar tasirin sarakunan gargajiya da zargin ware wasu daga harkokin siyasa da kuma ƙarancin damar da matasa ke samu, sun taka rawa wajen rura wutar rikicin.

Sakamakon haka, yankin ya daɗe yana fuskantar munanan rikice-rikicen ƙabilanci, waɗanda galibi ke faruwa tsakanin makiyaya Fulani masu yawo da kuma manoma mazauna yankin.

Sai dai masana na cewa, duk da cewa rikicin na ɗauke da alamun saɓanin ƙabilanci, akwai wasu matsaloli da dama da suka haɗu wuri guda wajen rura shi.

Waɗannan sun haɗa da ayyukan ƴan bindiga a karkara da satar shanu da rikice-rikicen mallakar filaye da amfani da ita, saɓani tsakanin manoma da makiyaya da rikicin hanyoyin kiwo da wuraren kiwon dabbobi da rikicin zaɓe.

Da ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuka da yawaitar makamai ba bisa ƙa'ida ba, da rashin aikin yi a tsakanin matasa da kuma matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Wane ne Nasir El-Rufai?

Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya fara siyasa ne tun daga shekarun 2000, lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya ba shi muƙamin ministan birnin Abuja.

Kazalika, yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar tsohuwar jam'iyyar CPC, da kuma APC ta haɗaka mai mulkin Najeriya a yanzu.

Alaƙarsa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ta ƙullu ne bayan fara yaƙin neman zaɓe na 2023, inda tsohon gwamnan ya tsaya kai da fata wajen nema wa abokin siyasar tasa ƙuri'un 'yan jiharsa ta Kaduna da ma na arewacin Najeriya.

El-Rufai na ɗaya daga cikin gwamnonin Najeriya da suka kai gwamnatin tarayya ƙarƙashin Muhammadu Buhari ƙara kotu saboda sauya takardun kuɗi na naira da ta yi ana dab da gudanar da babban zaɓe na 2023.

Gwamnonin sun zargi gwamnatinsu ta APC cewa matakin sauya kuɗin, wanda ya jawo wahalhalu mas tsanani saboda ƙarancin tsabar kuɗi, zai shafi farin jinin ɗantakararsu Bola Tinubu a zaɓen.

Yayin wata hira da BBC, El-Rufai ya taɓa cewa "a matsayinmu na gwamnonin arewa za mu yi iyakar ƙoƙari wajen ganin mulkin Najeriya ya koma kudu", yana mai nufin hannun Bola Tinubu.

Alaƙar Tinubu da El-Rufai ta lalace ne bayan shugaban ya gaza bai wa tsohon gwamnan muƙamin minista, inda majalisar tarayya ta ƙi tantance shi saboda wani rahoton da ta ce jami'an tsaro sun gabatar a kan sa.

Jim kaɗan bayan haka El-Rufai ya fara adawa da APC da gwamnatin Tinubu, inda a watan Maris na 2025 ya sanar da ficewarsa zuwa jam'iyyar PRP, kuma a yanzu yake cikin gaba-gaba wajen ƙulla haɗakar 'yan'adawa a ADC.