Amurka za ta kai hari kan Dutsen Kallang na Iran

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa manema labarai a ranar Juma'a cewa Amurka na iya kai hari kan Dutsen Kalang da ke Iran nan ba da jimawa ba.
Dutsen Kalang, wanda ke kusa da cibiyar tace sinadarin uranium ta Natanz, wuri ne da ke da tsauraran matakan tsaro, kuma yake ɗauke da manyan rukunin ramukan karkashin ƙasa masu zurfi ƙwarai.
A wani ɓangare na jawabinsa, shugaban na Amurka ya ce rikicin da ake yi da Iran "ƙaramin batu ne" idan aka kwatanta da sauran manyan ƙalubalen da Amurka ta fuskanta.
Tun da farko, Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya ce a ranar Alhamis cewa ba zai bayyana rikicin da Iran da kalmar "yaƙi" ba.
Da yake mayar da martani ga wani ɗan jarida a ranar Juma'a, wanda ya tambaye shi abin da zai faɗa wa Amurkawa game da rikicin da Iran idan ba za a kira shi yaƙi ba, Trump ya ce:
"To, zan gaya muku cewa mutane da dama ba sa kiransa yaƙi. Ni ina kiran sa rikicin soja ne, domin a gare mu abu ne mai ƙarancin tasiri idan aka kwatanta da wasu batutuwa. Ba wani babban al'amari ba ne. Mun ɗauki mataki a Venezuela kuma muka aiwatar da shi. Ba mu yi asarar ko mutum ɗaya ba a Venezuela. Mun rasa mutane 18 a rikicin da Iran. Amma a Yaƙin Vietnam, mun yi asarar mutum 100,000."
Trump ya yi amfani da waɗannan misalan ne domin bayyana cewa, a ra'ayinsa, rikicin da ake yi da Iran bai kai matsayin wasu manyan yaƙe-yaƙen da Amurka ta taba shiga a tarihi ba.


































