Me ya sa ake ci gaba da tsare El-Rufai duk da hukuncin kotu?

Nasir El-Rufai

Asalin hoton, Nasir El-Rufai/Facebook

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • Lokacin karatu: Minti 7

A ranar Alhamis, hukumar tsaron farin kaya a Najeriya (DSS) ta gurfanar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a gaban mai shari'a Joyce Abdulmalik a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

DSS ta gurfanar da shi ne saboda zargin shi da hannu a tatsar bayanai daga wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu.

Hukumomin Najeriya na tsare da tsohon gwamnan ne tun ranar 17 ga watan Fabrairun 2026 kan wasu zarge-zarge da suka shafi rashawa da almundahana, waɗanda tuni ya musanta.

Hukumar EFCC ce ta fara kama shi, kafin daga bisani ta miƙa shi zuwa ga takwararta ta ICPC da ke yaƙi da almundahana da laifukan da suka jiɓanci haka a ƙasar.

A ranar 1 ga watan Afrilun 2026 ne aka miƙa shi zuwa ga hukumar DSS bayan fara sauraron shari'arsa a wata kotu da ke Kaduna.

Kotuna biyu ne ke sauraron shari'ar El-Rufai - ta jiha da ta tarayya - kan laifuka da suka shafi zargin almubazzaranci da dukiyar jihar da kuma waɗanda suka shafi tsaron ƙasa.

A wata sanarwar da ICPC ta fitar a ranar Litinin kan gurfanar da shi a gaban kuliya, hukumar na tuhumar tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da zarge-zarge da dama da suka haɗa da:

  • Karkatar da kadarorin gwamnati ba bisa ƙa'ida.
  • Mallakar kadarorin jama'a ba bisa ƙa'ida ba.
  • Halasta kuɗaɗen haram.

Malam Nasir El-Rufai yana fuskantar wata shari'ar da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS kan zargin satar sauraron wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya musanta zarge-zargen da aka yi masa ciki har da binciken da hukumar ICPC ta gudanar a gidansa wanda ya bayyana da "haramtacce".

Lauyan da ke kare Nasir El-Rufai, Ukpon Akpan ya buƙaci kotun da ta bayar da belin tsohon gwamnan, yana mai cewa hakan na cikin haƙƙinsa a kundin tsarin mulki.

Hukunce-hukuncen da kotuna suka yanke

A ranar 14 ga watan Afrilu, kotun tarayya ta bai wa tsohon gwamnan na Kaduna, Nasir El-Rufai beli kan Naira miliyan 200 a shari'ar zargin almundahana da ake yi masa wadda ICPC ta shigar a kansa, inda ta umarci ya cigaba da zama a hannun hukuma har sai ya cika sharuɗɗan belin.

Mai Shari'a Rilwanu Aikawa da ya yi hukuncin ya ɗage sauraron shari'ar daga ranar 1 zuwa 14 ga watan Afrilu, 2026, domin yin nazari a kan buƙatun ɓangaren masu gurfanarwa da masu bayar da kariya.

Kotun ta kuma umarci cewa wajibi ne ga mutum biyu waɗanda za su tsaya masa su miƙa fasfo ɗinsu, sannan dole ne ɗaya daga cikinsu ya zama jam'i ne na gwamnati mai matsayi na 15 zuwa sama yayin da ɗayan kuma wajibi ne ya kasance sanannen mai sarauta.

Bugu da ƙari, kotun ta haramta wa El-Rufa'i furta wasu kalamai a bainar jama'a game da shari'ar kuma dole ne ya halarci dukkan zama da kotu ta kira.

Nasir El-Rufai

To sai dai babbar kotun jihar Kaduna ta yi watsi da buƙatar bayar da belin El-Rufai, a ci gaba da shari'ar da gwamnatin jihar ke tuhumar sa da almundahanar biliyoyin kuɗaɗe da kuma amfani da muƙami ta hanyar da ba ta dace ba.

A ranar 21 ga watan Afrilu, 2026, mai shari'a Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna ya ɗage zaman sauraron buƙatar zuwa makon farko na watan Yuni, 2026.

Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan (SAN), ya nuna rashin jin daɗinsa kan matakin kotun na ƙin bayar da belin tsohon gwamnan.

"Kotun ta yanke cewa saboda Nasir El-Rufai tsohon gwamna ne, hakan na nufin zai iya tsoma baki a bincike. Saboda haka ba shi da ƴancin samun beli. Muna godiya ga mai shari'a kan abin da ya yi, amma duk da haka ba mu amince da matakin ba," in ji Lauyan.

Ko da yake an saki El-Rufai daga hannun hukumomi a lokacin da mahaifiyarsa ta rasu, inda aka sake kama shi bayan yi mata jana'iza da zaman makoki na kwanaki uku.

Me ya sa ake ci gaba da tsare El-Rufai?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babbar kotun jihar, a wasu bayanan hukuncin da ta yi a ranar 21 ga watan Afrilu, 2026, mai shari'a Darius Khobo ya ce buƙatar belin El-Rufai na cikin wata takarda mai sakin layi 24 da Muhammed Bala Aliyu ya gabatar.

El-Rufai a cikin buƙatar ya ce, laifukan da ake tuhumarsa ba manyan laifukan ƙasa ba ne, kuma a matsayinsa na tsohon gwamna, mazauninsa ba ɓoyayye ba ne kuma za a iya ganinsa a duk lokacin da ake buƙata.

Ya ƙara da cewa, ya dawo Najeriya a ƙashin kansa daga Masar saboda mutunta dokokin ƙasa, kuma yanayin lafiyarsa na buƙatar kulawar likitoci.

Sai dai alƙalin ya zayyano cewa ICPC ta ƙalubalanci buƙatar, inda ya ce zarge-zargen da ake yi wa El-Rufai sun shafi laifukan "zagon ƙasa ga tattalin arziki" kuma tana fargabar wanda ake zargin "zai riƙa katsalandan ga binciken da ake masa da ma sauran mutanen da ake ƙarar"

ICPC ta ba da misali da yadda El-Rufai ya yi tutsu a lokacin da aka samu sa'insa tsakaninsa da jami'ai a filin jirgin saman Abuja a watan Fabrairu, inda ta ƙara da cewa tsohon gwamnan "zai iya tsere wa kamu saboda matsayinsa a cikin al'umma"

Bugu da ƙari, "babu wasu sahihan hujjojin da aka gabatar da suke tabbatar da rashin lafiyarsa," in ji ICPC.

Lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya shaida wa kotun cewa wanda ya ke karewa yana buƙatar belin ne "saboda ƴancinsa na ɗan ƙasa," buƙatar da lauyan ICPC Osuobeni Akponimisingha, ya ƙalubalanta.

Me ya sa alƙalin kotun jiha ya hana belin El-Rufai?

A cikin takardun hukuncin kotun da BBC ta gani, alƙalin kotun Darius Khobo ya ce buƙatar ba da belin El-Rufai abu ne da dole a yi la'akari da shi sosai saboda matsayinsa na tsohon gwamna kuma tsohon minista, wanda hakan zai iya tasiri a shari'ar.

Alƙalin ya ce iƙirarin da ICPC ta yi na cewa El-Rufai zai iya katsalandan a binciken da ake yi da na sauran mutane "abin dubawa ne"

Mai shari'a Khobo ya kuma ƙara da cewa ICPC ta bayar da "gamsassun hujjojin" da za su sa a hana ba da belin El-Rufai, kuma waɗanda suka shigar da buƙatar belin sun kasa gabatar da bayanan da za su ƙalubalanci matakin.

"Sakamkon rashin gabatar da wasu hujjoji daga masu neman belin, waɗanda za su ƙalubalanci buƙatar hana belin, hakan ya gamsar da cewa abin da suka faɗa gaskiya ne, saboda haka na yanke wannan hukuncin [hana belin]" in ji alƙalin.

"Doka ta fayyace cewa: idan aka gabatar da buƙatar beli, amma kuma akwai dalilai masu ƙarfi da suke nuna cewa mutumin da ake tuhuma zai iya tserewa, kuma za a sha wahalar ganinsa ko ya bayyana gaban kotu, ko kuma katsalandan ga binciken da ake yi wajen yanke hukunci, kotu na da hurumin hana belin," a cewar Khobo.

.

Asalin hoton, Others

Mai shari'a Khobo ya ƙara da cewa: "A buƙatar da aka gabatar da farko, wanda ake zargin ba shi da lafiya, kuma yana buƙatar kulawar likitoci, amma kuma bai gabatar da wata takardar shaida da ke tabbatar da iƙirarin nasa ba."

"Doka ta ce, idan mutum yana buƙatar beli a dalilai na rashin lafiya, sai ya gabatar da gamsassun hujjojin da suke tabbatar da hakan a gaban kotu."

"To amma wanda ake zargin, ya kasa gabatar da waɗannan hujjojin, saboda haka ba a amince da buƙatar ba," in ji mai shari'a Khobo.

Daga ƙarshe mai shari'ar ya yanke hukuncin cewa za a ci gaba da riƙe wanda ake tuhumar a hannun hukumar ICPC har zuwa lokacin da za a fara sauraren shari'ar.

Kotun ta ce dukkanin lauyoyin ɓangarorin su tabbatar sun shirya kafin lokacin fara shari'ar saboda za a yi ta ne a kowace rana idan aka fara ba tare da wani uzuri ba.

Za a fara shari'ar ne a ranakun 1, 2, 3, da 4 ga watan Yuni, 2026.

Su ma lauyoyin da ke shigar da ƙara da waɗanda suke kare El-Rufa'i sun amince a fara shari'ar a makon farko na watan Yunin.

.

Asalin hoton, Others

Wane mataki El-Rufai zai iya ɗauka?

Barista Musa Musa Dahiru, ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare El-Rufai a shari'ar da gwamnatin jihar Kaduna ke yi da tsohon gwamnan, ya ce duk da an yanke wannan hukuncin za su ci gaba da bibiya domin sake nazari da kuma ɗaukaka ƙara.

"Akwai mataki na farko na ɗaukaka ƙara na ƙin amincewa da matakin alƙalin. Shi kan shi harkar shari'ar za mu ɗauki matakin da za mu ga an yi abin da ya dace." in ji shi.

Ya ce: "Za mu ɗaukaka [ƙara} a yayin da muke ci gaba da sauraron shari'ar, ai beli daban, ci gaba da shari'a daban. Rashin hana shi beli ba zai sa a ƙi ci gaba da shari'a. Wannan ba yana nufin an kai ƙarshen shari'a ba ne".

"Shi kansa belin nasa za a iya ƙara maimaitawa. Shi kansa alƙalin zai iya yiwuwa a wannan karon ya yi kuskure a mataki na gaba ya gyara," in ji Barista Musa.

Ya ce suna sa ran za a iya bayar da belin El-Rufai kafin ranar da za fara sauraron shari'ar, inda ya ce hukuncin da alƙalin ya yanke ba shi suka yi fata ba.

Baristan ya ƙara da cewa hujjar da kotun ta bayar na cewa El-Rufai na da tasiri a jihar ba abu ne da zai sa a hana belinsa ba.

"Hakan mu a wurinmu, ba abu ne da aƙali ya yi amfani da mahanga ta shari'a ba. Mutum nawa ne waɗanda sun fi El-Rufai muƙami kuma an bayar da belinsu? Ko masu kisan-kai ma, doka tana kallon wani dalili da zai sa ta bayar da belin su," in ji Barista Musa.