Ramadan 2025: Yadda za ku aiko mana da bidiyon girke-girkenku

Girke-girken Ramadan na 2025.
Lokacin karatu: Minti 1

A kowace shekara idan watan azumi ya zo mata da dama kan shiga tunanin waɗanne irin abinci za su dinga tsara wa iyalansu don buɗa baki.

Haka ake fama duk shekara, kuma ba wai don ba su iya girkin ba sai don neman sabbin girke-girken da za a dinga gigita maigida da su.

To a sauƙaƙe kamar yadda muka saba a wannan karon ma BBC Hausa za ta zo maku da hanyoyin burge masu gida cikin sauƙi, tare da taimakon mata 'yan uwanmu.

Ke gwana ce a girki? Za ki iya ba mu dabarar yadda za a sarrafa abinci na zamani ko na gargajiya da zai yi daɗin ci a lokacin azumi?

To ga wata dama ta samu. Ki aiko mana da bidiyo na haɗaɗɗen abinci kala ɗaya wanda bai wuce minti biyu ba.

Tsawon bidiyon kar ya wuce minti biyu. Kuma a farkon gabatarwa ya kasance kin nuna kanki a bidiyon kin faɗi sunanki da kalar abincin da za ki nuna.

Sai kuma a dinga jin muryarki a lokacin da kike haɗa abincin ba tare da ganin fuskarki ba. Sannan ba a buƙatar ki sanya kiɗa a cikin bidiyon.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

Za mu wallafa bidiyon mutum ɗaya a kullum a shafukanmu na sada zumunta tare da tagging ɗinki don sauran mata su amfana da baiwarki.

Sannan a cikin fom din ki aiko da bayanin yadda ake girkin a rubuce da kuma sunayen kayayyakin da ake buƙata don abincin.

Amma fa wannan ba gasa ba ce ta samun kudi, gasa ce ta baje kolin gwanintar ta girki. Latsa nan domin aiko mana da bidiyon girkinku da kuma ganin ƙa'idojin.