Waɗanne dokokin zaɓe ne majalisar Najeriya ta amince a yi wa gyara?

INEC

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026 ne majalisar dattijan Najeriya ta amince da dokar zaɓe da aka yi wa garambawul.

Ɗaya daga cikin gyare-gyaren da aka yi wa dokar ta 2022 shi ne rage wa'adin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke da shi na fitar da sanarwar jadawalin zaɓe daga kwana 360 zuwa 180.

Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da Sanata Tahir Monguno ya gabatar na rage kwanakin da ake buƙatar hukumar INEC ta fitar da sanarwar zaɓe.

Monguno ya bayyana cewa rage wa'adin kwanakin ya zama dole domin hukumar INEC ta cika sharuɗɗan da ake buƙata wajen fitar da sanarwar, inda ya ce tuni aka makara idan aka yi amfani da kwana 360 bisa la'akari da babban zaɓe mai zuwa.

Majalisar dai ta fuskanci matsin lamba kan abin da wasu suka bayyana a matsayin jan ƙafa wurin amincewa da ƙudirin dokar zaɓen.

Sanata Yahaya Abdullahi mai wakiltar Kebbi ta arewa, kuma wakili a kwamitin majalisar dattawa kan gyare-gyare dokar zaɓen ya shaida wa BBC cewa tun bayan zaɓen 2023 ne aka fara nazarin tsohuwar dokar zaɓen domin aiwatar da gyare-gyaren da aka buƙata domin ƙara inganta sahihancin zaɓukan ƙasar.

"Tun bayan zaɓen 2023 aka fara wannan aiki. Sannan an zauna tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, ciki har da ƙungiyoyin mata da matasa da sauran su kafin muka kai ga wannan matakin da ake ciki."

Ya ƙara da cewa sun yi aiki tare da majalisar wakilai, "muna aikinmu, a can majalisar wakilai ma sun zauna domin aiwatar da gyare-gyaren da suka ga sun dace."

Sanatan ya ce a majalisar dattawa, "bayan asalin kwamitin sun kammala aikinsu, sai suka gabatar da zauren majalisa. Shi ne sai muka shiga zama na musamman na sanatoci zalla, inda duka sanatoci kaɗai suke zama domin tattaunawa. A nan ne aka amince a kafa kwamitin mutum 8 domin nazarin gyare-gyare, kuma ina ciki."

Shin za a tura sakamakon zaɓe ta na'ura?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan sanarwar amincewa da batun yi wa dokar zaɓen gyaran fuska an samu suka daga ɓangarori da dama bayan wasu bayanai sun ce majalisar ta ƙi amincewa da ɗaya daga cikin gyare-gyaren da aka daɗe ana taƙaddama a kai.

Rahotannin farko-farko sun ce majalisar ba ta amince da gyaran saɗara ta 60 ƙaramin sashen na 3 na ƙudurin dokar ba, wanda ke neman wajabta tura sakamakon zaɓe ta na'ura.

A maimakon haka sai majalisar ta sake jaddada tsarin da aka yi amfani da shi a baya, wanda ya ce: "malamin zaɓe zai tura sakamako, wanda ya hada da yawan masu kaɗa ƙuri'a da aka tantance da kuma yawan ƙuri'un da aka kaɗa, ta hanyar da hukumar zaɓe ta tsara."

Ƙungiyoyi kamar Yiaga Africa mai rajin kawo sauyi da ƙarfafa dimokuraɗiyya sun bayyana matakin a matsayin "cin amanar al'umma".

To sai dai Sanata Yahaya Abdullahi ya ce "abin da muka amince da shi, shi ne za a tura sakamakon zaɓe ta na'ura".

"Ba gaskiya ba ne cewa ba za a tura sakamako ta na'ura ba," kamar yadda sanatan ya shaida wa BBC.

Sai dai ya ƙara da cewa "ana dai kokwanto kan cewa akwai wasu wuraren da babu intanet, irin waɗannan wuraren za a zo a zauna a san yadda za a yi a tabbatar cewa ba a samu matsala ba."

Mataki na gaba

Sanata Yahaya ya ce yanzu mataki na gaba shi ne gwama gyare-gyaren da majaliar dattawa da waɗanda majalisar wakilai suka yi a wuri ɗaya ya zama kundi ɗaya da za a yi amfanin da shi.

"Dama idan an samu bambanci haka, ana zuwa ne a haɗa kwamiti mai ɗauke da mambobi ƴan majalisar dattawa da ƴan majalisar wakilai sai su zauna su yi aikin tattarawa tare da gwama aikin waje ɗaya."

Sanatan ya ce tuni an kafa kwamitin, amma bai fara aiki ba tukuna, sannan ya ƙara da cewa nan gaba za su zauna kafin a fitar da kwafin ƙarshe na sabuwar dokar zaɓen.

Sai dai ya ce duk da kasancewar sai kwamitocin majalisun biyu sun zauna kafin a ƙarƙare aikin gyare-gyaren, maganar da ake yaɗawa kan aika sakamakon zaɓe ba daidai ba ne.

"Gyare-gyare suna da ɗan dama. Amma abin da muka yarda da shi ne za a tura sakamakon zaɓe ne ta intanet. Kawai dai mun ce a tabbatar an yi tanadi na musamman domin samun intanet a wuraren da ba su da intanet," in ji Sanata Yahaya.

Ya ƙara da cewa akwai batun miƙa wa Inec rajistar ƴan jam'iyya, inda ya ce yanzu dole na kowace jam'iyya ta miƙa sunayen ƴan takararta da ƴaƴan jam'iyyarta baki ɗaya.

Sai dai ya ce an rage lokacin da ya kamata jam'iyyu su miƙa sunaye ƴan takarar, "a da kwana 120, amma yanzu an mayar da shi kwana 90. Sannan kwana 60 kafin zaɓe ne za a kafe sunayen ƴan takara da aka amince da su."

Jinkirin gyare-gyaren

An dai daɗe ana sauraro ganinn gyare-gyaren da za a yi a dokar zaɓen, lamarin da ya wa wasu jam'iyyun siyasa na adawa da ma wasu ƙungiyoyin fararen hula suka bayyana rashin jin daɗinsu, tare da zargin cewa da gangan aka ja-ƙafa.

Daga cikin fitattun ƴan Najeriya da suka tofa albarkacin bakinsu akwai tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya kuma jagoran ƴan hamayyar ƙasar, Atiku Abubakar, wanda ya yi zargin cewa "da gangan majalisa ta ja ƙafa kan aikin gyaran dokar zaɓen" ta Najeriya.

Atiku Abubakar ya yi gargaɗin cewa ci gaba da jinkirin aikin gyaran dokar zaɓen zai iya shafar ingancin babban zaɓen ƙasar na 2027 kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.