'Ana tsaka da shagalin bikina aka yi mana ruwan bama-bamai'

Tarkace a cikin wani ɗaki, gami da fasassun kwanuka a kasa da wani tebur da ya kife

Asalin hoton, Students' Revolutionary Force

Bayanan hoto, Sakamakon harin bam ɗin da aka kai wurin ɗaurin aure a garin Mataw
    • Marubuci, BBC Burmese
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, World Service News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ranar ɗaurin auren Hnin Si a farkon watan Yuni, wanda ya kamata ya zama ranar farin ciki a ƙauyen Mataw da ke yankin Sagaing na Myanmar, ya rikiɗe zuwa bala'i.

Hnin Si ta ce yayin da abokai da dangi kusan 100 suka taru domin murnar bikinta, kwatsam wani jirgin sama ya jefa bama-bamai, inda ya kashe mutane 33, ciki har da mata da yara.

"Bayan an ɗaura mana aure, sai muka fara ɗaukar hotuna da iyalai da abokan arziƙi, kawai sa muka ji bama-bamai sun fara tashi a tsakanin mu yayin da ɗaya kuma ya fashe a kusa da gidan angon." in ji Hnin.

A yayin da mutane ke ƙoƙarin taimaka wa waɗanda suka jikkata tare da kwaso waɗanda suka mutu, sojojin Myanmar kuma suka fara luguden wuta daga wani kogi da ke kusa.

Yankin Sagaing, tare da Mandalay da Magway, wani yanki ne da ke tsakiya da ake yi wa laƙabi da "busashen yanki" na Myanmar, wanda ya kasance cikin kwanciyar hankali har zuwa juyin mulkin soja a 2021.

Taswirar ƙasar Myanmar da ke nuna busasshen yanki na ƙasar, ciki har da yankunan Sagaing, Magway da Mandalay

Shekara uku bayan harin, yankin ya zama sansanin ‘yan adawa masu ɗauke da makamai da aka fi sani da People’s Defence Forces (PDF).

Sojojin sun tashi tsaye wajen fafatawa da sojojin 'yan tawaye na ƙabilanci a yankunan kan iyakar Myanmar, waɗanda galibi suna kai hari kan fararen hula a busashen yankin da ake zargi da tallafawa PDF.

Hotunan tashin bam din a wajen daurin auren da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna gawarwakin da ke ƙarƙashin gine-gine da bishiyoyin da suka faɗo da dai sauransu.

Bishiyoyin kwakwa guda biyu ne suka kare sabbin ma'auratan daga fashewar bam ɗin, amma Hnin Si ta suma lokacin da tarkace daga tashin bam ɗin suka same ta sai washe gari ta farka inda daga wajen wasu kawai taji labarin abinda ya faru.

Rundunar sojin Myanmar dai ba ta ce uffan ba game da harin, ko da yake mai magana da yawun rundunar Janar Zaw Min Tun, ya shaida wa BBC cewa wasu bayanai daga magoya bayan gwamnatin sojin sun nuna cewa PDF na gudanar da wani taro a ƙauyen da sunan bikin aure.

Trees lying on the ground with a damaged building in the background

Asalin hoton, Students' Revolutionary Force

Bayanan hoto, Kimanin mutum 100 ne suka halarci ɗaurin auren a garin Mataw lokacin da harin ya faru

Tashoshin Telegram da sojoji ke marawa baya sun ce an kai wa ƙauyen hari ne saboda ƴan ƙungiyar PDF guda biyu ke aure.

Sai dai Hnin Si ta ce mijinta farar hula ne yayin da kuma ita mamba ce ta PDF a baya, inda yanzu tana aiki da hukumar gudanar da Jama'a, wani ɓangare na gwamnati mai kama da juna a yankunan da ke da PDF.

Hnin Si ba sunanta na gaskiya ba ne, amma suna ne ta da bai wa kanta bayan juyin mulkin ƙasar.

Ta yi imanin cewa wani mai ba wa gwamnatin mulkin soja bayyanai ne ya kitsa harin wanda aka kai ta sama a ƙauyensu.

Ta ce: “Wataƙila akwai mutanen da suke jin haushina tunda kasance wani ɓangare na juyin juya hali tun daga farko."

Mazauna yankin Sagaing suna mika furanni ga sojojin PDF a watan Agusta 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu sa kai sun kafa dakarun tsaro a yankin Sagaing sakamakon juyin mulkin shekarar 2021
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar Nyan Lynn Thit Analytica (NLTA), wata ƙungiyar bincike da ɗalibai da masu fafutuka suka kafa, yawan hare-hare ta sama da gwamnatin mulkin soji ke ci gaba da yi ya ƙaru cikin shekaru uku da juyin mulkin da sojoji suka yi.

A cikin watanni huɗun farko na shekarar 2024 kaɗai, an kai hare-hare ta sama guda 819, guda 119 a Sagaing, na biyu mafi girma bayan Rakhine.

NLTA ta kuma bayar da rahoton cewa sama da makarantu 100 da gine-ginen addini kusan 200 ne suka lalace sakamakon hare-haren jiragen sama tun bayan juyin mulkin.

Cibiyar Nazarin Dabaru ta Duniya (IISS) ta ce dabarun mulkin soja a yankuna sun canza a shekarar 2023. Yayin da aka tura ƙarin sojoji a yankin, in ji ta, ana kai hare-hare inda aka kona kauyuka ba gaira ba dalili bayan harin PDF ya ba da damar ƙarin ayyukan share fage.

Wannan ya haifar da ƙaruwar tashin hankali abin da rahoton IISS a watan Yuli 2023 ya bayyana a matsayin "mummunan zalunci".

A wasu lokuta, sojoji suna kai farmaki ƙauyukan da jerin sunayen wasu sanannun ‘yan PDF, inda suke yin alƙawarin ba za su ƙona ƙauyukan ba idan mazauna garin suka ba da bayyanai game da su.

NLTA ta ce an kashe mutum 46 a cikin watanni huɗu na farkon shekarar 2024.

BBC ta tuntuɓi sojojin don jin ta bakinsu kan waɗannan rahotanni amma ba su samu amsa ba.

A village in Myanmar's Sagaing region on fire

Ita ma PDF din tana da hannu wajen ƙonaƙkauyuka da kashe fararen hula.

A ranar 9 ga watan Mayu, wasu ƙungiyoyin PDF da dama sun kaddamar da harin hadin gwiwa a ƙauyen Soneywa da ke yankin Mandalay, wanda wasu mayakan sa-kai masu goyon bayan gwamnatin soji mai suna Pyu Saw Htee ke iko da shi. An kashe fararen hula 31 a harin.

Bayan kwanaki biyu, sojojin gwamnatin mulkin soja suka mayar da martani da kisan kiyashi a kauyen Let Htoke Taw da ke yankin Sagaing.

Yan Naing (ba sunansa na gaskiya ba) ya farka da asuba da jin ƙarar harbe-harbe da fashewar abubuwa. “Na yi gaggawar tayar da babur na don in tsere, amma na ga sojoji suna tahowa daga bangarorin kauyen,” in ji matashin mai shekaru 30.

Ya yanke shawarar gudu zuwa gidan sufi na ƙauyen, inda mafi yawan mutanen ƙauyen suma suka ɓuya.

Da sojojin suka isa gidan sufin, sai suka umarci dukan mutanen da su durƙusa a tsakar gida, su kalli ƙasa. “Wasu daga cikinsu suna ihu, ‘Za mu kashe ku duka,’ ” Yan Naing ce.

Sojojin sun zargi mutanen kauyen da kare ‘yan PDF inda suka buƙaci su miƙa su.

Bayan haka, a cewar Yan Naing, wani babban soja ya ba da umarnin a fara harbi.

Tokar Let Htoke Taw bayan ta kone kurmus
Bayanan hoto, Sojojin mulkin soja sun mayar da mafi yawan Bari Htoke Taw tamkar tarin toka