'Ana iya far mana a kodayaushe kuma a ko'ina’: Rayuwar likitoci mata a Indiya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, BBC Indian Language Services
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
"Ina ganin abin ya isa haka. Yanzu lokaci ne da za mu fito mu yi zanga-zanga, lokaci ne da za mu nuna fushinmu, ba za a ci gaba a haka ba," in ji Anusha Das, wata ɗaliba a birnin Kolkata da ke jihar West Bengal ta Indiya.
Ms Das ta shiga cikin dubban matan da suke tattaki a kan tituna domin zanga-zangar nuna fushi kan kisan da aka yi wa wata likita mai neman ƙwarewa, wadda aka kashe lokacin da ta yi aikin dare a wata asibiti, cikin makon da ya gabata.
Matashiyar likitar mai shekara 31 ta kwanta ne tana hutawa a wani ɗakin taro bayan ta sha aiki a ɗaya daga cikin asibitoci mafi daɗewa a Indiya.
Amma washegari, sai abokan aikinta suka tsinci gawarta a kan dandamalin gabatar da jawabi tsirara da ɗauke da munanan raunuka.
Daga baya ƴansanda sun kama wani ma'aikacin sa-kai na asibitin wanda ake zargi da hannu a lamarin, wanda suka bayyana a matsayin batu ne na zargin yin fyaɗe da kisa a asibitin na RG Kar Medical, da ke Kolkata.
Masu zanga-zangar da aka gudanar a cikin dare, na nema ne a yi adalci ga marigayiyar sannan kuma a tabbatar da tsaron lafiyar miliyoyin matan ƙasar ta Indiya.
Masu shirya zanga-zangar sun ce sun zaɓi daren ne, wanda shi ne daren ranar tunawa da samun ƴancin kan ƙasar, domin su tambayi hukumomi, sai yaushe ne matan Indiya za su samu ƴanci.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Muna son dare ya daina zama barazana ga mata, ko maza da ma kowa," kamar yadda wata mai zanga-zanga ta bayyana, wani abu da da dama daga cikin mutanen da BBC ta zanta da su a asibitoci ke rajin gani.
Fyaɗe da kisan da aka yi wa likitar ya tuno wa al'umma da makamancin irin hakan da ya faru a shekarar 2012, lokacin da wasu suka yi wa wata ɗaliba likita fyaɗen taron dangi a cikin motar bas a birnin Delhi, lamarin da ya yi ajalinta.
Cin zarafin mata wata babbar matsala ce a Indiya - bayanan gwamnati sun nuna cewa an samu matsalar fyaɗe kimanin sau 90 a kowace rana a cikin shekarar 2022.
S Abarna, wata ɗaliba mai neman ƙwarewa a wani asibitin da ke birnin Chennai, ta ce abin da ya faru da ɗalibar da aka kashe a Kolkata ya haifar da fargaba a tsakanin mata ma'aikata.
Ta ce yanzu an yanzu ce wa ɗalibai masu neman ƙwarewa su riƙa amfani da ofishin manyan likitoci, kuma na ce musu su riƙa rufewa gam idan suna cikin ofishin.
Haka nan an ba su shawarar su riƙa amfani da da watan manhajar neman ɗauki na gaggawa ga ƴansanda, amma ta ce duk da haka "komai na iya faruwa a kowane lokaci."
Ta ƙara da cewa amma "samar da wayar tarho na oba-oba a ɗakunan kwantar da marasa lafiya zai iya taimakawa."
Tun bayan fyaɗen taron dangi da aka yi wa ɗalibar likitanci a cikin bas a birnin Delhi, hukumomi sun tsaurara hukuncin da ake yanke wa masu fyaɗe a ƙasar, sai dai duk da haka yawan fyaɗen da ake yi ya ƙaru a ƙasar, sannan kuma samun adalci ga matan da ake yi wa fyade na da wahala a ga mata, in ji masana.
Wannan fyaɗe da aka yi na baya-bayan nan a Kolkata ya ƙara taso da batun ƙalubalen da ma'aikatan lafiya ke fuskanta, waɗanda suka buƙaci a riƙa yin cikakken bincike da kuma samar da doka wadda za ta kare ma'aikatan lafiya a wuraren ayyukansu - musamman mata.
Ministan lafiya a Indiya, JP Nadda ya bai wa likitoci tabbacin cewa gwamnati za ta tabbatar an kawo tsaurararn matakai domin kare lafiyarsu a wurin aiki.
A wannan mako kuma hukumar kula da ma'aikatan lafiya ta Indiya ta fitar da wasu shawarwari ga duk makarantun koyar da ilimin likitanci ta yadda za su kare ma'aikata.
Wani rahoton jaridar harkokin lafiya ta Lancet ya bayyana cewa an bayar da rahoton mummunan hari da aka kai wa mata masu aikin lafiya a Indiya sau 153 a ƙasar Indiya tsakanin shekarun 2007 zuwa 2019.
Rahoton ya kuma yi bayani kan wasu dokokin da gwamnatin tarayya da na jihohi suka samar domin hukunta masu far wa ma'aikatan lafiya.
Lunguna masu duhu

Asalin hoton, Getty Images
"Nakan ji tsoro idan zan tafi asibiti daga ɗakin kwana a cikin dare," in ji wata likita da ke birnin Mumbai.
Wurare masu duhu na jefa irin waɗannan ma'aikata cikin fargaba. Wasu ma na fargabar su fita neman abinci, a maimakon haka sun gwammace su sayi abinci ta intanet.
"Idan muna aikin dare, muna buƙatar mu tashi daga wani gini zuwa wani. Amma babu masu gadi ko wasu jami'an tsaro a hanyoyin da muke ba," in ji wata likita da ke aiki a birnin Hyderabad.
Wasu ma'aikatan sun shaida wa BBC cewa suna damuwa ƙwarai da rashin wutar da ake sawa a kan hanya.
Sai dai hukumomi sun dage cewa suna bakin ƙoƙarinsu wajen samar da kariya ga ma'aikata.
Wani shugaban asibiti ya shaida wa BBC cewa an ƙara yawan kyamarar tsaro ta CCTV a makarantar koyon likitanci sannan kuma an samar da mutanen da za su riƙa sauraron ƙorafi a kowane lokaci, dare da rana.
Babu wuraren hutawa
Mata likitoci da dama sun ce akwai ƙarancin wuraren hutawa a lokacin aikin dare.
Wata likita a birnin Hyderabad ta faɗa wa BBC cewa babu ɗakin da aka ware wa mata likitoci na hutawa a lokacin da suke aiki.
"Gadon hutawar maza da na mata na jere ne gefe da gefe. Ba na jin daɗin hakan, kuma ba na iya sakewa. Saboda haka idan dare ya yi nakan je ɗakin kwanan ɗalibai ne da ke kusa idan ina so na huta," in ji ta.
Haka nan wasu ma'aikatan sun shaida wa BBC cewa hatta ban ɗakunansu babu tsafta kuma ba a faɗakar da mutane yadda za su kare kansu daga cin zarfai na lalata.
Barazana daga iyalan marasa lafiya

Asalin hoton, Getty Images
Haka nan ma barazana ta baka ko ta duka daga dangin marasa lafiya shi ma wani babban ƙalubalai ne ga likitoci.
Wata malamar jinya ta ce "sau da dama muna fama da mutanen da suka bugu da barasa a lokacin aikin dare."
Wani nazari a 2023 kan cin zarafin ma'aikatan lafiya ya nuna cewa cuzguna wa ma'aikatan lafiya ya fi faruwa ne a asibitocin gwamnati idan aka kwatanta da asibitoci masu zaman kansu.
Rahoto daga Umang Poddar, Saiyed Moziz Imam na BBC Hindi; Saradha Venkatasubramanian, BBC Tamil; Balla Satish, BBC Telugu; Sarabjit Singh Dhaliwal BBC Punjabi; Laxmi Patel, BBC Gujarati; Dipali Jagtap, BBC Marathi.







