Isra'ila na ci gaba da kai hari a Lebanon shekara guda bayan tsagaita wuta

Asalin hoton, Neha Sharma/BBC
A ranar Juma'ar da ta gabata da misalin ƙarfe 7:00 na yamma ne jiragen yaƙin Isra'ila suka kai hari kan wata mota a wani ƙauye da ke kudancin Lebanon mai suna Froun.
Wannan ɓangare na ƙasar, shi ne cibiyar al'ummar Musulmi mabiya Shi'a, kuma tsawon shekaru da dama yana ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hezbollah, da ƙungiyar ƴan Shi'a ta Lebanon da kuma jam'iyyar siyasa.
A kan tituna, an rataye tutoci ɗauke da fuskokin mayaƙan da aka kashe a yaƙin inda ake nuna su a matsayin "shahidai 'yan gwagwarmaya".
Na isa Froun awa ɗaya bayan harin. Tuni dai masu aikin ceto suka kwashe sassan jikin mutum ɗaya tilo da ya mutu- mutumin da sojojin Isra'ila suka bayyana a matsayin "ɗan ta'addar Hezbollah".
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, wanda ya kawo ƙarshen yaƙin baya-bayan nan da ƙungiyar Hezbollah, Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren bam, kusan kowace rana.
Isra'ila ta ce tana kai hari kan ƙungiyar Hezbollah ne da kuma yunƙurin ƙungiyar na murmurewa bayan ta sha kashi sosai a yaƙin. Na yi tattaki zuwa kudancin Lebanon domin ganin tasirin yaƙin da Isra'ila ke yi, na ga cewa hare-haren sun wargaza tunanin jama'a kan batun tsaro da ma wasu ra'ayoyi da suka daɗe suna riƙe da su a yankunan da ƙungiyar Hezbollah ta saba samun goyon bayansu.

Asalin hoton, Neha Sharma/BBC
Tsagaita wutar da aka yi a Lebanon ya kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe watanni 13 ana yi wanda ya yi sanadiyar mutuwar ƴan Lebanon 4,000 da 120 na Isra'ila. Isra'ila da Hezbollah sun shafe shekaru da dama suna gwabza faɗa, kuma wannan rikici ya fara ne lokacin da Hezbollah ta fara harba rokoki da makamai masu linzami a yankuna Isra'ila kwana guda bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da gagarumin martanin soji kan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoban 2023.
Tsagaitawar da Amurka da Faransa suka shiga tsakani, ta buƙaci ƙungiyar Hezbollah ta janye mayaƙanta da makamanta daga kudancin kogin Litani mai tazarar kilomita 30 daga kan iyakar ƙasar da Isra'ila, sannan sojojin Isra'ila su janye daga yankunan kudancin Lebanon da suka mamaye a lokacin yaƙin. Daga nan ne za a tura dubban sojojin Lebanon zuwa yankunan da ke ƙarƙashin ikon Hezbollah.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan shekara guda, sojojin Isra'ila na ci gaba da mamaye aƙalla tuddai biyar a kudancin ƙasar Lebanon, kuma sun kai hare-hare ta sama da na jiragen yaƙi marasa matuƙa a duk faɗin ƙasar kan wuraren da suke iƙirarin suna da alaƙa da ƙungiyar Hezbollah. A ranar Lahadin da ta gabata, ta kashe babban hafsan ƙungiyar da wasu mutane huɗu a wani harin da suka kai a wani gini da ke gundumar Dahieh da ke wajen birnin Beirut.
Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon (UNIFIL) da ke aiki a kudancin kogin Litani, ta ce Isra'ila ta aikata ayykan da suka saɓawa jarjejebiyar sama da 10,000 ta sama da ta kasa yayin tsagaita bude wutar. A cewar ma'aikatar lafiya ta ƙasar Lebanon, sama da mutane 330 ne aka kashe a hare-haren da Isra'ila ta kai ciki har da fararen hula.
Jami'an Isra'ila sun ce ƙungiyar Hezbollah ta na ƙoƙarin sake gina ƙarfin sojinta a kudancin Litania, wanda hakan zai zama saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wutar, sannan kuma ta yi ƙoƙarin shigar da makamai cikin ƙasar Lebanon tare da ƙara ƙaimi wajen ƙera jiragen yaƙi maras matuƙa a madadin rokoki da makamai masu linzami.
Ya zuwa yanzu dai Isra'ila ba ta bayar da shaidar da ta ce tana da su a bainar jama'a ba. Amma, an kwashe makwanni ana yi wa ƴan jaridar Isra'ila bayani game da shirye-shiryen da ake yi na ƙara matsin lamba kan ƙungiyar. ''Ministan tsaron Isra'ilan Isra'ila Katz ya bayyana a baya-bayan nan cewa, Hezbollah na tonon faɗa, kuma shugaban ƙasar Lebanon yana jan kafa.''

Asalin hoton, Neha Sharma/BBC
Joseph Aoun, shugaban ƙasar Labanon, ya hau karagar mulki a watan Janairu, yana mai alƙawarin cewa "gwamnati ce kaɗai za ta mallaki makamai" - a takaice dai, don kwance damarar Hezbollah. Ƙasashen da suka haɗa da Birtaniya da Amurka suna ɗaukar ƙungiyar a matsayin ƙungiyar ta'addanci. Amma a Labanon, Hezbollah ta fi ƙarfin ƙungiyar ƴan bindiga kaɗai. Duk da raunin da Isra'ila ta yi ma ta a baya-bayan nan, har yanzu jam'iyyar siyasa ce mai ƙarfi da ke da wakilci a cikin gwamnati da majalisa, inda ta ke bayar da gagarumin gudunmawa waurin inganta zamantakewa, da samar da ayyuka a yankunan da jihar ba ta tasiri.
Tun bayan da tsagaita wutar ta fara aiki, ƙungiyar ba ta kai hari kan Isra'ila ba, duk da cewa ta harba rokoki da dama da suka sauka a sansanin sojojin Isra'ila a yankin tsaunin Dov/Shebaa da ake takaddama a kai a tuddan Golan da ta mamaye a cikin watan Disamba, a matsayin martani ga abin da ta ce Isra'ila ta yi na keta yarjejeniyar.

Asalin hoton, Neha Sharma/BBC
Na wuce zuwa ƙauyen Yaroun da ke kan iyaka. Daga nan na ga wani katangar kankare da sojojin Isra'ila suka gina a cikin ƙasar Labanon. Hukumomin ƙasar sun ce wannan wani mataki ne na Isra'ila da ta saɓawa yarjejeniyar tsagaita wutar, da kuma keta hurumin ƙasar.
Al'ummomin Lebanon da ke kan iyaka har yanzu suna zaune a gidajen da suka ruguje - kawo yanzu sauran ƙasashe abokan huldar Lebanon sun ki bayar da kuɗaɗe don sake gina su, a wani ɓangare na ƙoƙarin kwance damarar Hezbollah - inda sojojin Isra'ila suka samar da wani yanki na tabbatar da tsaro. Dubbban ƴan ƙasar Lebanon ne suka ci gaba da gudun hijira, ba tare da sanin lokacin da za su iya komawa ba.
A dandalin birninYaroun, akwai wani allo mai ɗauke da hoton marigayi shugaban ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah, wanda aka kashe a harin da Isra'ila ta kai a Dahieh a lokacin da rikicin ya ɓarke a bara.











