Wane ne Bayajidda da ake iƙirarin ya kafa ƙasar Hausa?

Sarkin Daura Umar Farouk Umar

Asalin hoton, Facebook/Daura Emirate Council

Bayanan hoto, Dr. Umar Farouk Umar ne sarkin Daura a yanzu, wanda ya hau mulki a watan Fabrairun 2007
    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 8

Tatsuniya da hikayoyin Hausawa sun nuna cewa asalin masarautun ƙasar Hausa sun dogara ne da Yariman Bagadaza mai suna Abu Yazid, wanda aka fi sani da Bayajidda.

Labarin yariman ya nuna cewa ya taso ne daga Bagadaza, wanda shi ne babban birnin ƙasar Iraƙi a yanzu, zuwa yankin Hausawa a arewacin Najeriya.

Kamar yadda Farfesa Aliyu Abubakar Liman na Jami'ar Ahmadu Bello ya ruwaito a maƙalarsa mai suna 'Memorializing a Legendary Figure: Bayajidda the Prince of Bagdad in Hausa Land', Bayajidda ya tsallake masarautu da al'adu da dama kafin ya ƙaraso ƙasar Hausa.

Kamar kowace hikaya, ita ma tatsuniyar Bayajidda na shan suka daga masana tarihi da al'ada, waɗanda ke ganin akwai ayoyin tambaya game da labarin idan aka kwatanta su da al'adun Hausawa.

Tatsuniyar mai ruwayoyi da yawa na cikin mafiya shahara a ƙasar Hausa, wadda ta samo asali daga garin Daura na jihar Katsina.

Wasu ruwayoyin na cewa Bayajidda ya bayyana ne tsakanin ƙarni na 16 zuwa na 19, yayin da wasu ke cewa akwai shaidar samuwarsa a al'adar Hausawa tun cikin ƙarni na tara zuwa na 10.

Yadda Bayajidda ya isa ƙasar Hausa

Mahaya dawaki

Asalin hoton, Getty Images

An hakaito cewa Bayajidda ya nufi yammacin duniya ne daga inda ya taso, kuma ya wuce masarautu da al'adu masu yawa kafin ya shiga yammacin Afirka.

Isarsa garin ke da wuya, Bayajidda ya ƙwanƙwasa ƙofar gidan wata tsohuwa da ake kira Ayana, wadda ta tarɓe shi tare da tawagarsa cikin girmamawa irin ta Hausawa bayan isarsu daga yankin Borno.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An ce a garin Borno ya fara ya da zango, har ma ya auri gimbiyar garin mai suna Magira.

Dole ta sa Bayajidda ya bar garin ba tare da shiri ba saboda rigingimun kishi da hassada na 'ya'yan sarki da ya tsinci kansa a ciki.

An ce wasu mata da masu adawa da shi sun fara adawa ne bayan sun fahimci ya fara samun ƙauna da goyon bayan sarkin Borno saboda kaifin basira, da iya kokawa da jarumtarsa.

Yarima-yariman Masarautar Borno sun zargi Bayajidda yunƙurin yi wa sarki Mai juyin mulki, wanda shi kuma ya bayar da umarnin kamawa da kuma gurfanar da Bayajidda.

An ce kafin aiwatar da umarnin sarkin ne kuma labari ya je wa Bayajidda ta hannun matarsa Magira, kuma yana jin haka ya tattara nasa ya nasa suka fice daga garin tare da matarsa da jama'arsa.

An ce lokacin da ya gudu daga Borno matarsa na da cikin ɗansa na farko, saboda haka ne bai iya yin tafiya mai nisa da ita ba, abin da ya sa ya bar ta a Garun Gabas ko kuma Biram - mai nisa daga Masarautar Borno kuma wanda ba shi ƙarƙashin ikonta.

An ce ya bar ta a hannun sarkin garin tare da alƙawarin zai koma wajenta bayan ta sauka, inda shi kuma ya nausa garuruwan tsakiyar ƙasar Hausa har tafiya ta kai shi garin Daura.

Dalilin da ya sa Daurama ta auri Bayajidda

Sarkin Musulmi

Asalin hoton, Ahmad Kabeer Greenlight Photography

An ce bayan ya isa ƙasar garin Daura na jihar Katsina ya auri sarauniya mai mulkin garin da ake kira Daurama.

Ruwayoyi sun ce Daurama ta zama sarauniyar Daura, ɗaya daga cikin garuruwan Hausa mafiya girma da shahara, duk da cewa ba ta da aure kuma har sai da ya isa garin sannan ta aure shi bayan an ba ta labarin jarumta da kuma kyawunsa.

Aurensa da Dauram ya faru ne bayan wasu al'amura da suka faru waɗanda suka sa shi nuna jarumtar kashe wata shirgegiyar macijiya ko kuma mesa da ake kira Sarki.

Macijiyar ta hana mutane ɗiban ruwa a wata rijiya mai suna Kusugu, wadda ita kaɗai ce a garin, sai a ranakun Juma'a kawai.

An ce Bayajidda ya tafi ɗebo ruwa a rijiyar ne ranar Alhamis da dare.

Bayan macijiya ta yi yunƙurin hana shi ɗiban ruwan ne shi kuma ya fito da takobi kuma ya sare kanta.

Nan take labarin bajintarsa ya karaɗe gari, inda Sarauniya Daurama ta yi alƙawarin raba masarautarta biyu tare da bai wa wanda ya yi bajintar.

Daga nan ne kuma mutane da yawa suka shiga yin iƙirarin cewa su ne suka kashe macijiyar ba tare da kawo ƙwaƙƙwarar hujja ba.

Wannan ta sa tsohuwa Ayana ta kai wa sarauniya rahoton cewa baƙonta ya yi bajintar kashe macijiyar bayan ta yi bakin ƙoƙarinta wajen hana shi zuwa rijiyar.

Sarauniya Daurama ta sa aka kirawo Bayajidda kuma ta nemi hujja, inda shi kuma ya fito mata da makeken kan macijiyar, wanda aka ce ya kai girman kan doki.

Sai dai an ce Bayajidda ya ƙi yarda ya karɓi kyautar. A madadin haka, ya nemi ya aure ta kuma ta amince ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Babu daɗewa Daurama ta fara shiga takaicin kasa samun haihuwa da Bayajidda. Saboda haka ne ta yanke shawarar ba shi baiwa domin ta haifa masa ɗa.

Cikin ƙanƙanin lokaci baiwar ta samu ciki kuma ta haifi ɗa namiji, wanda aka saka masa suna Kamagari (wato karɓe gari).

Babu daɗewa ita ma Daurama ta haifi nata ɗan namiji, kuma aka saka masa suna Bawo (wato kawo garin da ka karɓe).

Hausa Bakwai da Banza Bakwai

Hausawa

Asalin hoton, Getty Images

Auren Daurama da Bayajidda ya yi albarka sosai saboda an samu magada a tsakaninsu, a cewar hikayoyin.

Bayan 'ya'yansu biyu - na sarauniya da na baiwa - sun girma, su ma sun haifi yara maza da yawa.

'Ya'yan Bawogari shida sun yi sa'ar tasowa da bajinta irin ta kakansu, abin da ya sa suka bazama duniya tare da kafa garuruwan Hausawa da suka haɗa da Gobir, da Kano, da Rano, da Zazzau, da Katsina, da Biram, da kuma Daura wanda Daurama ta bai wa mahaifinsu.

Garuruwan da Bawo ya kafa ana kallon su a matsayin halastattun garuruwan Hausawa (Hausa Bakwai) saboda kasancewarsa jikan Sarauniya Daurama.

A wani ƙaulin kuma, an ce ƴaƴan Kamagari, wanda baiwar da Bayajidda ta haifa masa ne suka kafa garuruwan da ake kira Banza bakwai - saboda kasancewarsa ɗan baiwa.

Garuruwan da ake kira Banza Bakwai su ne Kebbi, da Zamfara, da Gwari (Birnin Grawi), da Kwararafa (Jukun), da Oyo (garin Yarabawa a yanzu), Nupe, da kuma Yauri.

A gefe guda kuma, wasu hikayoyin na cewa ɗaya daga cikin sarakunan Biram jikan gimbiyar Borno ne Mariga wadda Bayajidda ya bari a garin a kan hanyarsa ta zuwa Daura.

An ce wannan salsalar ce ta zama asalin sarakunan Haɓe a ƙasar Hausa.

Masana tarihi na cewa sarakunan Haɓe sun mulki ƙasar Hausa fiye da ƙarni biyar kafin zuwan jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo a ƙarni na 19, wanda ya kafa Daular Sokoto, kamar yadda Farfesa Aliyu Liman ya bayyana.

Da gaske an yi Bayajidda a tarihi?

Masana tarihi da al'adun Hausawa sun kwana biyu suna muhawara game da ko tatsuniyar Bayajidda na ɗauke da ƙamshin gaskiya, ko kuma ma ƙarya ce baki ɗaya.

Farfesa Abdalla Uba Adamu masanin kimiyyar sadarwa ne kuma malami a Jami'ar Bayero da ke Kano, kuma yana ɗaya daga cikin masu ganin ba a taɓa yin Bayajidda ba a tarihi.

"Ni ban yarda akwai wani Byajidda ba," kamar yadda ya shaida wa BBC a wata hira da aka yi a 2017.

"Misali, lokacin da Mansa Musa ya tashi daga Mali zuwa Makka, marubutan Larabawa sun lura cewa lallai akwai wani hamshaƙin mai kuɗi da ya wuce kuma ya dawo, har ma suka dinga biyo shi, abin da ya sa kenan aka san inda Mali take," in ji shi.

"Saboda haka babu yadda za a yi a ce akwai ɗan sarki da jama'arsa sun taho tun daga Bagadaza, ya tsallake Tekun Maliya har zuwa yammacin Afirka kuma ba a samu wani marubuci da ya rubuta labarinsa ba."

Masanin ya kuma ce duk mutumin da ba shi da alaƙa da garuruwa bakwai da ke arewacin Najeriya, to ba Bahaushe ba ne. "Sai dai a kira shi mai magana da harshen Hausa," in ji shi.

Garuruwan su ne Kano, da Katsina, da Daura, da Zazzau, da Rano, da Gobir da kuma Biram. Amma farfesan ya yarda cewa Daura ce asalin ƙasar Hausa.

Sai dai Farfesa Tijjani Muhammad Naniya na sashen Tarihi a Jami'ar Bayero bai yarda da batun cewa ba a yi Bayajidda gaba ɗaya a tarihin Hausawa ba, yana mai cewa babu wani abu a duniya da ake zancensa ba tare da babu shi ba.

"Duk abin da ka ga ana maganarsa to akwai shi. Zan yarda idan aka ce ƙila an yi ƙarin gishiri, ko kuma an yi wani kuskure a labarin, amma ba wai a ce babu shi ɗungurungum ba''.

Ayoyin tambaya game da sahihancin labarin Bayajidda

Ƙofar Masarautar Kano

Asalin hoton, Maikatanga Photography

Masana da dama sun sha ɗiga ayoyin tambaya game da sahihancin wasu iƙirari da aka yi a labarin Bayajidda, musamman sashen da ke cewa shi ne ya kafa ƙasar Hausa da kuma batun Banza Bakwai da Hausa Bakwai.

Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ɗaya ne daga cikin masana harshe da al'adun Hausa, waɗanda ke ganin babu gaskiya a waɗannan iƙirarin biyu.

Ya zayyana wa BBC wasu daga cikin dalilansa kamar haka:

Ƙasar Daura ta yi shekaru da dama kafin Bayajidda

Farfesa Bunza ya ce alamu sun nuna cewa mazauna Daura da Bayajidda ya tarar sun shafe shekaru masu yawa kafin zuwansa.

Dalili shi ne, mutanen har sun yi zaman da za su haƙa rijiya, kuma suke da tsarin mulki irin na sarauta.

Duk al'ummar da ta gina rijiya tana da daɗewa kenan, kamar yadda ake kafa misali da rijiyar Zamzam ta garin Makka.

Wane littafi Bayajidda ya taɓa wallafawa?

Farfesa Bunza na ganin duk Larabawa da Turawan da suka shigo ƙasar kan taho ko kuma su rubuta littafi game da rayuwarsu a garin.

Abin tambaya shi ne, wane littafi Bayajidda ya taɓa rubutawa?

Ina ne kabarin Bayajidda?

Wani abu da ba a sani ba shi ne inda aka binne Bayajidda bayan mutuwarsa.

Farfesa Bunza ya ce akwai ƙabarin jikan Sayyadina Ali wanda ya rasu bayan zuwansa ƙasar Hausa.

Maganar Hausa Bakwai da Banza Bakwai ba gaskiya ba ce

Farfesan ya ce wasu masana sun ƙarƙare cewa Turawan mulkin mallaka ne suka ƙirƙiro maganar Hausa Bakwai da Banza Bakwai, domin babu ita a tarihin Hausawa.

A cewarsa, idan har da gaske 'ya'yan Bayajidda wato Bawo da Kamagari ne suka kafa garuruwan Banza Bakawai da Hausa Bakwai, me ya sa ba a taɓa samun wani jar fata ba a cikin sarakunansu tun da mahaifinsu Balarabe ne?

Ya ƙara da cewa babu wata tatsuniya ko waƙa ta Hausawa da ke nuni ga maganar Hausa Bakwai ko Banza Balkwai.

Haka nan, babu wani sarki a ƙasar Hausa da ke alaƙanta kan sa da wannan taken.

Shi ma Farfesa Abdalla Uba ya ce: " Babu yadda za a yi a ce sarakunan da suka mulki garuruwan Hausawa maguzawa ne, amma kuma a ce wai mahaifinsu Balarabe ne Musulmi daga garin Bagadaza.