Majalisar Dattawan Amurka ta soke dokar shiga yaƙi

Majalisar dattawan Amurka ta kaɗa kuri'ar sauya dokar da ta bai wa ƙasar damar kai wa Iraqi hari a 1992 da kuma a 2003, yaƙe-yaƙen da a yanzu yawanci aka ce kuskure ne.

Waɗanda suka goyi bayan matakin, daga jam'iyyar Democrat da kuma wasu 'yan Republican sun ce yin hakan ya zama dole domin hana shugabannin ƙasar na gaba amfani da ikonsu ta hanyar da ba ta kamata ba, wajen jefa ƙasar cikin yaƙi.

Sanatoci sittin da shida ne suka goyi bayan sauyin yayin da talatin suka ƙi.

A ƙarƙashin tsarin mulkin Amurka, majalisar dokokin ƙasar ce kawai take da ikon ayyana shigar ƙasar yaki.

To amma a ƙarƙashin wannan doka da ta bada damar amfani da ƙarfin soji shugabannin Amurka kan fake, su kai hari ko ƙaddamar da yaƙi a kan wata ƙasa ba tare da amincewar majalisar dokokin ba.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Chuck Schumer, ɗan Democrat ya ce idan wannan doka ta ci gaba da kasancewa, to wata gwamnati a nan gaba za ta iya amfani da ita, ta hanyar da ba ta dace ba, ta jefa Amurka cikin wani rikicin musamman a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kuma kafin kaɗa ƙuri’ar, jagoran 'yan Democrat ɗin a majalisar dattawan ya yi bayani kan dalilin da ya sa yake ganin sauya dokar, abu ne da ya dace.

Ya ce, "Amurka da Iraqi, da ma duniya baki ɗaya sun sauya sosai tun daga 2002, kuma lokaci ya yi da dokokin da ke kundaye, su dace da waɗannan sauye-sauye.''

''Waɗannan dokoki sun wuce lokacinsu. Waɗannan sauye-sauye ba za su cutar da sojojinmu da ke ƙasashen waje ba, ba kuma za su yi tarnaƙi ko hana tabbatar da tsaron lafiyar Amurkawa ba,’’ in ji Sanata Schumer.

Ya ƙara da cewa: ''A kowacce shekara muna barin waɗannan dokoki a cikin littattafai ko kundaye, akwai damar da wata gwamnati a nan gaba za ta iya amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.''

''Ikon zuwa yaƙi na hannun majalisar dokoki ne saboda haka nauyi ya rataya a wuyanmu, mu hana shugabannin ƙasa na gaba yin amfani da waɗannan dokoki, su jefa mu cikin wani sabon rikici a Gabas ta Tsakiya,'' in ji shi.

Sai dai wasu ‘yan majalisar dattawan na jam’iyyar Republican sun kafe cewa har yanzu akwai buƙatar dokokin, saboda suna bai wa fadar gwamnatin Amurka dama ta mayar da martani ga duk wata barazana a faɗin duniya cikin gaggawa.

Ɗaya daga cikin masu wannan ra'ayi, wanda jigo ne a cikin sanatoci ƴan Republican Jim Risch, ya ce sauya dokar zai iya aika saƙon cewa Amurka tana raunana matsayarta a kan Gabas ta Tsakiya.

Dubban ƴan Iraqi ne da kuma sojojin Amurka suka rasu a yaƙin 2003.

Tsohon shugaban Amurka George W Bush, wanda ya yi iƙirarin cewa Saddam Hussain ya mallaki makaman ƙare dangi, shi ne ya ayyana shiga yaƙin.

Tare da cikakken goyon bayan firaministan Birtaniya na lokacin, Tony Blair.

Yanzu dai mataki na gaba shi ne a miƙa ƙudurin ga majalisar wakilai don ita ma ta kaɗa ƙuri'a a kai.