Kano Pillars ta dakatar da Abdallah mako uku

Asalin hoton, Kano Pillars
Mahukuntan Kano Pillars sun bayar da sanarwar dakatar da koci, Usman Abdallah mako uku, sakamakon rashin kokarin ƙungiyar a bayan nan a bana.
A wata sanarwa da aka fitar daga jami'in ƴaɗa labaran ƙungiyar Ismail Abba Tangalash ta ce kociyan ya nuna halin rashin da'a, bayan tashi ba ci a wasa da Bayelsa ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano.
Pillars ta kasa hawa kan ganiya a ƴan wasannin bayan nan, wadda ta yi nasara ɗaya daga karawa uku a gasar ta Premier Najeriya.
Hakan ne ya sa shakku ga mahukuntan Pillars da magoya baya kan rashin kokarin ƙungiyar da abinda hakan zai haifar.
Bayan tashi daga karawa da Bayelsa a wasan mako na 24 ranar Lahadi, mahukuntan sun ce ba za su lamunci rashin da'a daga Usman ba da ya yi wa magoya bayanta, hakan ya sa aka ɗauki mataki a kansa.
Tuni aka bai wa Ahmed Yaro-Yaro aikin riƙon kwarya, inda Abubakar Musa da Gambo Muhammad da Suleiman Shu'aibu da kuma Ayuba Musa za su taimaka masa.
Kano Pillars za ta je Remo Stars a wasan gaba na mako na 24 a babbar gasar tamaula ta Najeriya.






