Bukatunmu kan gyaran dokar zaɓen Najeriya - El-Rufai

Lokacin karatu: Minti 2

Gyara ga dokar zabe na ci gaba da tayar da ƙura a Najeriya, inda yan'adawa suka ce tilas ne majalisar dattawan ƙasar ta amince da amfani da na'ura wajen aika sakamakon zabe nan take ta intanet.

Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai kuma jigo a jam'iyyar hamayya ta ADC, ya ce suna son a amince da dokar zaɓen da Majalisar Wakilai ta amince.

Amincewa da gyaran dokar zaɓen da majalisar dattawan Najeriya ta yi ne ya haifar da cecekuce a Najeriya musamman kan cire sashen da ke wajabta tura sakamakon zaɓe nan take ta na'ura.

Yan'adawa da ƙungiyoyin farar huka sun soki majalisar dattawan Najeriya da ƙin amincewa da gyaran sashen da zai tilasta aika sakamakon zaɓe ta na'ura.

"Tura sakamako ta na'ura dole ne a dawo da shi, kuma dole ne a ce hukumar zaɓe ta yi aiki da shi."

"Kuma lokacin da aka bayar na zaɓe a duba a rage shi domin ya yi yawa kuma yana wahalar da jam'iyyu da ƴantakara," in ji Malam Nasir El-Rufai.

Ya ƙara da cewa akwai gyare-gyare da dama da ƴanmajalisar wakilai suka yi da ma wasu da ƴamajalisar dattawa suka saka a dokar da ya kamata a ƙara.

A ranar Talata ne majalisar dattawa ta ce za ta yi zaman gaggawa, inda batun gyaran da ta yi wa dokar zaɓe ne ake sa ran za ta sake dibawa.

A ranar Larabar da ta gabata ne Majalisar dattawan ta sanar da tafiya hutu na tsawon mako biyu bayan ta amince da gyara ga dokar zaɓe.

Sai dai sanarwar da majalisar ta fitar ranar Lahadi, ba ta bayyana dalilin kiran gaggawan da ta yi wa ƴanmajalisar ba, amma ana tunanin ba ya rasa nasaba da ƙurar da ta taso bayan amincewa da dokar zaɓen da aka yi wa gyara.

Babbar ƙungiyar ƙwadago ta NLC da wasu ƙungiyoyin farar hula a Najeriya sun yi barazanar jagorantar zanga-zanga da ƙaurace wa zaɓen sakamakon ruɗanin da ke ya biyo baya kan gyaran dokar zaɓe, musamman rashin tabbas kan amincewa da tura sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da na'ura.