Mene ne tsarin tsugunarwa na E1 da ke barazana ga kafa ƙasar Falasɗinawa?

Asalin hoton, Reuters
Tsare-tsaren shirin tsugunar da Falasɗinawa mai cike da cece-kuce wanda ministan kudi na Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Bezalel Smotrich ya ce zai binne batun samar da ƙasar Falasɗinu, ya janyo gagarumar suka.
Tsarin mai suna E1 na gina gidaje 3,401 a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tsakanin gabashin Ƙudus da Maale Adumin - batu ne da aka jingine tsawon shekaru sakamakon sukar da aka yi a kai.
Galibin ƙasashen duniya na ganin matsugunan ba sa bisa tsari a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa duk da cewa Isra'ila ta musanta hakan.
A makon da ya gabata, Smotrich ya goyi bayan tsarin inda ya kira matakin "nasara ce a tarihi".
Ma'aikatar harkokin wajen Falasɗinu ta kira tsarin "wani yanayi na ƙarara faɗaɗ laifukan kisan kiyashi da ɗaiɗaita mutane da kuma mamaye yanki" - zarge-zargen da Isra'ila ta daɗe tana musantawa.
Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai da ƙasashe da dama kamar Birtaniya da Turkiyya duk sun soki ƙudirin na E1 inda suka nemi da a dakatar da shi.
Mene ne tsarin tsugunarwa na E1?

Asalin hoton, Reuters
Batun tsugunarwa na ɗaya daga cikin batutuwan da ke yawan janyo taƙaddama tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.
Tsarin tsugunarwa na E1, wanda aka fara bijiro da shi a shekarun 1990 a ƙarƙashin Yitzhak Rabin, ya soma ne da batun samar da gidaje 2,500.
A 2004, ta faɗaɗa zuwa kusan rukunin gidaje 4,000 tare da cibiyoyin kasuwanci da kuma wuraren yawon buɗe ido.
Tsakanin 2009 da 2020, an sanar da wasu sabbin matakan, ciki har da ƙwace filaye da batun tsara taswirar gida da kuma gina titi.
Sai dai shawarwarin ba sa samun karɓuwa a duk lokacin da aka gabatar da su saboda matsin lamba daga ƙasashen duniya.
Me ya sa ake taƙaddama a kai?

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gina yankin E1 abu ne da aka daɗe ana ganin yana haifar da naƙasu ga batun samar da ƙasar Falasɗinu.
Hakan na faruwa saboda muhimmancin wajen tsugunarwar na E1: ya raba yankunan kudancin Ƙudus daga waɗanda suke arewacinsa kuma zai kare samar da iyaka a yankin Falasɗinawa da ta haɗa Ramallah, kudancin Ƙudus da Bethlehem.
A cewar wata ƙungiyar Isra'ila mai fafutukar samar da zaman lafiya mai suna Peace Now, wadda ke sa ido kan batun tsugunarwar a Gaɓar Yamma, sabbin rukunin gidajen za su kasance ƙarin kashi 33 cikin 100 na girman yankin Maale Adumim, wanda a yanzu yake da yawan al'umma kusa 38,000.
Shirin zai haɗa unguwanni zuwa ga yankunan masana'antu kuma hakan zai bayar da kafar faɗaɗa ikon Isra'ila a yankuna da dama na Gaɓar Yamma, a cewar Peace Now.
Ƙungiyar ta ce a ranar Laraba mai zuwa ne kwamitin ƙwararru zai zauna kan neman amincewar ƙarshe ga batun tsarin tsugunarwar na E1 wanda tun asali ya yi watsi da duka ƙorafe-ƙorafen da aka yi kan shawarar.
Mene ne Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye?

Asalin hoton, Reuters
Gaɓar Yamma shi ne filin da ke tsakanin Isra'ila da kogin Jordan kuma gida ne ga Falasɗinawa da aka ƙiyasta sun kai miliyan uku.
Wani ɓangare ne na abin da aka fi sani da yankunan Falasɗinawa da aka mamaye wanda ya haɗa da Gabashin Ƙudus da Gaza.
Akwai matsugunan Isra'ilawa kusan 160, da ke ɗauke da Yahudawa 700,000 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Ƙudus.
Falasɗinawa sun daɗe suna sukar kasantuwar Isra'ila a waɗannan yankunan.
Har yanzu Isra'ila ce ke da iko da Gaɓar Yamma amma tun shekarun 1990, wata gwamnatin Falasɗinawa - da ake kira hukumar Falasɗinawa - ce take tafiyar da garuruwan da biranen.
Tun bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga Oktoban 2023, matsin lambar Isra'ila kan Falasɗinawan da ke Gaɓar Yamma ya ƙaru wanda take karewa a matsayin matakan tsaro.
A watan Yuni, Majalisar Ɗinkin Duniya ta samu bayanan adadi mafi girma na Falasɗinawa da suka ji rauni cikin sama da shekara biyu - inda ta bayyana cewa Falasɗinawa 100 ne Isra'ilawa ƴan kama wuri zauna suka raunata.
A tsukin watanni shida na farkon bana, Majalisar Ɗinkin Duniya ta samu bayanan hare-haren ƴan kama wuri zauna 757 wanda ya janyo mutuwar Falasɗinawa da kuma lalata dukiya - ƙarin kashi 13 cikin 100 na abin da aka gani a irin wannan lokacin a 2024.
Falasɗinawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun zargi sojojin Isra'ila da gazawa wajen kare Falasɗinawa da kuma al'ummarsu - ba wai kawai yin burus da hare-haren ba amma har da sa hannu, a cewar wani rahoto daga ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch da aka fitar a 2024.
Isra'ila ta yi iƙirari cewa tarukan Geneva da suka haramta tsugunarwa a yankunan da aka mamaye ba su shafi haka ba - wani hange da ƙasashe da dama cikin ƙawayenta da kuma lauyoyin ƙasa da ƙasa suka ga baike.
Falasɗinawa na son a rushe duka matsugunan Yahudawa saboda yadda suke kallon Gaɓar Yamma a matsayin ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta a nan gaba.
Sai dai gwamnatin Isra'ila ba ta amince da ikon Falasɗinawa su samu ƙasarsu ba inda ta ce Gaɓar Yamma wani ɓangare ne na Isra'ila.
A Yulin 2024, babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya, ICJ ta ce ci gaba da kasancewar Isra'ila a yankunan Falasɗinawa da aka mamaye ya saɓa doka inda ta ce ya kamata Isra'ila ta kwashe ƴan kama wuri zauna ɗin.
Daga cikin hukuncin da ta yanke shi ne, takunkumin da Isra'ila ta ƙaƙabawa Falasɗinawa a yankunan da aka mamaye daidai suke da nuna wariya saboda addini da ƙabila."
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce kotun ta ɗauki mataki na karairayi.

Asalin hoton, Reuters
Yaya duniya ke kallon tsarin tsugunarwa na E1?
Bayan sanar da ƙudirin, Smotritch ya yaba wa Shugaba Donald Trump da jakada Mike Huckabee bisa goyon bayansu, inda ya jaddada cewa, a ganinsa, yankin Gaɓar Yamma ba zai taɓa rabuwa da Is'ra'ila ba."
Ya kuma ce Firaiminista Benjamin Netanyahu yana goyon bayan tsarin don kawo sabbin mutane miliyan guda zuwa Gaɓar Yamma.
Ma'aikatar harkokin wajen Falasɗinu ta yi allahawadai da tsarin na E1 inda ta kira shi hari kan haɗin kan yankin Falasɗinawa kuma koma-baya ga yiwuwar kafa wata ƙasa.
A martanin da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi game da tsarin an E1, samar da tsaro a Gaɓar Yamma zai tabbatar da tsaron Isra'ila kuma hakan ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin nan na samar da zaman lafiya a yankin."
Sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai sun buƙaci Isra'ila da kada ta aiwatar da tsarin.
Majalisar Ɗinoin Duniya ta ce gine-gine a yankin E1 zai raba arewaci da kudancin Gaɓar Yamma, "hakan kuma zai zama maƙarƙashiya ga batun samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinawa."
Kaja Kallas, babbar jami'ar harkokin waje ta Tarayyar Turai ta ce tsarin tsugunarwar na E1 "zai ƙara taɓarɓara mafitar samar da ƙasa biyu yayin da hakan kuma ke zama keta dokar ƙasa da ƙasa."
Ministan harkokin wajen Birtaniya, David Lammy ya yi watsi da ƙudirin inda ya ce zai raba ƙasar Falasɗinawa da ake shirin sanarwa a gaba gida biyu kuma hakan ya saɓa da dokokin ƙasa da ƙasa."
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ita ma ta soki matakin da ta ce bai girmama dokokin ƙasa da ƙasa ba kuma ya ci karo da ikon kafa ƙasar Falasɗinu.
Masar ta kira shirin a matsayin take dokokin ƙasa da ƙasa tsagwaronsa da kuma shawarwarin tsaro da aka cimma.
Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Jordan ta soki shirin da ta bayyana a matsayin cin zarafi kan ikon Falasɗinawa na kafa ƴantacciyar ƙasa mai cin gashin kanta bisa ƙudirin iyakoki na ranar 4 ga Yunin 1967, yayin da Gabashin Ƙudus zai zama babban birni."
Sanar da tsarin E1 ya zo ne jim kaɗan bayan da ƙasashe da dama kamar Faransa da Canada suka ce sun shirya amincewa da ƙasar Falasɗinu nan gaba a wannan shekarar.
Zuwa yanzu galibin ƙasashe - 147 na mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya su 193 - sun amince da ƙasar Falasɗinu a hukumance.
Firaministan Birtaniya Sir Keir Starmer ya ce Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu a Satumba idan Isra'ila ta amince da wasu ƙa'idoji ciki har da amincewa ta tsagaita wuta a Gaza da kuma farfaɗo da yiwuwar samar da maslahar ƙasa biyu.
Bayan sanar da tsarin sabbin matsugunan na E1 ne Smotrich ya ce "babu wata ƙasa da za a amince da kafawa|.
"Duk wanda ke ƙoƙarin amincewa da ƙasar Falasɗinu a yau zai samu amsarmu nan take. Ba wai da wasu takardu ko matakai ko sanarwa ba, amma da hujjoji. Hujjoji kan gidaje da hujjoji kan maƙwabtaka," ya ƙara da cewa.
Waɗanda suka ba da gudunmawa wajen haɗa rahoton: Alla Daraghme da Muhannad Tutanji daga sashen Larabci na BBC.







