Tungar yaƙin Taliban a Afghanistan na farfaɗowa bayan shekara 20

- Marubuci, Yama Bariz
- Aiko rahoto daga, Sangin, Afghanistan
- Lokacin karatu: Minti 4
Zaune a cikin ɗakinsa, Abdul Sattar ya ɗaga yatsunsa uku na hannun dama. Muryarsa na rawa lokacin da yake lissafa sunayen 'ya'yansa da suka mutu.
"Watan Karima uku kacal da haihuwa," in ji shi. "Kamila na da wata tara, Zainullah wata bakwai, Obaidullah wata huɗu..."
Manomin da ke ƙauyen Sangin na lardin Helmand, Abdul ya bayar da labarin wani hari ta sama da ya kashe mutum 18 daga cikin danginsa.
"Mayaƙan Taliban sun yi sahu a kusa gidajenmu, su kuma dakarun ƙasashen waje suna tsallake daga gabas," a cewarsa.
Saboda gudun tsira da rayuwarsu, Abdul ya kwashe iyalansa zuwa wani ƙauye da ke kusa. Amma yaƙin ya bi su inda suke saboda tsananinsa.
"Makamai masu linzami biyu ne suka faɗa kan gidan da iyalina suke fakewa. Mutum 35 aka kashe a daren - 18 daga cikinsu dangina ne. Akasarinsu yara ne da mata."
Abdul ya yi imanin cewa ɗaya daga cikin sansanonin dakarun ƙasashen waje ne ya harbo makaman, duk da cewa ba a tabbatar da hakan ba.
Lamarin ya faru a 2010, amma da Abdul ya fara bayar da labarin sai abin ya zama kamar jiya ya faru.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Waɗannan ƙaburburan nasu ne kaɗai abin da ya rage masa nasu.
"Ko hotonsu ba ni da shi. Babu abin da ya tsira," in ji Abdul yana hawaye.
"Ba zan taɓa manta abin da ya faru ba. Ko kaji 17 ka yi asara sai ranka ya ɓaci. Dangina 18 aka raba ni da su a rana ɗaya. To wane irin ɓacin rai kake tunanin ina ciki?"
Kusan duk wani mazaunin Sangin ya rasa ɗan'uwansa. Tsawon shekara 2020 har zuwa 2021, gundumar na cikin wuraren da aka fi zubar da jini a Afghanistan sakamakon yaƙin da Taliban ke yi da sojojin ƙawance na Nato da kuma dakarun gwamnatin ƙasar.
Sama da 100 na sojojin Birtaniya 457 da aka kashe ne suka mutu a gundumar.
Abdul ya shafe shekaru yana neman a bi masa haƙƙinsa. Ya tuntuɓi tsohuwar gwamnatin ƙasar, da kuma Taliban daga baya bayan sun koma kan mulki.
Ya nuna min wata wasiƙa da tsohuwar gwamnati ta aika masa tana yi masa tayin kuɗin Afghanis 100,000 - dala 2,000 kenan - kan kowane mutum ɗaya. Amma bai amince ba.
"Ba ni da wani ƙarfi," a cewarsa. "Da zan iya kotu zan kai su, ta Shari'a ko kuma ta majistare. Akwia mutumin da zai iya jure irin wannan rashin adalcin?"

Da kyar ake ƙyale 'yanjaridar ƙasashen waje shiga lardin na Sangin tun da Taliban ta koma kan mulki a 2021. Na je domin na ga yadda rayuwa take a ƙarƙashin mulkinsu kusan shekara huɗu.
Titin zuwa Sangin daga Lashkar Gah babban birnin yankin na da haɗari sosai a baya, inda aka cika shi da ababen fashewa, dakarun ƙasashen waje a ko'ina, da kuma yawan hare-haren Taliban.
Yanzu ababen hawa na wucewa ba tare da matsala ba.

Muna ƙoƙarin ɗaukar fim ɗinmu, sai wani direba ya ce mu kashe kyamarar ya ba mu labari.
"Hankali ya tashi a lokacin nan. Ba mu iya yawo. Dakarun Taliban da na ƙasashen waje sun saka mu a tsakiya. Suna neman ƙwace Sangin, amma kuma mu ne muke shan wuya."

Har yanzu ana ganin lalacewar da lardin ya yi tun daga farkon garin.
Amma kuma akwai alamun an fara samun mafita. Babbar kasuwar Sangin da aka rusa gaba ɗaya ta farfaɗo yanzu.
Tun bayan fara sake gina ta a 2022, shaguna sun fara mamaye kasuwar masu sayar da kayayyaki iri-iri. A ranakun kasuwa da take ci sau biyu a mako, mutane na zuwa daga ƙauyuka masu nisa.

Sangin ya kasance wurin noman ganyen tabar wiwi, wanda ta mamaye tattalin arzikin yankin. A lokacin yaƙin, Taliban ta samu kuɗi sosai da cinikisa. Amma a watan Afrilun 2022, sun haramta nomansa, abin da ya jawo wa manoma matsala.
Su ma asibitoci da makarantu sun ci gaba da aikinsu, sai dai ban da yara mata.
Taliban ta dawo da kwanciyar hankali amma kuma ba da sauƙi ba.
Da na tambayi jami'in Taliban a Helmand saƙon da yake ɗauke da shi ga iyalan da suka rasa 'yan'uwansu a Sangin, ciki har da na hare-haren Taliban ɗin kanta, ya ba da amsa ba da wani ɗar ba.
"Abin da ya faru a nan mun yi ne a yaƙin neman 'yanci. Ba abu ne da gangan ba. Duk wani mataki yana da nasa tasirin. Duk wanda ke neman yi mana mulkin mallaka, zai fuskanci irin wannan martanin," in ji Maulavi Qasim Riaz.
"Sangin kamar wata tungarmu ce ta yaƙi mai tsarki. Cibiyar jihadi ce."
Sai dai mazauna yankin ba haka suke kallon lamarin ba - wurin gwagwarmaya ne, da tarihi, da kuma tsira da rai.
Yanzu da yake ƙarƙashin ikon Taliban, mutane na fatan zaman lafiya. Amma kuma rashin tabbas na nan a zukata - musamman game da tattalin arziki, da 'yancinsu, da kuma abin da zai faru nan gaba.











