'Talge muka riƙa sha da azumin bara a hannun maharan jirgin ƙasan Kaduna'

Kaduna train hostages

Asalin hoton, OTHER

Karyewar jari da damfara da miyagun mafarke-mafarke, shan talgen tuwo da gurɓataccen ruwa da kuma murnar shaƙar iskar 'yanci daga bisani, su ne abubuwan da har yanzu ke cikin zukatan wasu fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da 'yan Boko Haram suka sace, shekara ɗaya da ta wuce.

Ɗaya daga cikin fasinjojin 64, Mukhtar Bala Mohammed ya ce bai taɓa zaton zai kuɓuta ya koma cikin iyalinsa da rayuwa ba.

"Har yanzu idan na ji ƙarar jirgi, sai na firgita, na ruga da gudu," in ji shi.

Mummunan hari ne da ya yi matuƙar tada hankalin Najeriya da dugunzuma 'yan ƙasar tun bayan sace 'yan matan Chibok a 2014 da jerin satar gomman ɗalibai 'yan sakandire a jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna.

Da maryacen ranar Litinin ne 28 ga watan Maris ɗin 2022, gungun 'yan bindiga suka kai wa jirgin ƙasan da su Mukhtar ke ciki hari, yana tsakiyar tafiya a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Wani babban al'amari ne da ya canza rayuwar ɗan kasuwar, mai harkar man fetur gaba ɗaya.

Kaduna train attack

Asalin hoton, NRC

Bayanan hoto, Wani tarago kenan na jirgin ƙasan da aka kai wa hare-haren bam a bara

Hukumomi tun a wancan lokaci sun tabbatar da cewa 'yan Boko Haram ne suka kai harin tare da sace gomman fasinjojin jirgin. A cewar Mukhtar Bala sai da ya shafe tsawon kwana 197 cikin dokar daji a hannun masu garkuwar.

'Talge muka riƙa sha idan mun kai azumi'

Wani babban abu da ya fi bijiro masa a rai yanzu lokacin azumin Ramadan, shi ne yadda suka riƙa shan ruwa bara, idan sun kai azumi da talgen tuwo.

"Talgen tuwo ne za a zuba mana a cikin ɗan ƙaramin kofi. Sai ɗan ƙosai haka tsalli" in ji Mukhtari. "Ka gan ni nan, wallahi ko azumi ɗaya ban sha ba. Duk da yake a cikinmu akwai waɗanda suka sha azumi kamar biyu zuwa uku saboda wahala".

Ya ce yana farin ciki da ya kuɓuta, inda a yanzu yake iya shan ruwa bayan ya kai azumi da nau'in abincin da yake so a cikin iyali.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce "'yan ta'addan da suka kai harin sun karkatar da jirgin ƙasan daga kan hanyarsa da ƙarfe 7 na maryace bayan sun ɗana abin fashewar da ya tarwatsa wani ɓangare na kwangiri. Daga nan kuma suka buɗe wa taragonnin jirgin wuta, kafin sace fasinjojin da ke ciki".

Sanarwar da gwamnatin ta fitar don cika shekara ɗaya da kai mummunan hari, ta ce daga bisani an tabbatar da kashe fasinja tara a lokacin, sai waɗanda aka sace fiye da sittin, baya ga mutum 20 da suka ji raunuka.

Mukhtar Bala Mohammed, magidanci ɗan shekara 43, ya ce maharan da farko sun kwashe su ne zuwa ɗan wani tudu, inda suka yi jiran fiye da tsawon sa'a ɗaya, kafin su ɗauke su zuwa cikin daji, kuma suka shafe kimanin sa'a biyar suna tafiya.

Ya ce sun yi rayuwa cikin tsoro da ƙunci da barazana, kuma sun ga rashin ƙauna a tsawon kusan wata bakwai da suka yi a daji.

"Don gaskiya akwai alamun duk a gun za mu halaka.... Ga wasu abubuwa da ke zuwa daga cikin gari, da ke nuna mana rashin ƙauna. Ko shi ma ya sa duk mun sadaƙar a hannunsu za mu mutu. Ga yawan barazanar cewa za a yanka mu. Suna cewa mu mushirikai ne da sauransu," a cewar Mukhtar.

Wani lokaci in ji shi, sukan zo, su yi ta yi musu shaguɓe, suna cewa idan mallam ya ce a fara yanka ku, ta kan wane da wane, za a fara.

'Harkokinmu duk sun durƙushe'

Mukhtar Bala ya ce ya yi imani 'yan Boko Haram ne suka sace su kamar yadda gwamnati ta shaida tun lokacin da ake tsare da su a cikin daji. A cewarsa: "Yan Boko Haram ne suka haɗu da wani ɓangare na 'yan ta'addan daji, kuma suka musuluntar da su".

Ya ce yana cikin sahun ƙarshe na fasinjojin da suka kuɓuta daga hannun maharan ta hanyar wani kwamitin shiga tsakani da hukumomin Najeriya suka kafa don ganin an kuɓutar da duk fasinjojin da aka yi garkuwa da su lafiya.

A cewarsa, bayan ya dawo gida ne ya taras an sayar da kadarorin da ya mallaka a ƙoƙarin iyali da dangi na ganin an haɗa kuɗaɗen da za a karɓo shi.

"Rayuwa a yanzu ta yi min wahala saboda kusan duk harkokina sun tsaya. Jarina ya karye. Ga shi kuma duk an damfari iyalanmu," in ji Mukhtar.

Ya ce akwai gida da ya mallaka bayan tsawon lokaci yana tanadi don ya tare da iyalinsa gaba ɗaya, amma bayan ya kuɓuta sai ya taras an sayar da gidan don a karɓo shi.

Haka zalika, harkarsa ta dillancin man fetur ma a yanzu ta durƙushe.

Kaduna train hostage

Asalin hoton, Mukhtar Bala

Bayanan hoto, Mukhtar Bala ya ce ya yi asarar wata kwangila ta maƙudan kuɗi da aka so bai wa ƙungiyarsa kafin aukuwar harin

"Ina zuwa asibiti don kula da lafiyata amma saboda yawan shan magani da ƙarancin kuɗi, sun sa na daina zuwa. Matata har yanzu ta kasa sabawa da halin da nake ciki na firgici da tashin hankali.'

Kullum yana zuwa asibiti kuma yana shan in ji Mukhar Bala, amma ba ya ganin sauƙi. Wasu ƙuraje masu kama da ƙyazbi duk sun fito masa a kai, ga tsananin ciwon kai da yakan yi fama da shi.

Kuma "Ga mantuwa, sannan abu kaɗan ne zai ruɗa ni, kuma abu kaɗan zan ji ya fusata ni".

Ya ce rayuwa a yanzu ta kasance mai matuƙar wahala a gare su. Duk da yake, yana samun tallafi daga abokan arziƙi.

Kaduna train hostage

Asalin hoton, Mukhtar Bala

Bayanan hoto, Yadda Mukhtar Bala ya canza kwana biyu bayan kuɓutar sa daga hannun masu garkuwar jirgin ƙasa

Gwamnatin Kaduna dai ta ce shekara ɗaya bayan aukuwar harin a yankin Kasarami-Audu Jangom cikin ƙaramar hukumar Chikun, har yanzu akwai fasinjojin da ba su je sun karɓi jakunkunansu ba.

Da take sake miƙa saƙon jajentawa ga fasinjojin da iyalansu, gwamnatin Kaduna ta ce bayan bincike da aikin ceto, dakarun tsaro a bara, sun gano jakunkunan fasinjoji da dama kuma sun damƙa su hannunta.

Daga bisani dangi ko iyalan fasinjojin jirgin ƙasan 62 sun je sun karɓi jaka 94 ƙunshe muhimman takardu da fasfuna da mukullan mota da na gida da kuɗi da katunan cirar kuɗi da wayoyin salula da kwamfyutocin tafi-da-gidanka da litattafai da turarurruka da tufafi da kuma sarƙoƙi da 'yan kunne.

Sai dai har yanzu akwai sauran jakunkuna guda 16 da ba a je an karɓa ba ƙunshe da kayayyaki kamar dardumomi da litattafai da kuma tufafi.

Ga fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da aka sace kamar Mukhtar Bala, babban abin da suka ce sun fi so a yanzu, ba tsofaffin kayansu ba ne da akasari ba sa buƙata, sai dai ƙwaƙƙwaran tallafi don inganta lafiyarsu da kuma sake gina rayuwarsu da ta durƙushe.