'Za a fuskanci babban bala'i idan ba a kawo karshen dauke wuta ba'

Karfe 10 na dare ta dan gota a birnin Harare na kasar Zimbabwe, babu abin da kake gani saboda tsananin duhu.
Can daga nesa ina iya jiyo hira da shewar wasu mutane da ke gaban wata karamar masana'anta, da ke yankin masana'antu da ake kira Willowvale Industrial Park.
Mazan sanye suke da riga mai hade da wando, sun kunna wutar itace, ga kuma hasken farin wuta a sararin samaniya, zaman dakon dawo da wutar lantarki su ke yi domin samun damar yin aiki na 'yan sa'o'i kalilan kafin a sake dauke ta.
Dauke wutar lantarki ba wani bakon lamari ne ga 'yan Zimbabwe ba, hasali inda sabo sun saba har ya game jiki.
"Babu wani tsayayyen lokaci da za a ce za'a dawo da wutar lantarkin, - jiya sai 10 muka samu wuta, amma ka ga yau lamarin ba haka ya ke ba," in ji George Sadziwa a hirarsa da BBC, lokacin da ya ke kewaya injinan da ba za su taba aiki ba sai dole da wutar lantarki.
Kamfaninsa mai suna Geosad Engineering, ya samu kwantiragin surfen hatsi da nika, amma saboda rashin wutar lantarki, ga karancin man fetur da iskar gas, babban tashin hankalinsa shi ne, ba zai iya kammla aikin akan lokaci ba.
"Kasuwancinmu na tsananin bukatar wutar lantarki… jami'an gwamnati dai na ba mu tabbacin nan ba da jimawa ba lamura za su daidaita. Matukar aka ci gaba da tafiya a haka, tabbas za mu shiga babban bala'i."

An samu tabbacin ba lokacin samun wutar lantrkin, bayan kiran daya daga cikin jami'an hukumar raba lantarki ta wayar tarho. An kuma shaidawa Mista Sadziwa, ya sanya rai da samun wutar daga karfe 11 na dare har zuwa wayewar gari.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mista Sadziwa, ya shaida min yawancin 'yan kasuwa aminansa sun fara aikin dare. Lamarin ba anan ya tsaya ba domin 'yan kasar Zimbabwe na ji a jikinsu.
Dole su tashi tsakar dare, domin gugar tufafinsu, da amfanin kayan laturoni, da kallon kwankwan gasar kwallon kafar duniya da ke gudana a kasar Qatar.
Cikin shekaru 10, Zimbabwe ta kashe kusan dala biliyan 2 saboda wutar lantarki. Amma har yanzu kasar bata cimma nasara ba, hasali ma kar tabarbarewa lamarin ya yi.
Lamarin ya munana cikin kwanaki 4, bayan hukumomin madatsar ruwa na kogin Zambezi, suka bukaci cibiyar lantarki ta Kariba su dakatar da komai, sakamakon yadda ruwan kogin da ke samar da lantarkin ya yi kasa, wnda hakan babbar barazana ce.
Kwararru sun ce kamata ya yi cibiyar wutar lantarkin kasar ta ba da lantarkin yadda ya dace, to amma dadewar da injinan suka yi da rashin gyara ya janyo su na yawan dakatar da aiki.
Hakan ya tilastawa hukumomi samar da lantarkin ta amfani da kogin Kariba, un kuma kusan karar da ruwan da ake adanawa na kar ta kwana . Matsanancin fari da aka fuskanta shi ma ya haddasa karin matsalar rashin ruwan.
A yawanzu Zimbabwe na samar da megawat 600MW na wutar lantarkin a kowacce rana, ya yin da bin da kasar ke bukata a kowacce rana ya kasance megawat 2,000MW.

Asalin hoton, Getty Images
An amince Zimbabwe ta ci gaba da amfani da madatsar ruwa ta Kariba, domin samar da megawat 300 a kowacce rana, kamar yadda shugabar ma'aikatar makamashi a kasar Gloria Magombo ta shaida wa BBC.
Hukumar da ke kula da kogin, za ta sake nazarin yawan ruwan da ak da shi a watan Junairu, sakamakon fatan da ake da shi na samun damuna mai albarka.
Mutanen karkara sun fi kowa shan wuya
A wani sako da aka wallafa a shafin intanet a Zimbabwe, ya nuna yadda mutne za su goge tufafinu ba tare da amfani da lantarki ba, an nuna yadda aka dora tukunyar da ke dauke da ruwan zafi kan tufafin domin mikar da su.
Mutane na cikin damuwa. A wajen birnin Mbare cibiyar kasuwancin Zimbabwe, akwi iyalai matalauta da ke fama da rayuwa.
Misali kamar Wella Chidziva mai shekara 43, ta na kokarin iza wutar itace domin dumama dan abincin da za a ci kafin duhun dare ya kunno kai da kuma zubar ruwan sama.
Ta tattara tarkacen robobin da ta samu akan tituna, da shi ta ke amfani domin hada wutar itace, gas ya zama sai mai ido da kwalli ke amfani da shi.
Makonni biyu da suk gbta, Mis Chidziva ta dkatar da sida kaji saboda rashin wutar lantrki, ta kuma yi asrar kaji 30 da suk rube a cikin firinjinta.
Akan samu wutar lntarki da tsakar dare, wani lokacin sai 4 na asuba, wani lokaci ba ma a kawo ta baki daya. Ta shaidawa BBC iyalai uku ke rayuwa a gidan daya, kum kullum sai sun yi fada akan itacen girki.
"A yanzu mu na karba-karba ne a wurin girkin, daga baya muka kasafta wurin gida uku kowacce ta kama na ta bangaren,'' ta kuma nuna min inda suke yin girkin can a bayan gidan.
"Daidai ya ke da rahin lantarkin, saboda ko an kawo da tsakar dare, yara duk sun yi bacci. A yanzu da lokacin bikin Kirsimeti ke karawo, ban san yadda za mu karke ba."

Zimbabwe ta kashe dala biliyan biyu, ta zuba jarin dala miliyan 533 a kamfanin makamahi na China mai suna Sinohydro, domin kara adadin lantarkin da kogin Kariba ke samarwa da karin megawat 300.
Bayan wannan ta kara zuba dala miliyan daya da miliyan 400 domin samar da sabon sashen tattra lantarkin a Hwange Thermal, domin kara addin megawat 600 da ke samrwa a kowacce rana.
Sai dai aikin na Hwange ya fuskanci matsala sakamakon barkewar annobar korona.
"Ba mu zuba jari a lokacin da ya kamata ba," in ji Victor Utedzi, kwararre kan makamashi.
Shi ya samar da kamfanin Centragrid mai samar da lantarki ta amfani da hasken rana, tafiyar kilomita 30 daga birnin Harare, ya na samar da megawat 2.5, a yanzu ya na kokarin fadawa zuwa megawat 25.
"Babu takamaimai sassaukar hanyar samarwa ko magance matsalar wutar lntarki da ake fma da ita a Zimbabwe," a hirarsa da BBC.
"Idan kana son samar da karamar cibiyar lantarki ta amfani da haske rana, ka na bukatar akalla shekara 3 zuwa 4 kafin tabbata.
Sannan ka na buktar shekara 10 kafin samar da kudin da za ka yi aikin da su.

Asalin hoton, Shingai Nyoka
Zimbabwe na shirin kara karfin lantarki da megawat 500, ta amfani da makoftanta Zozambique da Zambia.
Amma hakan ba ta yiwu ba sakamakon tashe-tashen hankalin da ake yi a yankin Kudancin Afirka, ga kuma su ma fama da rashin isasshiyar lantarkin.
''Masu zuba jari ba su da tabbatacin kudinsu za su fito, dan haka komai da taka tsantsan suke yi,'' in ji Mista Utedzi.
Ya kara da cewa na bukatar samar da wasu tsare-tsare da za u ja hankalin masu zuba jari a ciki da wajen nhiyar Afirka.
Gwamnati dai ta yi amnna matsalar ta wucin gadi ce, da fatan samar da megawt 3,500 dga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.
Amma yanzu ta ce za a ci gaba da kokarin samar da lantarkin daga cibiyar Hwange, kuma kafin karshen shekara komai zai didaita.
Za kuma a kara fadada aiki da fatan ganin kogin Kariba ya samu isasshen ruwan da zai kara megawat din da ya ke samarwa.
Yayin da ya kasance babu ranar da matsalar lantarkin za ta kare a Zimbabwe, mutane kamar Wella Chidziva na fatan za a dawo da lantarkin albarkacin bukuwan Kirsimati da ke tafe.











