Real Madrid ta kai wasan karshe na Super Cup na Sifaniya

Asalin hoton, OTHERS
Real Madrid ta doke Valencia a bugun fanareti a wasan kusa da karshe na cin kofin Zakaran-zakaru na Sifaniya wato Spanish Super Cup, a karawar da aka yi a filin wasa na Sarki Fahd da ke babban birnin Saudi Arabia, Riyadh.
Karim Benzema ne ya fara daga raga da bugun fanareti a lokacin wasan inda zakarun na Turai da kuma La Liga suka kasance a gaba.
Sai dai kuma Samuel Lino ya farke kwallon jim kadan da komawa fili daga hutun rabin lokaci, wasan ya kasance 1-1.
Hakan ne ya sa aka tafi bugun fanareti a karshen wasan inda Madrid ta yi nasara da ci 4-3, inda ta ci dukkanin bugunta, yayin da Eray Comert ya barar da tashi, kuma mai tsaron raga Thibaut Courtois ya tare ta Jose Gaya.
Bayan wasan Courtois ya yi bayani kan yadda ya samu nasarar taka wa Valencia birki a bugun na fanareti.
Ya ce, ‘’ba shakka dole ne a matsayinka na mai tsaron raga ka yi nazari a kan fanareti.’’
‘’Gaya ya barar da bugun da ya yi na karshe a wasansu da Sevilla ta hannun hagu, sannan ya ci bugunsa na karshe ta tsakiya a karawarsu da Betis, to ka ga mun san nan zai nemi ya sake bugawa,’’ In ji Courtois.
A ranar Alhamis din nan ne Real Betis za ta kara da Barcelona a daya wasan na kusa da karshe na gasar ta Spanish Super Cup, kuma duk wadda ta yi nasara za ta hadu da Real Madrid a wasan karshe a birnin na Riyadh na Saudiyya.










