Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Batun hana shan barasa a gasar cin kofin duniya
"Abin tir da Allah-wadai," a cewar magoyin-bayan Ecuador, Jose kan batun haramta shan giya a filin wasa, yayin da yake komawa gida daga kallon ƙwallo.
"Na sayo wannan wanda babu giya a cikinsa, amma babu laifi ina iya jin gardin sinadarai."
"Kashi 100" a cewar Emilioa. "Akwai mutanen da ke ihu a ba su giya."
Shawarar karshe da aka yanke na haramta sayar da giya a filin wasa a Qatar ya kasance zance na baya-bayan nan da ya haifar da ce-ce-ku-ce a hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa.
Muhawarar da ake tafkawa kan daukar nauyi ya samo asali ne tun wasannin baya da ake zargin hukumar da sa son rai da fifita kudi sama da lafiyar magoya-baya.
Tsarin fifa na haramci
Duk da cewa matsalar Fifa kan giya shi ne kokarin tursasa wa Qatar ta ba da dama, suna ganin rashin shan giya na iya sa filin wasan ya kasance babu karsashi.
Har zuwa shekara ta 2014, kundin dokokinta kan taruka ya haramta sayar da giya a cikin fili, sannan duk mutumin da aka samu na shan giya a filin za a fitar da shi.
Sai dai matakin turasasawa da hukumomi suka yi na sake nazari kan wannan tsari da matsawa kan sayar da giya a filin gasar cin kofin duniya, ya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen da ke daukar nauyin wasanni.
Kawo karshen haramci kan Brazil
Bai wa Brazil damar shirya gasar cin kofin duniya, sai faɗuwa ta zo daidai da zama.
Kasar da sau biyar tana lashe gasar, giya abu ne da ya yi fice sosai a kasar.
Amma kamar sauran kasashe, soyayyar da 'yan Brazil ke yi wa ƙwallo a wasu lokaci na rikiɗewa zuwa tarzoma.
Sakamakon haka, an haramta shan giya a lokacin wasanni a Brazil a 2003, a wani ɓangare na matakan da ake ɗauka don hana dabanci ko kazamin rikici tsakanin magoya-baya a filin wasa.
Amma da haɗin-gwiwar tsawon lokaci tsakanin Fifa da kamfanin giyar Budweiser kan wasanni, an umarci masu daukar nauyin gasar cewa "dole su sauya dokar".
"Shan giya na cikin tsarin gasar cin kofin duniya na Fifa, don haka dole a sha giya.
"Ku gafarce ni idan kalamaina sun kasance marasa ɗa'a amma wannan abu ne da babu batun zaman sassantawa," a cewar shugaban Fifa a wancan lokaci, Jerome Valcke.
"Tun da muna da damar sayar da giya dole batun ya zama cikin doka."
Ministan lafiya a Brazil ya nuna adawarsa da sauyin kuma Marco Aurelio Garcia, mataimaki na musamman ga shugaban kasar, ya bayyana Vackle, a matsayin mara ɗa’a.
Duk da zanga-zangar 2014, masu daukar nauyin gasar sun sauya dokar domin bada damar sayar da giya a lokacin wasanni.
A lokacin gasar an yi ta samun tashin hankali tsakanin magoya-baya, ciki har da wasa tsakanin Colombia da Uruguay a Rio de Janeiro.
A lokacin mayar da martani, Valcke ya faɗawa kafar talabijin Brazil na wasanni cewa: "Na sha mamaki ganin adadin mutane da suka yi tilis da barasa."
Da aka tambaye shi ko Fifa za ta sauya tsarinta nan gaba, sai ya ce: "Idan mun ga bukatar takaita hakan za mu yi."
Matsi a kan Rasha
Amma a gasar cin kofin duniya na 2018 a Rasha ba a ga wasu sauye-sauye da Fifa ta yi ba.
Kamar dai a Brazil, Rasha tana da wasu daɗaɗɗun dokoki kan takaita shan giya a wasu muhimman wuraren wasanni.
A 2005, gwamnati ta haramta sayar da giya da tallata ta a fillin wasa.
A 2014 lokacin wasanni Olympics na hunturu a Sochi, babu wani kamfanin giya da ya ɗau nauyi, a 2012 kuma Rasha ta bijiro da haramcin doka kan tallata barasa a talabijin da shafukan intanet da kofofin yaɗa labarai.
Amma shekara da ta kama, Shugaba Vladimir Putin ya sanya hannu kan sabuwar doka da ke amincewa da sayar da giya a lokacin wasanni cin kofin duniya da kuma dage haramci tallata giya na dan wani lokaci.
Yankin Rostov ya yi kokarin haramta sayar da giya a filayen wasanisu, amma hakan ya fuskanci cikas saboda barazanar daukar matakan shari’a.
Batun addini
Maganar giya da ƙwallon tamaula a manyan wasanni ba wai batu ne na Fifa da gasar cin kofin duniya ba ga kasashe.
A gasar Euro 2022, Uefa tayi rikici da 'yan wasa da suka ƙi halartar taron manema labarai ɗauke da kwalaben giya a ɗaya daga cikin wasanni da Heineken ta ɗau nauyi.
Dan wasan Faransa, Paul Pogba ya kawar da kwalbar giya a gabansa kafin amsa tambayoyi.
Shi ma Karim Benzema, wanda Musulmi ne kamar Pogba, shi ma ya ki yarda ya yi magana sai da ya dauke kwalbar giya.
Duk da cewa giyar da Heineken ya daura a kan tebura ba wai mai karfi ba ce ko zallar giya, 'yan wasan sun nuna nesanta kansu daga tallata ta.
Daga baya Uefa ta bijiro da tsarin soma neman izinin masu horarwa da 'yan wasa kafin ɗaura musu barasa a kan teburi a taron manema labarai, amma tana mai gargadi za a iya cin tarar kungiyar da ke nuna kauracewa karara.
Haramcin Qatar
A gasar cin kofin 2022, haramci bisa addinin kasar da ke daukar nauyin gasar – da ta tsaurara matakan hana sayar da giya a faɗin kasar- ya tilasta wa Fifa amincewa da sharuɗan hana sayar da giya a filin wasanni a mataki karshe.
Sai dai masu riƙe da katin manyan baki, na iya sayan giyar a cikin wani akwati na alfarma, kafin wasa da lokacin wasa da kuma bayan wasa.
Yadda hakan zai shafi alaƙa tsakanin Fifa da kamfanin giya na Budweiser da sauransu har yanzu abu ne da ba a fayyace ba.
Wani babban wasa da aka gudanar a 1980, ana cewa sun biya kuɗi har dala miliyan 75 a gasar cin kofin duniya.
Koda ya ke a Amurka babu mamaki a ga sauyi gani cewa tana cikin kasashe uku da ke son daukar nauyin gasar cin kofin 2026.