Kane na tunanin komawa Barcelona, Man United da Tottenham na neman Branthwaite

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaba na Bayern Munich Harry Kane na da farashin Yuro miliyan 65 wanda zai fara aiki a bazara mai zuwa kuma ɗan wasan na Ingila mai shekara 32 yana nazarin zaɓin da ya ke da shi wanda ya haɗa da ci gaba da zama a Jamus ko kuma komawa Barcelona. (Sport)
Manchester United da Tottenham na sa ido kan ɗan wasan bayan Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 23, wanda Everton ta ƙaƙabawa farashin fam miliyan 70. (Caught Offside).
Tottenham da Chelsea na shirin yin hamayya kan ɗan wasan gaban Porto ɗan ƙasar Sifaniya Samu Aghehowa, mai shekara 21, wanda ke ɗauke da farashin Yuro miliyan 80. (Correio da Manha)
Arsenal da Barcelona suna zawarcin kyaftin ɗin tawagar Faransa na ƴan ƙasa da shekara 16 Lacine Megnan-Pave bayan ɗan wasan mai shekara 15 ya ci ƙwallaye 15 sannan ya taimaka aka zura 12 a wasanni 24 da ya bugawa ƙungiyar Montpellier ta ƴan ƙasa da shekara 17. (Sport)
Babban jami'in zaƙulo ƴan wasa na Liverpool Barry Hunter ya kasance a filin wasan Craven Cottage ranar Asabar don kallon ɗan wasan Fulham Kevin mai shekara 22 wanda ke ɗauke da farashin fam miliyan 35 (Football Insider)
Kocin Bournemouth Andoni Iraola shi ne kan gaba a jerin waɗanda Athletic Club za ta yi zawarci idan har Ernesto Valverde bai sabunta kwantiraginsa ba a bazara mai zuwa. (La Razon)
Daraktan wasanni na Bayern Munich Max Eberl ya ce ƙungiyar za ta yi duk abin da za ta iya don ganin ɗan wasan bayan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 27, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa a kulob ɗin. (Sky Sports Germany)
Ɗan wasan baya na Switzerland Manuel Akanji, mai shekara 30, ya ce Inter Milan ce ke da zaɓin mayar da zaman aronsa daga Manchester City zuwa na dindindin, kuma alamu sun nuna cewa ƙungiyar ɗin ta Serie A ta gamsu da hazaƙar da ya nuna a halin yanzu. (Football Italia).
Tsohon ɗan wasan tsakiya na Italiya da Roma Daniele de Rossi na cikin waɗanda za su iya maye gurbin Patrick Vieira bayan da aka kore shi a matsayin kocin Genoa. (La Gazzetta dello Sport )










