Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arzikin Ɗangote ya ninka zuwa dala biliyan 28 bayan fara aikin matatar mansa
Hamshaƙin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote ya samu ƙaruwar arziki, inda dukiyarsa ta ninku a sanadiyar fara aikin matatar mansa.
Yanzu arzikin attajirin ya ninku zuwa dala biliyan 27.8, kamar yadda rahoton mujallar 'Bloomberg Billionaire Index' - mai nazarin masu arziki na duniya - ya nuna.
Matatar man ta Ɗangote, wadda aka buɗe a jihar Legas da ke kudancin Najeriya, ita ce irinta na farko, wadda ke iya tace kusan kowane nau'in ɗanyan mai.
Matatar za ta iya kawo gagarumin sauyi a ɓangaren tattalin arzikin Najeriya, ta hanyar mayar da ƙasar mai dogaro da kanta a ɓangaren man fetur.
Game da ƙalubalen da ya fuskanta wajen gina matatar, Dangote ya ce ba zai yi wa ko da babban maƙiyinsa fatan shiga irin damuwar ba.
''Ban san muna gina wani abu ba ne da zai zo ya dame mu," in ji Ɗangote mai shekara 67 a wata ziyara da ya kai New York.
"Matsalolin sun zo daga ɓangarori da dama, mutane da yawa suna ta ruɗar da mu cewa ba za mu iya ba, kuma ko da mun yi ɗin, ba za mu samu nasara ba," kamar yadda kafar Bloomberg ta ruwaito.
Tun bayan da matatar ta fara aiki a watan Janairu, an samu saɓani daban-daban tsakaninta da gwamnati da kuma kamfanin man fetur na ƙasar, da kuma amfaninta ga ƴan ƙasa da ma tasirinsa ga muhalli.
A wajen Dangote - wanda ya fara zama biloniya da kasuwancin siminti - buɗe matatar man wani gagarumin aiki ne a rayuwarsa.
Gina matatar ya ɗauki shekara 11, ta kuma ci dala biliyan 20, kuma mafi yawancin aikin, shi ya ɗauki nauyinsa.
Yanayin kasuwancin Dangote
Ɗangote, wanda ya fara furfura yanzu saboda shekaru, hamshaƙin ɗankasuwa ne.
Asalin kasuwancinsa na kayayyakin masarufi ne, yawanci siminti ne da sukari da gishiri da fulawa.
Arzikinsa abin ban mamaki ne kasancewar a ƙasar da yake, kashi 40 na mutanenta suna rayuwa ne cikin talauci, kuma yawancin arzikin ƙasar a man fetur ne.
Sai dai masu sukar Ɗangote suna ganin nasararsa na da alaƙa da ƴansiyasa, kuma yana amfani da damar wajen yin kaka-gida a harkokin kasuwanci, amma shi yana alfahari da gudunmuwar da ya bayar wajen ciyar da ɓangaren masana'antun Najeriya gaba.
Sai dai a ɓangaren buɗe matatar man, ya shiga matsaloli.
An ƙwace asalin wurin da ya so ya buɗe matatar, bayan ya sha fama da rikice-rikice da ƴan ƙauyen.
Daga baya sai ya koma kudancin jihar Legas, inda can ma ya fuskanci wasu ƙalubalen da mutane.
Bayan an ba shi sabon filin, sai ya kasance kwari ne, inda dole ya yi aikin yashewa sannan ya yi ciko na kusan ƙafa biyar (mita 1.5) domin kiyaye aukuwar ambaliya. Kamfanin ya gina dam da tashar jirgin ruwa domin aikin matatar.
Shekara biyu bayan fara ginin, sai annobar korona ta ɓarke.
Wasu daga cikin kamfanonin da suke kawo masa kayayyaki sai suka samu matsalar kuɗi, suka dakata.
Sannan a wani ɓangaren kuma, Ɗangote yana biyan dala miliyan 50 zuwa dala miliyan 60 duk shekara a matsayin kuɗin ruwa na bashin dala biliyan 5.5 da ya karɓa daga bankunan cikin gida.
Amma bayan buɗe matatar a bana, dole ta fara neman ɗanyen mai daga ƙasashen Turai, wanda wannan ya ƙara masa tsada.
A yawancin harkokin kasuwancinsa, Ɗangote yana samun alaƙa mai kyau da shugabannin Najeriya, wanda hakan ke taimakon harkokinsa.
Sai dai bai samu wannan ba da shugaban Najeriya na yanzu, Bola Tinubu ba.
A watan Janairu, hukumar EFCC ta kai samame ofishin kamfanin Ɗangote a cikin binciken da take yi a kan harƙallar harkokin kuɗaɗen ƙasashen waje.
Samamen da rukunin kamfanonin Ɗangote ya ayyana da "cin fuska,"
Kakakin gwamnatin Najeriya bai ce komai ba a game da batun.
Rashin alaƙa mai kyau ɗin ya ƙaru ne bayan Ɗangote ya fito ya fara magantuwa.
A wajen wani taro, Ɗangote ya kwatanta ''mafiyoyin ɓangaren mai da mafiyoyin miyagun ƙwayoyi''.
Kuma bai ɓoye rashin jituwar da ke tsakaninsa da babban kamfanin mai na Najeriya NNPC ba, wato kamfanin man ƙasar wanda zai taimaka masa wajen samun ɗanyen mai da zai riƙa tacewa.
Domin ya daɗaɗa musu, sai ya shiga yarjejeniya da kamfanin a shekarar 2021 da kamfanin domin ya sayar musu da kashi 20 na matatar a kan farashin dala biliyan 13.8. Sai dai hakan bai yiwu ba, sai suka koma sayen kashi 7.2.
"Harkar mai harka ce da take cike da ɓoye-ɓoye, kuma cike take da masu rashawa."
Kakakin NNPC bai ce komai ba a game da wannan.
Ɗangote wanda bai cika magana ba, sai kwatsam ya fara magantuwa, wanda hakan ya ƙara fito da batun matatar waje, kamar yadda Zainab Usman, wata masaniyar tattalin arziki da siyasa kuma darakta a cibiyar Africa Program at the Carnegie Endowment for International Peace ta bayyana.
"Ya kashe dala biliyan 20 domin gina matatar ce saboda ya taimaka wa ƙasar, amma akwai gungun ƴansiyasar da suke ganin matatar tana barazana ga wasu harkokinsu, kuma suke so su masa zagon ƙasa," in ji ta.
"Yadda ya fito ya magantu a kan lamarin ya ƙara jawo masa girma da mutunci."
Barin baya mai kyau
A yanzu, cigaba ririta arziki a kowane irin mataki a Najeriya na da wahalar gaske.
Darajar kuɗin Najeriya wato naira ya karye da kusan ninki biyu da rabi a kan dala tun bayan da Tinubu ya ɗage takunkumin harkokin canjin kuɗaɗen waje.
Dangote ya ce kashi 80 na kasuwancinsa da dala ake amfani.
Ya ce a baɗi kamfaninsa zai zama wanda ya fi kowa samar da daloli a Najeriya, ƙasar da take fama da ƙarancin kuɗin na Amurka.
Yadda Ɗangote yake son Najeriya a zahiri yake. A gidansa na Legas yake zaune kusan shekara 34.
Amma zai buɗe wani ofis a Dubai domin faɗaɗa kasuwancinsa a ƙarƙashin kulawar ƴarsa Halima wadda ta koma can da zama kwanan nan.
Yana da wata gidauniya da ke bayar da tallafin miliyoyin daloli duk shekara, amma kuma zai ƙara kuɗaɗen da yake kashewa domin tallafin.
Ya ce ya fara shirin komawa baya a harkokin kasuwancin domin ƴaƴansa su cigaba, ciki har da jikansa wanda zai kammala jami'a a baɗi.
Ya ce ƴaƴansa mata sun yi girma ma a yanzu, idan aka kwatanta da lokacin da ya fara sayen jirgin samansa na farko wato shekara 23, da kuma lokacin da ya gina da katafaren gidansa wato shekara 33.
Wahalar da ya fuskanta wajen gina matatar man ta sa ya fara cire rai da faɗaɗa kasuwancin, amma ya ce yana alfahari da aikin.
"Ina jin daɗi da alfahari domin na bar abun da za a riƙa tunawa da ni, musamman a Afirka," in ji shi, "Na sa ƙasata da ma nahiyata sun wadata da abun da ba su taɓa tunani ba."