Mece ce makomar Hezbollah bayan illar da aka yi mata?

Mazauna kudancin Lebanon cikin jerin gwanon motoci riƙe da tutocin Hezbollah yayin da suke komawa ƙauyensu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mazauna kudancin Lebanon cikin jerin gwanon motoci riƙe da tutocin Hezbollah yayin da suke komawa ƙauyensu
    • Marubuci, Hugo Bachega
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 6

A ranar 26 ga watan Janairu, dubban ƴan Lebanon da ke zaune a wasu sassan ƙasar, bayan guje wa gidajensu, suka fara ƙoƙarin komawa gidajensu a kudancin ƙasar.

Sun riƙa tafiya cikin jerin gwanon motoci, inda suke riƙe da tutar Hezbolla mai launin ruwan ɗorawa tare da rera waƙoƙi.

Da dama ba su da inda za su zaune, bayan yaƙin da aka kwashe fiye da shekara guda ana yi a yankin.

Sun yi alhinin waɗanda suka mutu, a cikin baraguzan gine-ginen da suka ruguje, tare da sanya allunan tunawa da tsohon shugaban ƙungiyar, Hassan Nasrallah da aka kashe.

Ranar ta kawo ƙarshen wa'adin janye sojojin Isra'ila daga yankin, wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka da Faransa suka jagoranci ƙullawa, wadda ta buƙaci Hezbullah ta kawar da makamanta da mayaƙanta daga kudancin ƙasar.

Yarjejeniyar ta kuma buƙaci a jibge dubban sojojin Lebanon a yankin.

Sai dai Isra'ila ta ce Lebanon ba ta cika sharuɗan yarjejeniyar ba, don haka, ba duka sojojin da suka yi mamayar ne suka fice ba. Ita ma Lebanon ta zargi Isra'ila da jinkirta aiwatar da yarjejeniyar.

Ba abin mamaki ba ne, an samu tashin hankali. A wasu yankunan sojojin Isra'ila sun buɗe wuta tare da kashe mutane 24 ciki har da wani sojan Lebanon.

Ga ƙungiyar Hizbullah, wadda ita ce ke da karfi a kudancin Lebanon tsawon shekaru da dama, tashin hankalin wata dama ce ta gwada ƙarfinta, bayan da ta sha fama da rikici da Isra'ila.

Amma shin ƙungiyar za ta iya tsira daga guguwar sauye-sauye a Lebanon, da sake fasalin iko a Gabas ta Tsakiya?

Damar raunana gwamnati

Shugaban Lebanon, Joseph Aoun yayin taron manema labarai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan da ya gabata majalisar dokokin Lebanon ta zaɓi tsohon shugaban sojin ƙasar, Joseph Aoun a matsayin sabon shugaban ƙasar.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cikin shekaru da dama Hezbollah - wadda ƙungiyar Shi'a ce ta masu ɗauke da makamai, kuma ta siyasa - ta tabbatar da matsayinta na ƙungiya mafi ƙarfi a Lebanon.

Da taimakon Iran, ta gina rundunar soji mai ƙarfi fiye da na ƙasar Lebanon.

Ƙasancewarta ƙungiya mai ƙarfi a majalisar dokokin ƙasar na nufin cewa babu wani babban mataki da za a ɗauka ba tae da amincewarta ba yayin da tsarin siyasar ƙasar ya ba ta wakilci a cikin gwamnati.

A takaice dai, Hezbollah na da damar raunata gwamnatin Lebanon - kuma a lokuta da dama ta yi hakan.

Rikicin baya-bayan nan ya ɓarke ne a watan Oktoban 2023, yayin da Hezbollah ta buɗe fagen yaƙin na biyu a kan Isra'ila, bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza a matsayin martani ga hare-haren Hamas.

Rikicin ya yi ƙamari a watan Satumban bara, yayin da Isra'ila ta ratsa ƙungiyar ta hanyoyin da ba za a iya misalta su ba.

Na farko, ƙaddamar da hari kan na'urorin sadarwar da wayoyin oba-oba da mambobin ƙungiyar ke amfani da su.

Hare-hare ta sama babau ƙaƙƙautawa da kuma mamayar kudancin ƙasar ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 4,000 ciki har da fararen hula da dama, ya bar yankunan da mabiya mazhabar Shi'a - waɗanda su ne mafi yawan goyon bayan ƙungiyar Hezbollah - sun zama kango, tare da yin mummunar ɓarna a sansanin mayaƙan ƙungiyar.

An kashe da yawa cikin jagororinta, musamman Nasrallah, wanda ya shafe sama da shekara 30 yana jan ragamar ƙungiyar.

Magajinsa, tsohon mataimakinsa, Naim Qassem, wanda ba mai farin jini ko kwarjini ba ne, ya amince cewa ƙungiyar ta fuskanci mummunar asara.

Yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki cikin watan Nuwamba, tamkar miƙa wuya ƙungiyar ta yi, wadda Birtaniya da Amurka da wasu ƙasashe ke kallo a matsayin ƙungiyar ta'addanci.

Mazauna gari cikin jerin gwanon motoci riƙe da tutar ƙungiyar da kuma hotunan tsohon shugaban ƙungiyar Hassan Nasrallah da aka kashe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hezbollah, ƙungiyar mabiya Shia mai ɗauke da makamai ta kasance ƙungiyar siyasa mai ƙarfi a Lebanon.

A cikin wannan sabuwar yarjejeniyar ta watan da ya gabata, majalisar dokokin ƙasar Lebanon ta zaɓi sabon shugaban ƙasa - wanda tsohon hafsan sojin ƙasar ne, Joseph Aoun, wanda Amurka ke goyon bayansa, bayan ya shafe sama da shekara biyu babu jituwa da ƙungiyar Hezbollah.

An raunana, ƙungiyar ba za ta iya hana ɗaukar wasu matakan gwamnati ba kamar yadda ta yi a baya, a wata alama da ke nuna raguwar matsayinta.

Aoun ya naɗa Nawaf Salam, wanda ke riƙe da muƙamin shugaban Kotun Duniya ta ICJ, wanda kuma ba zai yi alaƙa da ƙungiyar ba, a matsayin firaministan ƙasar.

Hezbollah, a halin yanzu, da alama tana mayar da hankali kan wani ɓangaren, musamman sake gina sansanoninta.

Ƙungiyar ta shaida wa mabiyanta cewa rashin nasarar da ta yi a yaƙin nasara ce a gareta, amma a zahiri ba haka ba ne. An lalata yankunan da take da ƙarfi, kuma Bankin Duniya ya ƙiyasta cewa asarar da ƙungiyar ta yi ya haura dala biliyan uku.

Hoton wani yanki da aka lalata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hare-haren Isra'ila ta sama da mamayar kudancin Lebanon ya kashe fiye da mutum tare da ruguza yankin.

A ƙasar da ke fama da durƙushewar tattalin arziki, babu wanda ya san wanda zai taimaka masa a ƙasar, kamar yadda taimakon ƙasashen duniya suka shata wa gwamnatin ƙasar sharuɗan ɗaukar matakan da za su dakile ƙarfin ƙungiyar Hezbollah.

Kungiyar ta biya diyya ga wasu iyalai, kamar yadda ta yi bayan yakin 2006, amma tuni alamu suka nuna rashin gamsuwa.

"Idan har yanzu mutane suka zauna a cikin tantuna nan da wata shida, ko kuma cikin ɓaraguzan gidajensu, za su iya fara ɗora alhaki kan ƙungiyar Hizbullah maimakon gwamnati ko Isra'ila.

Wannan shi ne dalilin da ya sa suke ba da gudummawa sosai a yanzu don ƙoƙarin kauce wa hakan, "in ji Nicholas Blanford, babban jami'in wata ƙungiyar mai ayyuka a yankin Gabas ta tsakiya kuma mai fashin baƙi.

'Barazana a fakaice'

Amma duk wani mataki da aka ɗauka kan Hezbollah ka iya zama mai kasada.

A ranar 26 ga watan Janairu, sa'o'i bayan sun yi ƙoƙarin komawa komawa kudancin ƙasar, wasu matasa a kan babura sun bi ta yankunan da ba na ƴan Shi'a ba a birnin Beirut da sauran wurare da daddare, suna ta ihu tare da ɗaga tutocin Hizbullah.

Mazauna wasu yankunan sun yi yunƙurin tunkararsu. A ƙasar da rarrabuwar kawuna ta yi katutu, kuma da yawa har yanzu suna tunawa da yaƙin basasar 1975-1990, ana kallon ayarin motocin a matsayin wata dabara ta tsoratarwa.

Mista Blanford ya ce Hezbollah na da "barazanar tayar da hankali a fakaice" saboda ƙarfin sojinta. "Idan ka matsa su da karfi, za zsu mayar da martani,'' kamar yadda ya

Wani jami'in diflomasiyyar ƙasashen Yammacin, wanda ya nemi a sakaya sunansa domin tattaunawar sirri, ya shaida cewa: "Mun jima muna gaya wa abokan hamayyar ƙungiyar da kuma wasu ƙasashe cewa ''idan ka taɓa Hezbollah, to tabbas za ta mayar da martani, kuma akwai hadarin samun tashin hankali.''

Wani matshi tseye a gaban babban hoton tsohon shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah, da aka kafa jikin wani gini da aka ruguza.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kashe da dama cikin jagororin Hezbollah, ciki har da Nasrallah, wanda ya jagoranceta na fiye da shekara 30

An yanzu da aka buɗe sabon babi a Labanon - ƙasar da cin hanci da rashawa suka yi katutu - rashin gudanar da ayyukan gwamnati da tashe-tashen hankula da ake gani marasa adadi ka iya haifar da rashin ayyukan gina ƙasa.

A yayin da yake jawabinsa na farko ga majalisar dokokin ƙasar, Aoun ya alƙawarta kawo sauye-sauye da aka dade ana jiran gani, yana mai cewa matsawar da a aiwatar da gagarumin sauyi ba, babu yadda za a iya ceto ƙasardaga durƙushewa.

Ya sha alwashin sake gina cibiyoyin gwamnati, da farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, sannan da mayar da sojojin Lebanon su zama su kaɗai ne masu ɗaukar makamai a ƙasar.

Aoun bai ambaci sunan Hezbollah ba, amma abin da yake nufi kenan. Zauren ya jinjina masa, yayin da ƴan majalisar Hezbollah suka yi shiru.

Shugaban Lebanon, Joseph Aoun tare da firaministan ƙasar, Nawaf Salam.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Lebanon, Joseph Aoun tare da firaministan ƙasar, Nawaf Salam.

Sabbin shugabannin Lebanon na fuskantar matsin lambar ɗaukar matakan gaggawa.

Kawayen ƙasar na ƙetare na ganin sake fasalin iko a yankin Gabas ta Tsakiya wata dama ce ta raunana iko dda tasirin Iran a Labanon.

"Abin da kawai muke buƙata shi ne samun kwanciyar hankali a ƙasar,'' kamar yadda wani mazaunin ƙasar da ke yankin Kiristoci a Beirut ya bayyana. Wannan kuwa shi ne fatan kusan kowane ɗan ƙasar.

Har ma magoya bayan Hezbollah na aza ayar tambaya game da rawar da ta taka.

Duk da cewa da kamar wuya Hezbollah ta koma yadda take a baya, to amma ba za ta iya ajiye makamai ba.