Yarjejeniyar zaman lafiyar DR Congo da Rwanda ta janyo saɓanin ra'ayi

Mayaƙan M23 a cikin motan a jamhuriyar dimokuradiyyar Congo a ranar 7 ga watan Afirelun 2025

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rwanda ta musanta cewa tana goyon bayan mayaƙan M23 a gabasin jamhuriyar dimokuradiyyar Congo.
    • Marubuci, Paul Njie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Goma
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin jamhuriyar dimokuraɗiyyar Congo da ta Rwanda a birnin Washington ya janyo ra'ayoyi mabanbanta , inda tsohin shugaban Congo, Joseph Kabbila ya bayyana shi a matsayin ''Wani abu da bai wuce yarjejniyar kasuwanci ba''.

Ƴarjejeniyar da aka ƙulla a ranar Juma'a ta buƙaci a rushe duk ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai gabashin Congo, da karɓar makamansu, da sake shigar da su cikin al'umma, duk da cewa babu cikakken bayani a game da yadda tsarin zai zama.

Yayin da mutanen irin su Kabila ke sukar matakin, akwai wasu masu yaba wa batun, kuma suna ganin cewa hanya ce ta magance rikicin da ya shafe shekaru yana janyo koma baya.

Rwanda ta musanta zargin cewa tana goyon bayan ƙungiyar M23 wadda ta shafe shekaru tana faɗa a jamhuroyar dimokuraɗiyyar Congo.

A farkon shekarar nan mayaƙan M23 suka ƙwace iko a mafi yawan gabashin jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ciki harda hedikwatar yankin wato birnin Goma da birnin Bukavu da kuma filayen jirgin sama biyu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe dubban mutane kuma an tilastawa wasu dubub dubatan fararen hula barin muhallinsu, bayan hare-haren da ƴan tawaye suka ƙadamar a kwanan nan. Myaƙan M23 sun ƙaryata ƙididdigar, suna cewa ƙasa da mutane dubu ɗaya ne suka mutu.

Bayan mayaƙan sun ƙwace iko a wasu sassan ƙasar, gwamnatin jamhuriyar dimokuraɗiyyar Congo ta karkata ga Amurka domin neman taimako a fannin tabbatar da tsaro.

Daga ɓangaren ta, rahotanni sun ce jamhuriyar za ta bai wa Amurka damar amfana da ma'adinan ƙasar,

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wani saƙo da ya wallaa a shafinsa na X bayan sanya hannu a yarjejeniyar a ranar Juma'a Kabila ya bayyana shakku a kan mutanen da suka halarci taron sanya hannun, yana mai cewa jamhuriyar dimokuradiyyar Congo ba ta yaƙi da mutanen da suka bayyana a hoton da aka ɗauka wajen sanya hannun, ciki harda shugaban Amurka Donald Trump da sauran jami'ansa da kuma ministan harkokin wajen Rwanda.

Babu dai tabbacin ko tsokacin nasa wata suka ce a kan rashin gayyatar wakilan mayaƙan M23 a zaman na Washington.

Kabila ya ce "Dole mu daina canza bayanai, mu kuma daina yaɗa farfaganda," ya ƙara da cewa "Gaskiyar lamari jama'ar Congo ke son ji, ba wai nuna dabarun diflomasiyya ba''.

A birnin Goma na gabashin Congo, inda mayaƙan ke riƙe da ƙarfin iko ma an lura da rashin halartar M23 a yarjejeniyar.

"Ta ya za su ce suna ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya amma ba su gayyaci M23 ba?'' in ji wani mazanin birnin. Ya kuma bayyana fatan an gayyaci mayaƙan kafin ƙulla yarjejeniyar.

Wani mazaunin garin kuma wanda ke sana'ar acaɓa ya shaidawa BBC cewa ''Mutane sun gaji, ba su damu da zancen tattaunawa ba, abin da suka fi so shi ne zaman laiya.''

Ya hakiƙace cewa tattaunawa ta baya da aka yi ba ta samu goyon bayan ɓangarorin da ke jayayya ba, lamarin da ya janyo tababa a kan nasarar ta.

Haka nan kuma, Sam Zarifi, shugaban ƙungiyar Physicians for Human Rights (PHR), wata ƙungiya mai gudanar da ayyukan jin ƙai a jamhuriyar dimokuraɗiyyar Congo a tsawon shekaru, ya ce akwai giɓi a yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta jagoranta.

"Ba za a samu wanzuwar zaman lafiya ba tare da yi wa kowanne ɓangare adalci ba.'' in ji Mr Zarifi.

Ya ƙara da cewa "Yarjejeniyar ta yi watsi da yiyuwar ci gaba da samun tashin hankali ba ta hanyar amfani da ƙananan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, waɗanda kuma binciken mu ya tabbatar cewa suna da hannu a tashin hankali da dama.''

Stephanie Marungu, shugabar ƙungiyar bayar da agaji a Goma ta bayyana fatan cimma nasarar shirin.

"Sanya hannu a kan yarjejeniyar gagarumar nasara ce kuma za ta kawo zaman lafiya a yankin gabashin ƙasar,'' ta shaida wa BBC cewa ''hakan zai tainaka wajen wanzar da lumana a yankin, ta yadda ƙungiyar za ta samu ikon gabatar da ayyukanta na jin ƙai ga mabuƙata.''

Sai dai ta amsa cewa za a iya fuskantar wasu ƙalubalen wajen aiwatar da yarjejeniyar.

"Idan har wannan yarjejeniya za ta kawo mana zaman lafiya, bamu da wata matsala da hakan,'' in ji wani mazaunin Goma.

Ya dai rage a ga yadda abubuwa za su kasance wajen aiwatar da wannan yarjejeniya a cikin kwanaki masu zuwa.