Sauyin zamani: Ko mata za su koma auren mazan da ba su kai su aji ba?

Mahalarta taro suna taya amarya da ango shagalin bikinsu

Asalin hoton, kkshepel/Getty Images

    • Marubuci, Selin Girit
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Daga tsararren labaran aure irin na su Cinderella da Yarima Charming zuwa na labarin aure haɗi irin na su Elizabeth Bennet da Mr Darcy na littafin Pride and Prejudice Jane Austen, auren wadda ake ganin namiji ya fi mace ne aka fi sabawa da shi a rayuwar yau da kullum. Amma yanzu da mata suka dage wajen samum ilimi mai zurfi da dagewa wajen neman arziki domin tsayawa da ƙafarsu, sai lamarin ya fara canjawa.

"Yanzu haɗa aure a tsakanin matasa yana wahala, saboda akwai mata masu ilimi sosai sama da maza," in ji Nadia Steiber, masaniyar halayyar ɗan'adam a Jami'ar Vienna da ke Austria.

Saboda haka, mata da dama suna neman abokan zama ne masu ilimi irin nasu ko matsayin rayuwa, a lokuta da dama suna ɓigewa ne da auren wanda suka samu kawai ba dole sai yadda suke so ba, lamarin da ta ce ana bayyanawa da "rage aji".

Me ake nufi da wanda ka fi aji?

Idan aka ce auren wanda ka fi aji, ana nufin mace ta aura namiji ko ƙulla soyayya da wanda ta fi aji ko arziki ko ilimi.

A al'adance, akasin hakan ne ya fi zama ruwan dare a tsakanin mata. An fi sabawa da ganin mace ta aura wanda ya fi ta arziki da shekaru kuma ya fi ta ilimi.

An tsara labarin soyayyar Cinderella ne a kan auren ɗaya ya fi ɗaya aji, saboda yadda ajinta da darajarta suka ɗaga bayan aurenta da Yarima Charming

Asalin hoton, Historical Picture Archive

Bayanan hoto, An tsara labarin soyayyar Cinderella ne a kan auren ɗaya ya fi ɗaya aji, saboda yadda ajinta da darajarta suka ɗaga bayan aurenta da Yarima Charming

"A tarihi, maza - waɗanda dole su yi aiki - sun fi samun ilimi sama da mata - waɗanda suka fi mayar da hankali kan koyon aikace-aikacen gida daga iyayensu mata," in ji Catherine Hakim, wani mai bincike ɗan Birtaniya.

"Bambancin shekaru da ilimi tsakanin ma'aurata yana bayar da damar tara iyali, daidaito a ilimi tsakanin mata da maza na cikin abubuwan da ci gaban zamani ya zo da shi," in ji ta.

Yadda alƙaluma suke sauyawa

Alƙaluma da suke fitowa yanzu suna nuna ana samun sauyi. A wani bincike da cibiyar Pew Research Center ta fitar a shekarar 2023, ta gano cewa kashi 24 na mata ma'aurata a Amurka sun fi mazansu ilimi, wanda ƙari ne daga kashi 19 da ake da shi a shekarar 1072.

Binciken ya kuma nuna cewa kashi 29 na ma'aurata, maza da matan suna samun kuɗi daidai da juna. Sannan duk da cewa an fi samun maza suna ɗaukar ɗawainiyar gida, kashi 16 na iyali mata ne suke ɗawainiya da gidan.

Sannan matan da suke samun kuɗi sama da mazansu ya ninku da kusan ninki uku a cikin shekara 50 da suka gabata.

Littafin labarin Pride and Prejudice na Jane Austen wanda daga baya aka mayar da shi fim ya bayyana yadda ake zaman aure a tsakanin wanda ya fi matansa daraja

Asalin hoton, Mark Lawrence/TV Times

Bayanan hoto, Littafin labarin Pride and Prejudice na Jane Austen wanda daga baya aka mayar da shi fim ya bayyana yadda ake zaman aure a tsakanin wanda ya fi matarsa daraja da aji

Irin waɗannan sauye-sauyen da ake samu suna nuna yadda abubuwa suke canjawa game atsarin aure da soyayya.

"A daidai lokacin da wasu mata suke cigaba da neman auren waɗanda suka fi su aji da daraja, wasu da dama yanzu sun fi mayar da hankali kan daidaituwa da girmama juna, sama da ƙarfin aljihu," in ji Michelle Begy, mai dalilin aure a kamfanin Ignite Dating.

"Wannan sauyi ne daga yadda aka saba na mayar da hankali kan muhimmantar da ƙarfin aljihu da aji a baya wajen abokin zama," in ji ta.

Ms Hakim ta ce yanzu ilimi ne ke kan gaba a cikin abubuwan da aka fi lura da su wajen neman aure a turai da arewacin Amurka.

"Kusan rabi, ko kua uku bisa huɗu na masu neman aure sun ce ilimi ya fi muhimmanci," in ji ta.

Abubuwan da aka saba

Duk da cewa ana samun ƙaruwar auren mace ta fi aji a turai, har yanzu auren maza su fi aji da ƙima ya fi yawa a faɗin duniya.

"Littafan addinin Hindu sun bayyana auren tsara, amma al'adar aure da ake krta 'anuloma' wanda namiji ya aura macen da ya fi aji ma da laifi ba ne, amma auren 'pratiloma' inda namiji yake auren macen da ta fi aji haramun ne," in ji Sonalde Desai masaniyar halayyar ɗan'adam a Jami'ar Maryland a Amurka.

Ango da amarya 'yan India

Asalin hoton, MarcoVDM/Getty Images

Bayanan hoto, Har yanzu an fi samun aure tsakanin ma'auratan da aka haɗa a Indiya

Sai dai ta ce yanzu ana samun ƙaruwar yadda mata suke auren maza waɗanda ba su kai su aji ba.

Iran ma wata ƙasa ce da ke da yawan mata da suke kammala karatun jami'a a yankin Gabas ta Tsakiya. Amma duk da haka al'adar namiji ya ɗauki nauyin gida ya fi yawa a ƙasar, wanda hakan ya sa ake yawan samun mata marasa aure saboda suna rasa waɗanda za su aure su saboda "ajinsu."

Wasu mata uku a tsaye

Asalin hoton, Grigorev_Vladimir/Getty Images

Bayanan hoto, Matan Iran na yanzu sun dage kai da fata wajen kawo sauyi a yadda aka saba zamantakewar aure a ƙasar

A China, kalmar "sheng nu" kalma ce ta cin mutunci da take nufin "matan da suka daɗe ba aure", ana amfani da ita ne domin bayyana mata masu ilimi da ba su samu miji ba, sannan a Japan mata suna ƙin aure ko su kashe auren saboda suna zama da ƙafarsu.

Ƙasashe irin su Norway da Sweden su kuma abubuwansu daban ne, saboda suna da dokokin daidaito tsakanin mata da maza masu ƙarfi.

"Yadda ake kallon al'amari ya bambanta daga yanki zuwa yanki," in ji Ms Steiber.

"A kudu duk da mata sun fi ilimi ko da kuwa ba su kai mazan samun kuɗi ba- amma sukan fi mazan daraja a cikin al'umma. Sukan zama suna da ƙarfin faɗa a j a gidansu sama da mazan - alhalin a wasu al'adun wannan da wahala ya yiwu," in ji ta.

Rawar kafofin sadarwa

Duk da raguwar da ake samu, auren namiji ya matar daraja yana tashe a kafofin sadarwa musamman a lokutan bayar da shawarwarin soyayya da aure.

An sha ganin kalma irin "passport bros" a turai inda maza suke neman aure a wasu ƙasashe da za su samu mata masu zaman gida da kuma gangamin "tradwife" da suke fafatukar ba mata shawarar su aura mazan da suka fi su kuɗi duk sun taimaka wajen sake dawo da tsarin auren namiji wanda ya fi mace.

"Waɗannan ƴan fafutikar suna gangami ne domin riƙe al'adu, inda suka fi ba auren namiji wanda ya fi mace ƙarfi muhimmanci, in ji Ms Begy.

Matan da suka fi mazansu arziƙi

Ms Steiber ta ce lokacin da mata suka fi mazan ƙarfin aljihu, mazan suna fuskantar ƙalubale, saboda a cewarta, "yana kawo tsaiko kan darajar namiji da aka saba gani a al'adance."

"Lamari ne na yadda macen za ta iya amincewa da wanda take ganin ta fi ƙarfinsa, d kuma yadda ko namiji zai iya jure zaman aure da wadda ta fi shi ilimi da daraja," in ji ta.

Jerin mata

Asalin hoton, PeopleImages

Bayanan hoto, Duk da cewa ana samun ƙaruwar mata masu digiri, har yanzu mazan sun fi ƙarfin aljihu