Ƴanmajalisar Tarayya biyar da aka taɓa yunƙurin yi wa kiranye a Najeriya

Dino Malaye, da Hon Faruk Adamu Aliyu, da Natahsa Akpoti Uduaghan, da Umar Jibirl na daga cikin 'yanmajalisar Najeriyar da aka taba yi wa kiranye

Asalin hoton, Facebook/Multiple

Lokacin karatu: Minti 5

Hukumar INEC ta ce ta karbi takardun sanya hannu kan batun yi wa sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan kiranye, sai dai ta yi korafin cewar wadanda suka yi koken ba su cika ka'idojin da suka kamata ba.

Mai magana da yawun hukumar ta INEC Hajiya Zainab Aminu ta ce 'masu kiranyen ba su bayar da adireshi, da lambobin waya da lammbar tura sako na email da za a iya tura musu sako ba'.

"Wadanda suka kawo takardar lambar jagoran masu kawo koken ne kadai ce a kan takardar da aka kawo ta kiranyen wadanda kuma kudin tsarin mulkin Najeriya, da dokar zaben Najeriya ta 2022 da tanad- tanaden zaben, duk sun fayyace matakan da suka kamata a ce sun bi wajen yin kiranye' in ji mai magana INEC Zainab Aminu.

Sanata Natasha Akpoti na fuskantar kiranye ne tun bayan taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin ta da shugaban majalisar dattijan Najeriya, Godswill Akpabio, bayan zargin da ta yi masa na yunƙurin cin zarafi na lalata.

Sai dai majalisar dattijan ta zargi Natasha da karya dokokin majalisa ta hanyar ƙin komawa sabuwar kujerar da aka sauya mata, da kuma yin hargowa a majalisa, lamarin da ya kai ga dakatar da ita daga majalisar na tsawon wata shida.

Yanzu haka dai hukumar zaɓen Najeriya ta tabbatar da cewa an kai mata ƙorafin neman yi wa ƴar majalisar kiranye, inda aka tura mata takardu ɗauke da sa hannun rabin masu kaɗa ƙuri'a 474,554 na rumfunan zaɓe 902 da ke mazaɓar ƴar majalisar a ƙananan hukumomin Adavi da Ajaokuta da Ogori/Magongo da Okehi da kuma Okene.

Matakan da ake bi wajen yi wa yanmajalisa kiranye

Hajiya Zainab Aminu ta ce cikin matakan da ake bi wajen yi wa yanmajalisar kiranye a Najeriya sun hada da:

  • Dole a samu kashi 51 cikin dari na mutanen mazabar, suna sanar da bukatarsu na yin kiranye, tare da sa hannunsu kai.
  • Dole ne wakilan wato wadan da ke jagorantar kawo takardar bukatar kirayen ga hukumar zabe, su bayar da bayanai kamar haka:

i. Adiresin inda suke zaune

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

ii. Lambobin waya

iii. Email

Bayan cika wadannan ka'idoji ne dai, INEC, za ta karbi koken nasu, sannan sai ta bi didigin sa, don tabbatar da cewar adadin mutaanen da ke da rajistar zabe kuma suke so a yi kiranyen da suka sa hannun a takardar sun kai yadda ake bukata ko kuwa.

Haka kuma hajiya Zainab Aminu ta ce ida aka kamala tantancewar ne za kuma a ji ra'ayin daukacin al'ummar mazabar dan majalisar da lamarin ya shafa, don jin wadan ke da rinjaye wajen yin kiranyen ga dan majalsiar ko kuma akasin hakan.

'Sashe na 69 da na 110, na kudin tsarin mulki Najeriya, da shashe na 116 na dokar zaben Najeriya ta 2010 da aka yiwa kwaskwarima, ya baiwa hukumar zaben ta INEC damar yin kiranye ga dukkan wani dan majalisa walau na tarayya ko na jiha, inda har kashi 50% na mutanen mazabarsa da suka yanke kauna daga gareshi, suka rattaba hannu kan takardar yi masa kiranye', in ji hajiya Zainab.

Ana so kuma a kammala kiranyen ne a cikin kwanaki 90 (Wattanin uku kenan).

Idan har aka yi nasarar yin kirayen, INEC zata mika takaradar shaidr kiranye ga dan majalisar, wanda hakan ya kawo karshen waadin dan majalisar, sannan a saka ranar da za a gudanar da zaben cike gibi bayan an baiwa masu sha'awar tsaya takarar dama neman goyan bayan masu zabe.

Sai dai babu wanda aka yi kiranye a cikin wadan da zasu yi takarar.

Wasu daga cikin yanmajalisun Najeriya da aka taba yi wa kiranye

Wannan ba shi ne karon farko ba da aka taba yi wa yanmajalisa kiranye ba a Najeriya, musamman a matakin majalisar wakilan kasar.

George Okoye

A shekara ta 2000, an taba yi wa Hon. Goeorge Okoye da ya wakilci mazabar Njikoka-2 a majalisar wakilan Najeriya, a shekara ta 2000. Sai dai bayan tsari a da ya shida da hukumar zaben Najeriya INEC kiranyen bai yi nasara ba, sakamakon karancin fitowar masu zabe, wajen sauraren ra'ayin jama'a kan kiranyen.

Dino Melaye

Sai kuma wanda aka yi wa dan majalisar Kogi ta Yamma Dino Malaye a shekara ta 2017.

A 2017 ne al'ummar mazabar sanata Dino Melaye suka gabatar da korafi, inda suka ce ba ya yi musu wakilcin da ya dace a majalisar dattijan kasar.

Sai dai sanatan ya zargi gwamnan jihar na wancan lokaci Yahaya Bello da hannu a kitsa batun yi masa kiranyen.

A karshe, a sanarwar da ta bayar, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta ce kokarin tantance sahihancin wadanda suka sanya hannu kan kokarin yin kiranye ga sanata Melaye a ranar 28 ga watan Afrilun 2018 ya gaza, bayan da kashi 5.34% kacal na yawan mutanen da ake bukata suka fito domin jaddada muradinsu na yi wa sanatan kiranye.

Mutane 18,742 ne suka iya fita zuwa rumfunan zabe domin tabbatar da sahihancin korafinsu, a cikin mutum 189,870 da tun farko suka sanya hannu kan korafin.

Farouk Adamu

Haka zalika a shekara ta 2006, shi ma Hon Farouk Adamu Aliyu da ya wakilci mazabar Birnin Kudu/Buji a majalisar wakilan Najeriya, ya taba fuskantar kiranyen.

A cikin watan Agustan 2006 ne hukumar zabe ta gudanar da kuri'ar kiranye a kan dan majalisar dokokin tarayya mai wakiltar Birnin Kudu da Buji daga jihar Jigawa, Farouk Adamu Aliyu, bisa korafi da neman yin kiranye da aka gabatar a kansa.

Alkaluma da aka samu bayan kada kuri'ar sun nuna cewa masu son a yi wa dan majalisar kiranye su ne suka yi galaba.

Sai dai daga baya batun kiranyen na Hon Faruk - wanda ya yi kaurin suna wajen adawa da kudurin wa'adin shugabanci na uku na shugaba Olusegun Obasanjo - ya sha ruwa bisa wasu dalilai da ba a fayyace ba.

Obasanjo dai ya musanta cewa ya yi niyyar yin tazarce a karo na uku lokacin da yake kan mulki.

Umar Jibril

Sai wanda aka so a yi wa Umar Jibril da da ya wakilci Lakoja/Kogi/Koton Karfe a majalisar wakilan shi ma, sai dai shi ma ya sha sakamakon wasu yanmazabar tasa da suka aikewa da hukumar zaben takardar cewar tursasa musu aka yi su sanya hannu kan takardar kiranyen da aka nemi a yi masa.

Natasha Akpoti Uduaghan

A yanzu duk da cewar an gabatar da takardar bukatar yin kiranye ga Sanata Natasha Akpoti, abin jira a gani shi ne ko wane mataki masu kiranyen za su dauka ganin INEC din ta ce ba su cika sharuddan da ya kamata ba wajen shigar da koken nasu gareta ba, kamar yadda doka ta tanada ba.