Me ya sa Iran ke da hannu a rikice-rikicen duniya?

    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

A yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a Gaza, rawar da Iran ke takawa a sassan gabas ta tsakiya na jan hankalin duniya.

Iran na goyon bayan Hamas a yakin da ake tsakanin Isra'ilar da Gaza, ta kuma kai hare-hare kan Iraqi da Syria da kuma Pakistan, sannan kuma Rasha na amfani da makamanta a kan Ukraine.

Kodayake Iran ta musanta hannunta a wasu hare-hare da aka kai gabas ta tsakiya kamar hare-haren da aka kai wa Isra'ila daga Lebanon, da wani harin jirgi maras matuki a kan dakarun Amurka a Jordan.

Harwayau da kuma hare hare ta saman da aka yi niyyar kai wa jiragen ruwan kasashen yamma a tekun maliya wanda kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran ke daukar alhakin kaiwa.

To amma su waye wadannan kungiyoyin da ke wadannan hare-hare sannan kuma ta yaya ake samun hannun Iran a wadannan rikice-rikice?

Wadanne kungiyoyi Iran ke goyawa baya?

Akwai kungiyoyin masu dauke da makamai da dama a sassan gabas ta tsakiya wadanda ke da alaka da Iran.

Wadannan kuwa sun hada da har da Hamas a Gaza da Hezbollah a Lebanon da 'yan Houthi a Yemen da kuma wasu a Iraqi da Syria da kuma Bahrain.

Yawancin su an san su da cewa jajirtattun kungiyoyi ne, kuma kasashen yamma na ayyana su da kungiyoyi ne na 'yan ta'adda, sannan kuma a cewar Ali Vaez, wani kwararre a bangaren rikicin kungiyoyin Iran, wadannan kungiyoyin na da manufa guda wadda ita ce ta kare yankin daga barazanar Amurka da kuma Isra'ila.

Babbar barazanar Iran na da nasaba da Amurka, daga nan kuma sai Isra'ila, wadda Iran ke yi wa kallon 'yar amshin shatar Amurka a yankin in ji shi.

Iran dai ta musanta hannunta kai tsaye a harin jirgi maras matukin da aka kai Jordan a ranar 28 ga watan Janairu, wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Amurka uku.

To sai dai kuma kungiyar Islamic Resistance a Iraq, wadda ta hada kungiyoyi da dama ciki har da wadanda Iran ke marawa baya, ta dauki alhakin kai harin.

Wannan ne karon farko da aka kashe dakarun Amurka a hare-hare ta sama a yankin tun bayan da Hamas ta kaddamar da hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a kan Isra'ila.

Hakan ne ya janyo barkewar yaki a Gaza, a don haka sai aka matsa wa shugaba Biden na Amurka lamba kan ya yi martani a kan harin.

A wani martani, Amurka sai ta kai hari kan sojojin juyin-juya halin Iran da ake kira sojojin Quds, da kuma kai hari kan mayakan sa-kai a Iraqi da Syria bayan mako guda, sannan kuma da wani harin hadin gwiwa da Amurka da Birtaniya suka kai kan 'yan Houthi da ke samun goyon bayan Iran a Yemen.

Da sannu a hankali Iran ta tsinci kanta a cikin wannan rikici, kodayake kusan shekaru 30 kenan tun bayan da aka daina yaki a kasar.

Iran dai ta sha tsame kanta daga cikin wannan yaki, to amma tana goyon bayan kungiyoyin mayakan sa-kai tun bayan juyin-juya halin kasar shekaru 45 da suka gabata.

Tarihin Iran da kuma alakarta da Amurka

Muhimman abubuwa biyu da suka faru a tarihin Iran da za su taimaka wajen bayanin matsayin kasar a yankin da kuma alakar kasar da Amurka

Juyin-juya-halin Iran da aka yi a 1979, ya nuna yadda aka ware kasar daga kasashen yamma.

A Amurka, a lokacin mulkin Jimmy Carter, ya yi kokari ya 'yanta wasu jami'an diplomasiyyar Amurkawa su 52 da aka tsare a Tehran babban birnin Iran tsawon shekara guda, hakan ya sa aka hukunta Iran da kuma ware ta daga cikin abubuwa da dama.

Wannan dalili ya sa Amurka da sauran kawayenta kasashen yamma suka rinka fifita Iraqi wadda Saddam Hussein ya mulke ta daga 1979 zuwa 2003.

Dalilin haka ya sa yaki ya barke tsakanin Iran da Iraqi inda aka shafe shekaru takwas ana yi.

Yakin ya zo karshe ne bayan da kasashen biyu suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.

To amma duk da haka an tafka asara inda aka kashe mutane miliyan guda da jikkata wasu da dama a kasashen biyu, kuma yakin ya janyo tabarbarewar tattalin arzikin Iran.

Wannan sai ya kirkiri wani abu a zukatan manyan jami'an Iran cewa akwai bukatar kasarsu ta yi duk mai yiwuwa wajen kare kanta daga dukkan wata mamaya a nan gaba, ciki kuwa har da batun kare shirinta na kera mamakamai masu linzami da dai sauran su.

Daga bisani, Amurka ta jagoranci mamaye Afghanistan a 2001 da kuma Iraqi a 2003, da kuma karuwar mamaya a sassan kasashen Larabawa a 2011.

Me Iran take so, kuma me ya sa?

A fannni soji, a hakikanin gaskiya ana ganin Iran ba ta da karfin soji kamar Amurka, kwararru da dama sun yi amanna cewa ikirarin da Iran ke yi na kokarin kare kai shi ne ya sa ta tsawon rai.

Kamran Martin daga jami'ar Sussex a Birtaniya, ya amince cewa Iran na son zama ja gaba ko kuma babbar kasa a duniya.

Ya ce, " Iran ta yi amanna cewa ta cancanci wani babban matsayi a yankin da ma duniya baki daya bisa la'akari da irin al'adunta na Persia da wasu abubuwanta na musamman da ya sa kasar ta yi fice."

Wanne irin karfin iko Iran ke da shi?

Wata mai fafutukar kare dimokradiyya a Iran Yassamine Mather, daga jami'ar Oxford a Birtaniya, ta ce Iran ba ta da wani karfi a kan kungiyoyin mayaka.

Amfani da 'yan Houthi a Yemen, wadanda ke kai wa jiragen ruwa hari a tekun maliya, misali ne da Mather ke cewa ba sa amfani da umarnin Iran. Suna da ta su manufar.

Ali Vaez, daga kungiyar Crisis Group, ya amince cewa matsalar kasa kamar Iran ita ce mika wuya ga wadanda ba su dace ba, shi ne ya hana ta iko da yankunan da take so.

Kazalika, Iran na da shirinta na nukiliya, abin da Vaez ya ce shi ne wanda yanzu take fadada shi.

Yakin duniya na uku

A yayin da ake yawan kai hare-hare a yankin, babu bukatar duba batun yakin duniya na uku.

Vatanka daga MEI, ta ce dole Iran ta yi takatsantsan saboda tana fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen iyakarta, bayan zanga-zangar da aka yi a shekarun baya bayan nan da mata suka jagoranta.

Akwai 'yan kasar ta Iran da suke adawa da irin abubuwan da gwamnatin kasar ke yi.

Haka kuma, kasashen yamma ma ba sa son yaki da Iran kamar abin da Ellie Geranmayeh, ya fada.

Geranmayeh, kamar sauran kwararru ya amince cewa yaki ba shi ne abin da ya kamata a sanya a gaba ba.

Ya ce, " Amurka da Iran na amfani da sojojin haya wajen kai wa juna hari, suna yaki da juna amma a fakaice.