PSG na shirin sayar da Neymar, Barcelona za ta cefanar da 'yan wasa domin dawo da Messi

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain na tunanin sayar da Neymar a bazaran nan inda Chelsea da akalla wata kungiyar Premier daya ke duba yuwuwar sayen dan gaban na Brazil. (Mirror)
Lionel Messi na son komawa Barcelona amma kuma kungiyar na bukatar ta hada fam miliyan 88 ta hanyar sayar da 'yan wasanta da kuma wata hanyar da za ta samu kudi kafin ta iya sake sayen kyaftin din na Argentina. (Mail)
Harry Kane na cikin 'yan wasan da Bayern Munich ke son zawarci a bazara amma kuma ana ganin kyaftin din na Ingila ba ya son barin gasar Premier. (Bild)
Juventus na shirin sayen dan bayan Senegal Kalidou Koulibaly, wanda ba ya jin dadin zamansa a Chelsea bayan kaka daya kawai. (Gazzetta dello Sport)
Liverpool ta fara hakura da matashin dan bayan Croatia Josko Gvardiol mai shekara 21 saboda tana ganin cewa farashin da Red Bull Leipzig ta sanya masa na fam miliyan 80 ya yi yawa sosai. (Football Insider)
Manchester City na shirin sayen matashin dan bayan Brentford, Aaron Hickey, na Scotland mai shekara 20 wanda aka yi masa farashi fam miliyan 30. (Sun)
Tsohon kociyan Sifaniya Luis Enrique ya fice daga cikin wadanda ke neman aikin horad da Chelsea. (Fabrizio Romano)
'Yan wasan Chelsean na farin ciki cewa watakila tsohon kociyan Tottenham Mauricio Pochettino ya zama sabon kociyan nasu. (Telegraph)
Arsenal da Chelsea da kuma Liverpool sun bayyana sha'awarsu a kan matashin dan bayan Valencia Yunus Musah, dan Amurka mai shekara 20. (90Min)
Chelsea ba ta da niyyar sayar da dan bayanta na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 Levi Colwill, a bazara duk da sha'awarsa da Liverpool da Tottenham da kuma Manchester City ke yi. (Football Insider)
Newcastle da Crystal Palace da kuma Brighton na bibiyar tauraron matashin dan wasan tsakiya na Blackburn Adam Wharton mai shekara 18, dan Ingila wanda ake kwarzantawa sosai. (Sun)










