An haife tagwayen da aka daskarar da 'yan tayinsu shekara 30 da suka wuce

Yan biyu

Asalin hoton, NATIONAL EMBRYO DONATION CENTER

Bayanan hoto, Lydia Ann and Timothy Ronald Ridgeway were born on 31 October 2022
    • Marubuci, Sam Cabral
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
    • Aiko rahoto daga, BBC News

An haife wasu ƴan biyu da aka daskarar da ƴan tayinsu tun shekara 30 da suka wuce a jihar Tennessee da ke Amurka.

A yanzu an yi amannar cewa wannan lamari shi ne sabon tarihi da aka kafa na daskarar da ƴan tayin da suka yi sanadin haifar ƴaƴa da ransu.

An adana su a ma'aunin sani na ƙasa da digiri 128 ranar 22 ga Afrilun 1992.

Rachel Ridgeway ƴar garin Oregon, wacce ke da ƴaƴa huɗu, ta haifi ƴan biyun ne ranar 31 ga watan Oktoba.

Mahaifin ƴan biyun Philip Ridgeway, ya ce lamarin na da "ɗaure kai".

Lydia Ann da Timothy Ronald Ridgeway ga alama sun kafa sabon tarihi, a cewar cibiyar ba da gudunmowar ƴan tayi, NEDC, wato ƙungiyar da ta ce ta taimaka wajen haihuwar jarirai fiye da 1,200 daga ƴan tayin da aka samu kyauta.

A cikin kundin tarihi na NEDC dai, Molly Gibson, jaririn da aka haifa a shekarar 2020 shi ne wanda aka haifa daga ɗan tayin da ya shekara 27 a daskare.

"Matakin... na ajiye waɗannan ƴan tayi zai ƙara ƙwarin gwiwa wa mutanen da ke tababar ko ƴan tayin da aka ajiye tsawon shekara 5 ko 10 ko 20 za su yi aiki," in ji Dr John David Gordon, wanda ya aiwatar da dashen ƴan tayin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Amsar ita ce tabbas za su yi aiki!"

Ƴan biyun dai an haifar wa wasu ma'aurata ne da suka nemi a ɓoye sunansu ta hanyar dasa musu.

Mutumin na cikin shekarunsa na 50 kuma an ce ya dogara ne kan wani ɗan shekara 34 da zai ba shi kyautar ƙwan haihuwar.

An ajiye tayin ne a wani ɗakin gwaji a can wani waje a gaɓar kogin yammacin Amurka a shekarar 2007 lokacin da NEDC ta bai wa ma'auratan kyautar ƴan tayin a Knoxville da ke Tennessee ga wasu ma'auratan su yi amfani da su maimakon wancan.

Daga nan sai wani ƙwararre a daga wani asibiti na NEDC ya aiwatar da aikin dashen a mahaifa a farkon shekarar nan.

A wata sanarwa, NEDC ta ce tana fatan labarin zai ƙarfafa wa sauran mutane gwiwa wajen amfana da albarkar da ke tattare da ajiyayyen ɗan tayi.

Ƴan biyun su ne na farko da Ridgeway - mai ƴaƴa huɗu ƴan tsakanin shekara ɗaya zuwa takwas - ya same su ta hanyar dashe.

"Shekarata biyar a lokacin da Ubangiji ya wanzar da rayuwar Lydia da Timothy, ya kuma ta adana rayuwar tasu sun lokacin har sai yanzu da suka zama mutane," kamar yadda Philip Ridgeway ya shaida wa CNN.

"A wani fannin za a iya ce wa su ne manyan ƴaƴanmu, duk da cewa su ne ƙananan.

"Akwai abin ɗaure kai sosai a kan lamarin nan," ya ƙara da cewa.