Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Onana ya tare fenariti a wasan da Kamaru ta doke Cape Verde
Vincent Aboubakar ya ci ƙwallo biyu, yayin da Andre Onana ya tare fenariti a wasan farko da Marc Brys ya ja ragamar Kamaru ta doke Cape Verde 4-1 ranar Lahadi.
Tun farko an samu rashin jituwa cikin watan Afirilu, bayan da Ma'aikatar wasanni ta naɗa Brys kociyan Indomitable Lions, yayin da hukumar ƙwallon kafar kasar ba ta amince da hakan ba.
Minti 13 da fara wasa Kamaru ta fara zura ƙwallo a raga, sannan Nouhou Tolo ya ci na hudu, yayin da Cape Verde ta zare ɗaya ta hannun Jamiro Monteiro.
Kamaru ta yi nasara a kan Cape Verde ne, wadda ta kai quarter finals a gasar kofin Afirka a 2023, duk da ƙalubalen da ta fuskanta a fafatawar.
Sun kuma kara ne a wasa na uku a cikin rukuni na hudu a fafatawar neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Wasan da aka buga a Yaounde a gaban dubban ƴan kallo, ta kai ga Onana ya tare fenariti a minti na 94, bayan da Kevin Pina ya buga ƙwallon.
Haka kuma an yiwa golan na Manchester United keta ta hannun Gilson Benchimol lokacin da ya yi kokarin kama ƙwallo a daf da layin raga.
Da wannan sakamakon Indomitable Lions ta koma ta ɗaya a kan teburi na hudu da tazarar rarar ƙwallaye tsakani da Libya da kowacce take da maki bakwai a wasa uku-uku.
Dukkan tawagar da ta ja ragamar kowanne rukuni tara daga Afirka za ta kai wasan cin kofin duniya kai tsaye da za a yi a 2026.